Ticker

6/recent/ticker-posts

Hukuncin Sallah A bayan Wanda Yake Luwaɗi

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Menene Hukuncin Sallah Abayan Wanda Yake Luwaɗi? Kuma menene Ingancin Sallah abayansa?

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

الحمد لله.

1. Da farko idan An Tabbar da Mutum yana Aikata wata Alfasha, bai tuba daka Aikata taba, kamar wannan babban laifi mai girma, Wajibine Ayiwa mutum wa'azi da nasiha da tsoratar da shi Allah, Idan yaki tuba wajibine adakatar da shi daka limanci, acanja shi da limami wanda yake adali tsayayye akan addininsa, Wanda yake kwadayin Aikata ayyuka na tsoran Allah, Hakika Annabi sallallahu Alaihi wasallam yahana wani mutum dayayi kaki yatofar agabansa inda Alkibla take yana cikin sallah, yayi sallah a matsayin shi ne limamin mutanensa ya ce da shi ( Kai kacutar da Allah da Manzansa) Abu dawda (481) Albani yakyautatashi acikin Sahihu Abu dawda.

Ina kuma ga mai aikata wannan laifi mai girma, lallai shi ne yafi kamata da can-cantar ahanashi limancin mutane.!!.

Saboda sanya shi yazama limami girma mawace agareshi, Fasiqi kuma baya cikin wadanda ake girmamawa, limami kuma Mutane Suna koyi da shi ne a galibi, suna koyan ilmi daka wajansa, suna karɓar Inda yafuskantar dasu a harkar rayuwa kota addini, yana kuma shiryar dasu, duk lokacinda yazama tsayayye zai kasance yafi kusa da mutane su Amfana dashi, kuma Sudunga karɓar zancensa..

Amma idan yazama fasiqine Mutane bazasu dunga karɓa daka wajansaba, Saidai ma yazama sababi na lalacewar wasu yafitinesu da irin nau'in fasikancin dayake aikatawa, Allah ya Tsare.

2. Abu Na biyu: Ingancin Sallah Abayan fasiqi, Hakika malamai sunyi saɓani akan hakan, Abun da jamhur din malamai suka tafi akai shi ne: Ingantuwar sallah abayansa tareda karhancin yinta abayansa.

Imamun Nwawi acikin Majmu'u fatawa ( 4/151) ya ce:

" Sallar Abdullahi ɗan Umar Abayan hajjaju bin yusuf ta tabbata acikin Sahihul Bukhary da waninsa hadisai masu yawa ingantattu sun nuna ingantuwar Sallah Abayan fasiqi da kuma jagorori Azzalumai fitinannu.

Malaman mu sukace: Sallah abayan fasiqi ingantacciya ce ba haramun bace, saidai makaruhice, haka makaruhice yinta abayan ɗan bidi'a Wanda bai kafirta da bidi'arsa ba,

Imamu Shafi'i ya nassanta acikin Muktasar karhancin sallah Abayan fasiqi da dan Bidi'a, idan kuma mutum yayi ta inganta.

Shaikul Islam ibnu taimiyyah Allah yajikansa da rahama Acikin Fatawa dinsa (23/341) Ya ce:

" Idan mutum yana cikin masu kulada addini to wanda yafi sanin Alqur'ani da Sunnah wajibine agabatar da shi akan wanda bai kaishi ba, idan kuma daya fajirine kamar wanda aka sanshi da karya da fajirci dacin Amana da yaudara, da sauran nau'ikan fasiqanci, dayan kuma muminine cikin ma'abota tsoran Allah, to nabiyun shi ne yafi can-canta. da limanci, idan yana cikin ma'abotanta.

Idan fasiqin masanine makaranci to lallai Sallah abayan fasiqi an hana, hani na haramci awajan wasu malamai, awajan wasu kuma hanine na tan-tancewa, bai halatta jagorantar da fasiqi ba tareda cewa za a iya sanya mutumin kirki.

Yasake cewa a (23/375)

" Bai halatta a jagorantar da maishan wiwi ko wanda yake aikata munanan ayyuka ya limanci mutane ba, tareda cewa za a iya sanya mutumin kirki,.

Malamai Sunyi ittifaqi akan karhancin Sallah abayan fasiqi, saidai sunyi saɓani wajan ingancin sallar abayansa, wasu sukace ba ta ingantaba kamar faɗin Malik da Ahmad a ɗaya da cikin ruwayotinsa,.

Wasu sukace: Ta inganta kamar maganar Abu hanifa da Shafi'i, Basuyi jayayya akan bai kamata sanya shi yazama limami ba.

Duba Sharhin Mumti'i ala zhadul Mustaqini'i (4/304, 308).

3. Na Uku: Malamai Sun rarrabe abun da ya waba a'aikatashi akan limaminda yake fasiqi, Mazinaci mai shan giya dan luwadi ɗan fashi ɓarayo makaryaci azzalumi Annamimi da sauran nau'ikan fasiqanci,* ya zo afatawa Lajnatul da'imah.

" Idan limamin Masallaci fasiqine yaki jin nasiha wajibine acireshi, idan hakan zai iyu, fitina bazata faru ba, idan bazai iyuba wata fitinar datafi fasiqancinsa tana iya biyo baya, wajibine ayi Sallah bayan mutumin kirki wanda ba shi ba, dan zaburar da shi dakuma tsoratar dashi, idan babu wata fitina dazata biyo baya akan hakan.

Idan Bazai iyu ayi sallah abayan wanin saba, yahalatta ai sallah abayansa, dan tabbatar da Maslahar Al'umma..

Idan Ana tsoran faruwan fitina sai ayi sallah abayansa dan dakile fitina, da ɗaukar Abun da yafi sauqin cuta sama dawanda illarsa babbace.

Fatawa lajnatul da'imah (7/370)

Dan haka sallah abayan mai luwaɗi ingantacciya ce Matukar ya iyata, Amma makaruhine, laifin luwaɗinsa shi kaɗai yashafa bazai shafi ingancin sallar mamu dasuke bayan saba.

Domin Allah madaukakin Sarki ya ce: Ba'a dora laifin wani akan wani.

WALLAHU A'ALAM

Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance Damu...

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam

Post a Comment

0 Comments