Ticker

6/recent/ticker-posts

Hukuncin Mace Ta Yi Salla Kafafunta A Waje?!

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Assalamu Alaikum. Malam barka da yau Allah ya qara rufa asiri. Malam shin menene hukuncin sallah da qafafuwa waje ga mace, ina jin malamai na cewa babu banbanci ga sallar macce da ta namiji da Manzon Allah (S A W) ya ce kuyi sallah kamar yanda kukaga inayi, ban saniba ko nayi kuskure toh naga maza ba sa rufe qafafuwan su, don Allah malam ina son sanin hukuncin sallah da safa shin dole ne ko mustahabbi?? Na gode

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

Wa'alaikumus Salam warahmatullahi Wabarkatuh

An shar'anta wa mace baliga wacce ba baiwa ba, ta rufe jikin ta baki ɗayansa idan zatayi sallah, sai fuskar ta da tafukan hannayenta ne kaɗai bazata rufe ba. Saboda ita mace 'ya gabaɗayanta al'aurah ce.

Idan ta yi sallah alhali ba ta rufe wani sashen jikinta ba kamar qwaurinta ko kafarta ko dukansu ko kuma wani sashen kanta a buɗe, toh sallar ta ba ta yi ba. Manzon Allah (sallallaahu alaihi wa sallam) ya ce:

"لا يقبل الله صلاة حائض إلا بخمار" رواه أحمد وأهل السنن إلا النسائي بإسناد صحيح.

 "Allah baya karɓar sallar mace wacce ta fara al'ada har saida khimaar (maya fin rufe kai)"

Ahmad da Abu Dawud da Ibn Majah da Tirmizi suka ruwaito shi da isnaadi ingantacce.

و لما روى أبو داود عن أم سلمة عن النبي صلى الله عليه و سلم أنها سألت النبي عن المرأة تصلي في درع و خمار بغير إزار فقال: " المرأة عورة"

Abu Dawuda ya ruwaito daga Ummu Salamah (radiyallah anha) cewa ta tambayi Manzon Allah (sallallahu alaihi wa sallam) gameda matar da ta yi sallah tana sanye da dir'a (kamar riga) da khimaar (maya fin rufe kai) amma ba ta sanya Izaar (kamar wando na mata mai rufe tafukan kafar su) ba? Sai Manzon Allah (sallallahu alaihi wa sallam) ya ce "Ita Mace Al'aurah ce"

Amma ita fuskar mace, abin da yake sunnah shi ne baza'a rufe ta ba a lokacin yin sallah matuqar babu maza waɗanda ba muharramanta ba a gurin.

Mafiya yawan malamai sunce wajibi ne a rufe tafukan kafa, wasu malaman kuma sunce ba wajibi bane rufe su, amma dai mafiya yawan malamai sun tafi akan wajibcin rufe kafafu gabaɗayansu a ya yin sallah.

Abu Dawuda ya ruwaito daga Ummu Salamah (radiyallahu anha) cewa an tambaye ta akan matar da ta yi sallah tana sanye da khimaar (maya fin rufe kai ko kuma karamin hijabin da bai wuce kwankwaso ba) da kuma qamees (Riga)? Sai Ummu Salamah tace: babu laifi a hakan idan dir'a (wando ko doguwar riga) ɗin nata ya rufe tafukan kafafunta.

Amma ya fi kyau a kowane irin yanayi ta rufe tafukan kafafunta domin tsallake siradin kokwanto. Saboda haka idan mace za ta yi sallah ta sanya safa (socks) yin hakan ya fi dacewa.

WALLAHU A'ALAM

Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance Damu...

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam

Post a Comment

0 Comments