TAMBAYA (46)❓
Ko da akwai alaƙa tsakanin bayyanar Dajjal da tsadar rayuwarmu ta
yau ?
AMSA❗
Tabbas da akwai alaƙa mai ƙarfi tsakanin bayyanar Dajjal da kuma
yanayin tsadar rayuwa da muka tsinci kanmu a yau. Hakan yanada nasaba da
bayyanar ƙananan alamomin tashin alƙiyama waɗanda muke ganinsu a kan idanunmu
Daya daga cikin hanyoyin da Dajjal zai bi ya samu biliyoyin magoya baya shi
ne bangaren amfani da kudi, wanda a zamaninnan a kan kudi sai mutum ya yi kisan
kai saboda tsabar son zuciya. To ina kuma ga idan Dajjal ya bayyana wanda zai
ba ka duk abin da kake so indai har za ka yarda shi Allah ne (Wal'iyazubillah)
Magana ake ta tsananin son kudi saboda tsadar rayuwa wanda hakan ya zama
silar salwantar imanin miliyoyin musulmai, har hakan ke kaisu ga rantar kudi a
wasu bankunan waɗanda
suke bayarda bashi da kudin ruwa (riba). Munsan kuwa cin riba haramunne
A shekarun baya wani babban sirri ya fito daga babban bankin duniya (World
Bank wanda ake kira da Central Bank of Central Banks) ?
A cikin sirrin an gano yanda masu manyan madafun iko suke son su mulki
duniya. Michael Snyder – Global Research, February 01, 2015
An wallafa sirrin a 30 ga watan Satumbar shekarar, 2013. Karen Hudes, wadda
ta tona musu asirin, ta kammala karatunta na Lawyer daga makarantar koyon lauya
ta garin Yake dake kasar Amurka, inda ta samu aiki a bangaren Legal department
na bankin duniya, ta share sama da shekaru 20 tana aiki a bankin, wanda hakan
ya bata damar sanin sirrika dayawa da bankin ya boye. A karshe suka kore ta don
kawai ta tona asirin cin hanci da rashawa (corruption) da wasu sukayi a cikin
bankin. Sirrin da ta fitar ya girgiza ya yi matuƙar girgiza gwamnatin
amurka da ma sauran al'umma baki daya. Hudes, tace: Manya manyan masu madafun
iko suna son amfani da ma'aikatu da makarantu don ganin sun mallaki duniya. Manufarsu
shi ne su sarrafa al'umma ta hanyar tirsasawa mutane karban bashi (debt) ta
yanda a karshe za su bijiro da aƙidarsu ta yanda mutane za su karba hannu bibbiyu
ta hanyar amfani da tasirin bashin da suka bayar, yanda mutum ba zai iya tona
musu asirin sirrinsu ba tun da daman sune suke sarrafa manyan kafafen yada
labarai na duniya
Karen, ta ci gaba da cewa: wannan fa bawai maganace daga masu ba da labarin
ƙanzon kurege ba (conspiracy theories), saidai sirrine da aka sameshi daga
attorney wadda ta share sama da shekaru 20 a matsayin ma'aikaciyar babban
bankin duniya. Waɗannan
sune muƙaman da ta riƙe, wanda an samesune kai tsaye daga shafinta;
Ta karanci fannin shari'a (Law) a makarantar Yale da kuma fannin tattalin
arziƙi (Economics) a jami'ar Amsterdam duk a kasar Amurka. ta yi aiki a bankin
shige da fice na na Amurka daga shekarar 1980 zuwa 1985. ta yi aiki a Legal
Department a babban bankin duniya daga shekarar 1986 zuwa 2007. Ita ce ta
kirkiro Non Governmental Organization Committee na International Law sashen Bar
Association na Amurka da kuma Committee a kan Multilateralism da Accountability
na International Organizations na Amurka reshen kungiyar lauyoyi na duniya
(International Law Association)
Karen Hudes ta wallafa littattafai kamar haka "The World Bank: A Case
Study in Corruption" (2006), "The Debt Bomb" (2008), "The
Best-Kept Secrets of the Money and Banking Industry" (2010), da kuma
"The World Bank: The Untold Story" (2011)
A yanzu haka, tana ta fallasa asirin manyan shugabannin duniya waɗanda manufarsu shi ne sunfison yanda suka
dama haka kowa zai sha, kamar yanda ta yi bayanin hakan a firar da New American
ta yi da ita
Tsohuwar ma'aikaciyar tace: Wasu tsirarun kungiya ne suke sarrafa tsarin
jujjayawar tattalin arziƙin kasashen duniya, cin hanci da rashawa ya yi musu
katutu a zuciya. Sune suka mallaki manyan kafafen yada labarai ta yanda ba za a
tona musu asiri ba. Sun koreta ne a yunƙurinta na ganin ta toshe kofar cin hanci
da rashawa a babban bankin na duniya, wanda kuma har yanzu tananan a kan manufarta
da taimakon wasu masu irin aƙidunta
Hudes, ta yi sharhi a kan 2011 Swiss study da wanda PLUS ONE suka wallafa
"kungiyar masu son sarrafa duniya”, tace: sunanan sunata aiki tuƙuru
musamman a kan manyan bankunan kasashe (central banks) don ganin sun cimma
manufarsu
Kwanakin baya da akwai binciken da aka gudanar a Swiss Federal Institute of
Technology dake jihar Zurich a kasar Switzerland. An bincika alaƙar
dake tsakanin kamfanoni miliyan 37 da masu zuba hannun jari. Sai aka gano akwai
wasu 147 kacal waɗanda
sune sukeda kaso 40% cikin 100% na kudaden da ake zubawa a hada-hadar kasuwanci
na duniya gaba daya. Shi kuma babban bankin duniya da kuma sauran bankunan
kasashe ananne ake sarrafa waɗannan
maƙudan kudade
Mutane dayawa ba su ma san mene ne bankin International Settlements ba, wanda
saninsa yanada matuƙar muhimmanci (Musamman a wannan zamanin, wanda
duniya ta zo karshe). A kwanakin baya na yi bayani a kan yanda tsarin wannan
banki ya shafi dokar kowacce gwamnati da takeda hurumi da bankin. Bankin da
yake sarrafa kudaden kasashe a sirrance wanda ba kowa ba ne yasan da hakan
Bankin yana garin Basel ne dake kasar Switzerland, kuma yanada rassa a Hong
Kong da Mexico. Bankine ba irin kowanne banki ba, bankine ba irin wanda aka
zaba ba haka kuma ya barranta daga dukkan haraji ko kuma dokokin kowacce kasa. Wikipedia
ma sunce banki ne wanda ba ya karkashin kulawar kowacce gwamnati a duniya. International
Bank of Settlements sune suka taimakawa Nazis (Kungiyar Hitler) da maƙudan
kudade domin aiwatar da yaƙin duniya na biyu (World War II)
Saidai yanzu babban bankin na duniya (IBS) ya karkata akalarsane a kan yanda
zai sarrafa dukiyoyin mutane su dawo karkashinsa (Ta yanda idan Dajjal ya bayyana
zai samu sauƙin samun mabiya. Wal'iyazubillah). A yanzu haka da
akwai manya manyan bankuna har guda 58 waɗanda suke karkashin babban bankin duniya (IBS). Wannan
dalilin ne ya sa a duk duniya babu kasar da takai Amurka karbar bashi musamman
mai kunshe da kudin ruwa (interest). Ke nan kunga ita kanta ma Amurka a
karkashin bankin take. (Wani zai iya tambayar wai to shin su wanene suke
sarrafa wannan bankin ?. Ba kowa ba ne face Banu Isra'ela wato Yahudawa, eh
Yahudawa, gashidai ba su da wani yawa amman sharri da bala'insu ya yi yawa a
ban kasa, tun daga zamanin Annabi Musa A. S har zuwa wannan zamanin namu na
karshen rayuwar ba ni Adam)
Duk bayan watanni biyu, suke hada taron karawa juna sani a kan yanda za su
cimma manufarsu wanda silar wannan taro da suke mutane suka matuƙar
cutuwa, namiji, mace, yaro da babba amman ba wanda yake cewa komai silar hakan.
(Ba haka nan aka kirkiri wannan babban banki ba, domin kuwa sun dade suna
gudanardashi wanda manufarsu shi ne su kafa: "Sabuwar Dokar Duniya” (New
World Order) kamar yanda hakan yake a rubuce a bayan kudin Amurka (American
Dollar) babban manufarsu shi ne a cire addini a rayuwar dan Adam)
Haka kuma Karen Hades ta fitarda article mai suna: "Su wanene suke
mulkar duniya: Hujjoji ƙwarara da suke nuna masu mulkar duniya”, ta hada
da abin da Professor Carrol Ƙuigley (na jami'ar Georgetown) masanin tarihi ya
fada a cikin littafin da ya wallafa a shekarar 1966: "Manyan masu madafun
iko suna ƙoƙarin mulkar duniya ta hanyar amfani da kudaden banki da kuma ƙaƙabawa
mutane riba (interest) yayinda aka ba su rancen kudi” Wanda idan muka duba
yanayin da kasashen duniya suke ciki za mu tabbatarda cewar babu shakku a cikin
wannan lamarin
Ana kiran tsarin da sunan neu-feudalism, wanda a iya kasarmu kadai za mu gasgata
hakan ta hanyar duban bangaren bankunan kasarmu inda zakaga za su ba ka bashi
ammanfa saidai idan ka tashi biyansu ka dora musu kudin ruwa (interest) wanda
kuma sanin kanmune cewar cin kudin ruwa haramunne a addinin musulunchi. Akwai
kuma bankunan da suke tsarinnan wanda idan ka ba su ajiyar kudi sai su dinga
juyasu suna dora maka ladan ajiya, manufar hakan shi ne, idan mutum yafara jin
dadin kudin, zai wahala ka ga bai bi tawagar Dajjal ba idan ya bayyana
la'akarida idan mutum bai bi Dajjal din ba to fa shi ke nan ya rasa kudinsa. Kuma
dai munsan mutum akwai son dukiya kamar yanda Allah ya fada a cikin Suratul
Fajr ayata 20:
( وَتُحِبُّونَ الْمَالَ حُبًّا جَمًّا )
الفجر (20) Al-Fajr
Kuma kuna son dũkiya, so mai yawa
A yanzu haka da akwai manyan kafafan yada labarai guda 6 waɗanda suke sarrafa kaso 90% cikin 100% na
labarai da rahotonnin da kuma wasanni a kasar Amurka. Wannan sune daga dalilan
da ya sa suka saka tambarin ido daya na Dajjal a bayan dollar ta Amurka, tareda
rubutun "Annuit Ceptus" (Yana farin ciki da tsarinmu) da kuma daya
rubutun da yake daga kasan hoton triangle "Novus Ordo Seclorum"
ma'ana Sabuwar Dokar Duniya
Cin riba ya zamo ruwan dare, kuma Annabi SAW ya ce mafi ƙanƙantar
illar cin riba shi ne mutum ya yi zina da mahaifiyarsa. Anata shigo mana da
tsare-tsare kala-kala waɗanda
sukeda alaƙa da cin riba. Idan kana amfani da Palmpay zakaga idan ka ba su ajiya
(deposit) N1, 500, 000 za su juya maka kudin su ba ka N610 a matsayin kudin
ruwa na kwana daya, N18, 416 a wata daya, N240, 087 a shekara guda, za su dinga
ba da damar cire kudin ruwan kullum a kowacce safiya idan ka amince
tsare-tsarensu. Flexi Cash suna turowa mutane saƙo ta SMS cewar za su ba
ka rancen N3, 000 ba tareda kudin ruwa ba (Zero interest) dama ce ta kwana daya,
ammanfa sai idan kai sabon shiga ne. Idan ka ranci N1, 000, 000 za su dinga
daukan kudin ruwa (interest) N20 a kullum. Idan ka kuskura ka shiga tarkonsu to
akwai yiwuwar za ka bi Dajjal la'akarida idan ya bayyana zai sarrafa waɗannan hanyoyin samun kudin ta yanda zai
wahala mutum ya ƙi binsa idan ya ce ka bini, idan ka yarda ni Allah
ne zan maido maka da dukiyarka. Wal'iyazubillah
Mu duba mu ga yanda gwamnatinmu taketa ranto maƙudan kudade waɗanda ake bayarwa da kudin ruwa (interest)
wanda a Labaran yammacin Asabar 23/09/2023CE - 08/03/1445AH gidan radio na
Guarantee suka fitar da sanarwar: "Shugaban kasa ya sake karbo bashin dala
miliyan 700 daga bankin duniya ". Idan ka maida kudin Naira zai koma
Biliyan Dari Biyar da Arba'in da Shida (N546, 000, 000, 000). Magana ake ta
fiyeda rabin tiriliyon daya. Matsalar a nan ita ce: iya masu madafun iko ne
kadai suke amfana da kudin amman talakawa da ake fakewa cewar domin su ake
rantowa su dinne kuma suke shan wahala domin kuwa manyan can dinne dai suke
rarrabe kudin a tsakanin, ta hanyar siyen motocin hawa na miliyoyin kudi da
kuma sauye sauyen kayan masarufinsu na yau da gobe waɗanda a iya wannan fannin kadai Allah ne
kadai yasan biliyoyin dalolin da aka wawashe a kasa da tenuwa 3 ko 5 da suka
gabata. Ku yi tunani sosai a kan wannan maganar tawa. Duk da dai akwai yunƙurin
da gwamnatin tarayya take yi na ganin an sauƙaƙewa al'ummar radadin
talaucin da ya yi kaka gida a taredasu ta hanyar sauya kudaden yanzu su koma
sababbi (Old naira to New naira notes), wanda canjin zai fara aikine daga watan
January na shekarar 2024. Muna fatan hakan yakawo sauƙi a kasar ta fuskar
tattalin arziƙi. To ammanfa kada mu shagala domin kuwa shi Dajjal
ba ruwansa da batun sabo ko tsohon kudi, burinsa kawai ka bishi ya ba ka duk abin
da kake so (Aljannar duniya)
Idan muka kuskura muka biyewa son zuciyarmu to tabbas za mu fada halaka, halakar
da yahudawa suke son su ja mu ciki, mu bi wanda suka dade jiran bayyanarsa wato
Dajjal. Daga cikin ikon da Allah SWT zai bashi, shi ne zai warkar da mara
lafiya nan take, zai ce masa ta zubo da ruwa (wanda a yanzu hakama kasashen
yamma irinsu China da Amurka sun fara wannan tsarin wanda ake kira da Cloud
Seeding wato Artificial Rain, Dubai da wasu kasashen Gabas suma sun bi sawu), zai
raba mutum gida biyu kuma ya umarce shi ya hade (Yanzu an dauko hanyar wannan
ta amfanida laser ayiwa mutum CS batareda jini ya fito ba), zai tada na kabari a
zahiri (Saidai a badini aljanine zai shiga gawar sai ya rudi mutane tun da har
Aljanu ma za su bishi), Yahudawa 70, 000 za su fara binsa riƙe da
baƙar tutarsu daga yankin Isfahan dake Iran. Zai kwace tattalin arziƙin
mutane, bankunansu, kasuwanninsu, abincinsu da abin shan su, wanda ya bi shi ya
samu duniya wanda ya bijire masa zai sha wahala saidai hakan jarabawace ga
muminai wanda ba su bishi ba, makomarsu Aljannah silar haƙurinsu
Kumadai munga abin da ke faruwa ga manoman Dutch dake kasar Netherlands, yan
sanda sun tasosu a gaba sunata kashesu tareda kwace musu amfanin noma kamar
yanda tashar talabijin ta France24 da wasu tashoshin suka wallafa. Ƙudirin
gwamnatin Dutch shi ne ta naƙasa manoma 3, 000 kafin shekarar 2030 wai hujjarsu
ta yi hakan yanada nasaba da yanda manoma suke zama silar gurbacewar yanayin
muhalli. Manoman Dutch unyi zanga zanga (No Farmers, No Food, da kuma: Farming
- Food & Climate Justice Now #DutchFarmers) amman matsalar bata kau ba sai
ma abin da ya karu
Wanda ita ma gwamnatin Saudi Arabi ta bi irin wannan sahun saidai ita ta ce
za ta siyo hatsinne ta killace a rumbunta domin gudun afkuwar yanayin tsananin
sanyi da za a shiga da kuma karancin abinci a shekaru masu zuwa. Amman a zahiri
batun ba haka ba neba, domin kuwa munsan kasashen yamma dayawa waɗanda suke da aƙidar mallake bangaren
noma kacokan su raba manoma da harkar ta yanda za su dinga sarrafa komai da
kansu, kunga ke nan idan Dajjal ya bayyana zai samu sauƙi kwace abin da mutane
suka dogara da shi su rayu wato abinci
A bangaren bayyana boyayyun aƙidunsu, sunada alamu dayawa a kusan kowanne abunda
ake amfani da shi a wannan zamanin, tun daga bangaren kimiyya har na fasaha. Saka
satellite a sararin samaniya a matakin 22, 000 meters yanada alaƙa da
lambar shaidan domin kuwa yana son multiple din 11 (Irinsu 22, 33, 44, 55, 66
da sauransu). Neil Armstrong shi ne ya fara zuwa duniyar wata a shekarar 1969, acan
yaji kiran sallah saura kiris ya karbi musulunci musamman ma da ya kara jin
kiran sallar a kasar Egypt amman kungiyar NASA (masu sarrafa da kuma tura
mutane sararin samaniya) suka ce masa idan ya sake ya kara fitarda wannan
sirrin to za su janye masa tallafi kuma za su cire sunansa daga tarihin mutum
na farko da ya fara taka kan wata. Karshedai bai musulunta ba saboda rashin
rabo da tsoron talauci. Kuma Malaman mu'ujizar Ƙur'ani sun yi bincike a
kan Suratul Ƙamar aka gano tanada alaƙa da cewar wani mutum
zai je duniyar wata a 1969, idan ka irga ayoyi tun daga Ƙamar zuwa Nas zakaga
ayoyi 1, 389 ne wanda ya yi daidai da Gregorian calendar na lokacin saukar ayar.
Allahu Akbar
Akwai wata waƙa da Eminem ya yi mai suna "My Darling"
inda ya fito da ma'anar 666. Ga kuma masu daukan selfie suna daga yan yatsunsu
2 ma'ana 11 (Daya a cikin daya, wanda mudai musulmai munsan Allah SWT shi ne
daya kacal, amman shaidan ya yi musu wahayin fitarda yatsu biyu don nuna alamun
kishiya ga Allah wato shirka) Wannan ilimi ne mai zaman kansa da ke kira da
Numerology wato ilimin sanin sirrin lambobi. Kuma idan ba mu manta ba ai ya zo
a sahihan hadisai cewar anyiwa Annabi SAW sihiri, inda akai amfani da ƙulli
11 aka tofe aka wulla rijiya. A karshe Allah ya saukarda Surorin kariya wato
Falaƙi da Nasi (Wanda idan mun irga ayoyinsu zamuga guda 11 ne, silar hakan sai
sihirin da akai masa, SAW, ya warware ma'ana kowacce aya daya ta warware ƙulli
daya)
Tasirin wancan tofin da akayi sau 11 ne ya sa ake kiran lambar da Devil's
Number, bi ma'ana Lambar Shaidan. Haka kuma suna son lambata 13 saboda ita ma
odd number ce, bata raba kanta da kanta, ganye (leaf) guda 13 ne a kafar dama
ta angulun dake bayan American dollar haka kuma masu (arrows) guda 13 ne a
kafar hagun, kuma taurari (stars) 13 ne a saman angulun, saboda tanada alaƙa da
Original 13 British Colonies (Manyan jihohin amurka da ake tunƙaho
dasu guda 13 waɗanda
birtaniya ta yi colonizing; 1) New York, 2) Pennsylvania, 3) Virginia, 4) North
Carolina, 5) South Carolina, 6) Georgia, 7) New Hampshire, 8) Massachusetts, 9)
Rhode Island, 10) Connecticut, 11) New Jersey, 12, Delawale, 13) Maryland)
saboda suna da alaƙa da Mithrah da Deciples dinsa su 13, wannan
dalilin ya sa a benayen Amurka babu hawa na 13 saidai na 12 na samansa kuma sai
su rubuta 14. Ido 1 da yake a saman pyramid na dolar Amurka ba su sauko da shi ba
saboda har yanzu babban Dajjal din bai bayyana ba, gwamnatin ta amince da
fitarda wannan tambari na Pyrmid ne a shekarar 1782, a shekarar 1776 aka ƙirƙiro
wannan aƙida da gudunmawar Christopher Columbus wanda ya yi descovering USA kamar
yanda suka rubuta da Roman number (MDCCLXXVI)
Peter wanda ya fito a matsayin jarumin film din Spiderman na Marvel company,
ya kasance a film din wanda gizo-gizo ya cijeshi silar hakan shi ma ya
dabi'antu da yin yana yana jefawa yana tashi sama, illar film din ita ce:
Spiderman din yana amfanida yan yatsu 2 ne, manuniya da kuma dan ƙurya
(yatsan karshe) wanda hakan ke nuna lamba 11, wato lambar shaidan. Ya gwada
sakin babban yatsa da sauran yatsunsa a kan yanar ta fito amman bata fito ba
har saida ya saki yan yatsu 2 a lokaci guda sannan yanar ta fito. Shaidanci da
shirka ta bayyana. Munsan cewar Allah SWT ya ce gida mafi rauni shi ne gidan
gizo-gizo:
( مَثَلُ الَّذِينَ اتَّخَذُوا مِن دُونِ اللَّهِ أَوْلِيَاءَ كَمَثَلِ الْعَنكَبُوتِ اتَّخَذَتْ بَيْتًا ۖ وَإِنَّ أَوْهَنَ الْبُيُوتِ لَبَيْتُ الْعَنكَبُوتِ ۖ لَوْ كَانُوا يَعْلَمُونَ )
العنكبوت (41) Al-Ankaboot
Misãlin waɗanda
suka riƙi waɗansu
masõya waɗanda
bã Allah ba, kamar misãlin gizõgizo ne wanda ya riƙi wani ɗan gida, alhãli kuwa lalle mafi raunin
gidãje, shĩ ne gidan gizogizo, dã sun kasance sunã sane
Sharrin yahudawa da Nasara ne ya sa suke fito na fito da wannan ayar, bawai
gizo-gizo ba, sai suka tsara yanda za su ƙaryata waccan ayar ta hanyar wasan
kwaikwayo suka fitarda mutumin gizo-gizo (Spiderman) wanda yake da dabi'ar
taimakon mutane alhalin a zahiri munsan waccan ayar ta tabbatarda raunin gidan
gizo-gizo la'akarida iska kadai idan ta kada za ta rusahsi. Ƙalubale
ga wasu matasan zamani masu mashin din Adaidaita Sahu da suke saka hoton
Spiderman a jikin mashin dinsu
Celebrities waɗanda
suke cikin ƙungiyoyin bautar shaidan (Freemasons) sun hada da
Madonna, Hannah Montanah, Nicki Minaj, John Lennon, Rihanna, Ketty Perry, Lady
Gaga, Aliester Crowley, Miley, Marilyn Manson ga kuma Anton Lavey wanda shi ne
ministan chochin Shaidan a Amurka. Duk suna rudar mutanene da daukakarsu ta
hanyar amfani da kide kide da waƙe waƙe, wannan kadai ya isa ya tabbatarwa da mutane jin
kida haramunne domin kuwa idan mutum bai tuba ba akwai yiwuwar idan Dajjal ya
bayyana kaima ko kuma kema ki zamo mabiyinsa. Ƙalubale ga masana'antar
Kannywood. Tun da ya tabbata a cikin sahihayn cewar Dajjal zaizo har nan inda
kake karanta wannan rubutun, zai zagaye duniya a cikin kwanaki 40, kwana 1
kamar shekara, kwana na 2 kamar wata, kwana na 3 kamar sati sai kuma ragowar
kwanaki 37 kamar na yau da gobe, saidai Makka da Madina ne kawai ba zai iya
shiga ba suma saboda zaiga Mala'iku suna gadin kofofin ta, kuma a hakan sai
wasu sun fito daga waɗannan
kasashe masu daraja sunbiyoshi don kawai son zuciya. Wanda kuma mata sune za su
fi yawa a cikin mabiyansa saboda mata sunfi maza sakaci musamman bangaren
addini kuma daman Annabi SAW ya ce sune suka fi yawa a Jahannama. Wal'iyazubillah
Bari na tsaya iya haka saboda gudun kada in ja lokacin mai karatu da yawa duk
da cewar akwai bayanai dayawa waɗanda
lokaci ba zai sa na rubutasu ba. Amman inason na yi amfani da wannan damar don
janyo hankalinmu a kan mu koma mu damƙe karatu da sanin ma'anar Ƙur'aninmu
da sunnar ma'aiki SAW domin kuwa su kadaine tafarkin tsira. Mu yawaita karanta
addu'ar da Annabi SAW ya koyar mu dinga karantawa a duk bayan kowacce sallar
farillah
An karbo daga Abu Hurairah (RA) da Nana Aisha (RA) sunce Annabi SAW yana
karantarda wannan addu'ar a cikin kowacce sallarsa ta farillah (Bayan Tahiyya
kafin sallama):
ﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﺍِﻧِّﻲ ﺍَﻋُﻮْﺫُ ﺑِﻚَ ﻣِﻦْ ﻋَﺬَﺍﺏِ ﺟَﻬَﻨَّﻢَ ﻭَﻣِﻦْ ﻋَﺬَﺍﺏِ ﺍﻟْﻘَﺒْﺮِ ﻭَﻣِﻦْ ﻓِﺘْﻨَﺔِ
ﺍﻟْﻤَﺤْﻴَﺎ ﻭَﺍﻟْﻤَﻤَﺎﺕِ ﻭَﻣِﻦْ ﺷَﺮِّ ﻓِﺘْﻨَﺔِ ﺍﻟْﻤَﺴِﻴْﺢِ ﺍﻟﺪَّﺟَّﺎﻝِ
“Allaahumma
inni a’oodhu bika min ‘adhaab jahannam wa min ‘adhaab al-ƙabri wa min fitnat
il-mahyaa wa’l-mamaat wa min sharri fitnat al-maseeh al-dajjaal”
Ya Allah, ka rabani da azabar jahannama, da azabar kabari, da masifar
rayuwa da mutuwa, da kuma sharrin masifar Dajjal"
(Sahih Muslim 588a)
A hadisin Ibn Abbas (RA) kuma ya kara da cewar: Muslim Ibn Hajjaj ya ce:
Tawus ya tambayi dan sa shin kayi wannan addu'ar a cikin sallarka ? ya ce: A'a.
Sai ya ce masa je ka maimaita sallar gaba dayanta
(Sahih Muslim 590)
Muna roƙon Allah ya kiyayemu daga sharrin kawunanmu da
kuma tarkon iblis. Allah ka amshi rayuwarmu muna musulmai. A daure a yada
wannan rubuta domin kuwa Allah SWT kadai yasan waɗanda za su amfana dashi, kuma dan Allah
kada a canja ko da harafi guda daya
Domin neman hujjojin abin da na rubuta sai a duba:
1) Looking into the eye of the Dajjal by Abu Muhammad Ibn Dawod, 2) The Ƙuran
Dajjal and the Jasad by Imran N. Hosein, 3) Albidaya wan Nihaya by Abubakar
Alhafiz Ibn Khathir, 4) Talbis iblis by Imam Ibn al-Jawzy, 5) Signs Of The Last
Day by Harun Yahya, 6) The Signs of the Hour and What after Death, 7) Ƙuran
and Modern Science by Dr. Bashir Sokoto 8) The Evils of Music The Devils Voice
and Instrument by Ibn-al-Ƙayyim-al-Jawziyah, 9) Rational Believer YouTube
Channel 10) Sense Islam YouTube Channel
Wallahu ta'ala a'alam
Subhanakallahumma wabi hamdika ash-hadu anla'ilaha illa anta astaghfiruka
wa'atubi ilayk
Amsawa:
Usman Danliti Mato (Usmannoor_As-salafy)
Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance Damu. . .
𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇
https://whatsapp. com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G
𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇
Https://www. facebook. com/groups/336629807654177
𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇
https://t. me/TambayoyiDaAmsoshi
ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ
**************************
Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.