Ticker

6/recent/ticker-posts

Tana Neman Taimakon Kuɗi Awurin Tsohon Saurayinta Bayan Ta Yi Aure

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Assalamu Alaikum. Mutun ne ya nemi mace tun tana budurwa amma Allaah bai ƙaddara shi ne mijinta ba. Kuma yau bayan shekaru ashirin sai gashi take neman taimakon kuɗi a wurinsa, wai tana ɗaukar shi a kamar yayanta ne kawai! Mene ne abin yi?

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

Wa Alaikumus Salaam Wa Rahmatul Laah.

Bayan an ɗaura aure kuma ta tare duk nauye-nauyen mace na ciyarwa da tufatarwa da magani da sauransu, sun koma kan mijinta ne. Ko iyayenta da sauran ’yan uwanta bai zama haƙƙi na dole a kansu su ɗauki nauyin komai na irin waɗannan abubuwan ba. Sai dai ko ta fuskar kyautatawa ko kuma idan ta shiga cikin halin ƙunci, kamar a lokacin da mijinta ya talauce. Har haka haƙuri da nema a wurin Allaah shi ne ya kamaci mai Imani da taƙawa kuma mai neman kare mutunci.

Fatimah Az-Zahraa (Radiyal Laahu Anhaa) wadda ta ke sashen jikin ma’aiki (Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallam) ce, kuma wadda duk abin da ya cutar da ita shi ma ya cutar da shi, ita ce ta tafi neman taimakon baiwa guda ɗaya daga wurin mahaifinta Annabin Rahama (Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallam) saboda ta riƙa taimaka mata a kan ayyukan gidan aurenta, amma sai ya biyo ta da cewa:

« إِذَا أَخَذْتُمَا مَضَاجِعَكُمَا تُكَبِّرَا أَرْبَعًا وَثَلاَثِينَ ، وَتُسَبِّحَا ثَلاَثًا وَثَلاَثِينَ ، وَتَحْمَدَا ثَلاَثَةً وَثَلاَثِينَ ، فَهْوَ خَيْرٌ لَكُمَا مِنْ خَادِمٍ »

Idan kun tafi wurin kwanciya ku yi: SUBHAANAL LAAH sau talatin da uku, da ALHAMDU LIL LAAH sau talatin da uku, da ALLAAHU AKBAR sau talatin da huɗu. Shi ne ya fi muku alkhairi fiye da mai hidimar da kuke nema. (Sahih Al-Bukhaariy: 3705)

Amma idan aka bincika kuma aka tabbatar da cewa matar tana cikin tsanani da ƙuncin rayuwa a gidan mijinta, kuma iyaye da sauran danginta sun kasa ko sun ƙi taimaka mata, to ba za a hana musulmi ya taimaka wa yar uwarsa musulma ba. Annabi (Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallam) ya ce:

« مَنْ نَفَّسَ عَنْ مُؤْمِنٍ كُرْبَةً مِنْ كُرَبِ الدُّنْيَا نَفَّسَ اللَّهُ عَنْهُ كُرْبَةً مِنْ كُرَبِ يَوْمِ الْقِيَامَةِ وَمَنْ يَسَّرَ عَلَى مُعْسِرٍ يَسَّرَ اللَّهُ عَلَيْهِ فِى الدُّنْيَا وَالآخِرَةِ وَمَنْ سَتَرَ مُسْلِمًا سَتَرَهُ اللَّهُ فِى الدُّنْيَا وَالآخِرَةِ وَاللَّهُ فِى عَوْنِ الْعَبْدِ مَا كَانَ الْعَبْدُ فِى عَوْنِ أَخِيهِ »

Duk wanda ya yaye wa wani musulmi wata damuwa daga cikin damuwoyin duniya, Allah zai yaye masa damuwa daga cikin damuwoyin ranar ƙiyama. Kuma duk wanda ya sauƙaƙa wa wanda ke cikin ƙunci, Allaah zai sauƙaƙa masa a duniya da lahira. Kuma duk wanda ya rufa sirrin musulmi, shi ma Allaah zai rufa sirrinsa a duniya da lahira. Kuma Allaah yana cikin taimakon bawa matuƙar dai bawan yana cikin taimakon ɗan’uwansa. (Sahih Muslim: 7028).

Allaah ya shiryar da mu.

WALLAHU A'ALAM

Sheikh Muhammad Abdullaah Assalafiy

Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance Damu. . .

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://whatsapp. com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www. facebook. com/groups/336629807654177

𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

https://t. me/TambayoyiDaAmsoshi

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam

Post a Comment

0 Comments