NA
IBRAHIM GARBA
AMINCEWA
Wannan kundin bincike na Ibrahim Garba mai lamba (Adm, 1610104009), ya cika ƙa’idoji da aka shimfiɗa dangane da neman takardar
shaidar digirin farko na (B.A Hausa) A Sashen Nazarin Harsuna da Al’adu na Jami’ar
Tarayya Gusau.
SADAUKARWA
Na sadaukar da wannan aiki ga mahaifana ALH Garba Safsafci bakin total Gusau da mahaifiyata Hajiya Rabi Ibrahim bakin total Gusau da kuma ‘yan uwana da suka taimaka a lamarin karatuna. Ina fatan Allah Ya saka masu da alheri alfarmar Shugabanmu Annabi Muhammadu (S.A.W).
GODIYA
Dukkan yabo da godiya sun tabbata ga Allah Madaukakin Sarki, Mai kowa Mai komai da a ba ni rai da lafiya da ikon gudanar da wannan bincike.
Tsira da amincin Allah (SWT) su tabbata ga Fiyayyen halitta wato Annabi Muhammadu (SAW) tare da iyalan gidansa da Sahabbansa da duk magoya bayansa tun farko har ya zuwa ranar ƙarshe.
Godiya ta musamman ga dukkan bayin
Allah da suka taimaka domin ganin wannan bincike ya kammala, musamman ga mahaifiyata hajiya Rabi Ibrahim
bakin total Gusau, wadda ita
ce ta jajirce da kuɗinta, da addu’o’i, da tanbihi wajen ganin na cimma nasarar
kammala wannan karatu da ma ‘yan uwana kamar su; Sa'adatu Garba total, Umma Garba
total, Sha'awanatu Garba total, Hussaina Garba total.
Bayan haka,
ina godiya ta musamman ga malammaina, tare da jinjina garesu, da suka tarbiyantar
da mu a fagen ilimi, Allah Ya saka masu da gidan Aljannah, Allah ya faranta masu
rayuwar su duniya da lahira amin. Malaman sun ha]a da; Prof. Yakawada Zaria, Prof.
M. L. Amin Zaria, Prof. Balarabe Zaria, Prof. Aliyu Muhammadu Bunza UDUS, Prof.
Aliyu Musa B.U.K,, Dr Tahir Zaria, Dr Adamu Rabiu Bakura wanda ya ɗauki tsawon lokaci yana duba
wannan aikin tare da taimakawa wajen ganin an aiwatar
da dukka gyare-gyare da za su saita wannan bincike, Dr musa fadama, Mal. Rabi’u Aliyu ɗangulbi, Mal. Isah S Fada, Mal. Bashir, Mal.Muhammad Arabi Umar da Mal. Abu Ubaida Sani, da kuma Malama Halimatu Kurawa da ma duk wani malami da
ya koyar da ni wanda ban samu damar sanyo sunansa ba a Sashen Nazarin Harsuna da Al’adu da ma inda
na yi aron kwas don cika sharuɗɗan karatu da wanda na sani ya taimaka da ban san ma ya taimaka
ba ko da a tsaron jarawa. Allah Ya saka masu da alheri, amin.
Godiya ga abokan karatuna, da suka taimaka a fagen karatu,
Mahadi Almustapha Ajiya Gusau,
Yusif Muhammad Kwalli Kano, Umar
muhammad ammani, Sadam yusuf Zurmi, Abbas muhammad gidan dawa, Amir tujjani, Abdulrashid
Bala tsafe, Aminu Muhammad Gusau, Abdulrashid
Isma’il Kaduna,, Saudatu Ɗalhatu Sokoto, Binta Gambo Gusau, Asiya Sulaiman Gusau da
Khadija Ɗanbuba Gusau, Asma'u
Ibrahim birnin Magaji da ma wanda
bai ji na ambaci sunansa ba saboda rashin samun damar rattaba su a cikin wannan
bincike. Na gode, Allah Ya saka masu da alhairi, kuma Ya ƙara muna son juna. Allah Ya nuna muna wannan karatu ya amfani
kowa daga cikin mu amin.
BABI NA ƊAYA
GABATARWA
1.0 SHIMFIƊA
Sana’ar ƙira daɗaɗɗiyar
sana’a ce a duniya baki ɗaya. Ba za a iya
cewa ga lokacin da Hausawa suka fara ƙira ba. Sai daiza a iya kirdadon lokacin da Bahaushe
ya samu hanyar neman abinci da mazauni da zai zauna tare da iyalinsa da dukkan
abin da ya mallaka. Ita dai sana’ar ƙira sana’a ce ta samar da kayan amfani na aikin gona, makamai don
kare kai, wasu abubuwan amfani da rayuwa ke buƙata da dai makamantan su. Domin samun sauƙin gudanar da wannan bincike, an kasa shi gida biyar
kamar yadda dokar rubuta kundi ta wannan makaranta ta tanada. An raba shi bisa
ga tsarin babi-babi har babi biyar.
Babi na farko zai ƙunshi manufar
bincike da farfajiyar bincike da
muhimmancin bincike hanyoyin gudanar da bincike daga karshe a zo da naɗewa. A babi na biyu
kuwa nan ne aka yi bitar ayyukan da suka gabata tun daga bugaggun litattafai da
kundayen bincike da maƙalu da mujallu da aka buga a cibiyoyin
ilimi daban-daban.
Babi na uku mai taken “Luguden Ma’anonin Tubalan Bincike”
ya ƙunshi ma’anar zamani, ma’anar sana’a, nau’o’in sana’a, ma’anar ƙira, nau’o’in ƙira, tsokaci a kan
garin Gusau wanda shi ne farfajiyar da ake gudanar da bincike. Daga nan kuma
sai naɗe tabarmar wannan babi.
A babi na huɗu kuwa, wanda ke da taken “Tasirin Zamani a Sana’ar Ƙira a Garin Gusau” . wannan babi shi ne zuciyar wannan binciuke. A cikinsa ne za aka zo da
bayanin kafuwar maƙeran farko a garin Gusau, hanyoyin
samar da kayan sarrafawa kayan aikin ƙira, abubuwan da
ake ƙerawa, dangantakar maƙera da al’umma, muhimmancin ƙira ga al’umma, tasirin
zamani a sana’ar ƙira a garin Gusau, bunƙasar maƙera da sauyawar
zamani a garin Gusau, tasirin zamani a kan kayan sarrafawa, zamani da abubuwan
sarrafawa, sauye-sauyen zamani a kan abubuwan da ake ƙerawa sai a naɗe tabarmar wanna babi.
Babi na biyar wanda shi ne babi na ƙarshe a wannan bincike, a cikinsa ne za a naɗe tabarmar wannan
bincike gaba dayansa. An zo da sakamakon bincike sai taƙaitawa da kammalawa. An kuma zo da shawarwari dangane da
abinda binciken ya gano.
1.1 MANUFAR BINCIKE
Bincike dangane da sana’ar ƙira musamman idan aka duba irin tasirin da zamani ya yi a
cikin sha’anin wannan sana’a abu ne mai matuƙar burgewa. Duk wani
abin da ɗan Adam ya ƙuduri ya
aiwatar a rayuwarsa,
za a tarar
cewa, lallai, akwai wata manufa ta musamman da ta wajabta
masa aiwatar da wannan
abu.
Wannan bincike na da manufofi na
aiwatar da shi da suka haɗa da:
i.
Bayyana
sana’ar ƙira ga al’ummar garin Gusau.
ii.
Fito da
wasu kayyaki da sana’ar ke samarwa domin amfanin al’umma.
iii. Bayyana irin tasirin da zamani ya yi ga sanaar da kuma kayan da aka samu sakamakon tasirin zamani a kan sanaar.
1.2 TAMBAYOYIN BINCIKE
Domin samun nasarar gudanar da wannan bincike, an zo da
wasu tambayoyi da suka yi wan wannan bincike jagora wajen neman matsalar da ta
haddasa aikin binciken. Waɗannan tambayoyi kuwa sun haɗa da:
i.
Yaya
sana’ar ƙira take a garin Gusau?
ii.
Waɗannan kayayyaki
sana’ar ke samarwa domin amfanin al’umma?
iii.
Wane
irin tasiri zamani ya haifar ga sana’ar ƙira? Ko akwai kayan
da aka samu sakamakon tasirin zamani?
1.3
FARFAJIYAR BINCIKE
Kafin a shiga bayanin farfajiyar bincike, yana daga cikin ƙa'ida ta bincike, ɗalibin bincike ya
yi nazari a kan abin da yake kusa da shi,
wato muhalin ko farfajiyar da yake zaune, domin samun ingantattun
bayanai game da abin da yake bincike.
Wikepedia (2019) an bayyana muhallin bincike da
cewa, shi ne wuri na musamman wanda aka
gudanar da bincike a kan wani abu da ke da mazauni a wurin, kamar al'umma, abubuwa da sauransu, ta hanyar
littatafai, da muƙalu, da kuma
tarukan ƙara wa juna sani, domin samun wani
sakamako.
Farfajiyar da ake gudanar da wannan bincike ita ce Gusau
babban birnin jihar Zamfara. An gudanar da nazari a kan tasirin zamani a sana'ar
ƙira a garin Gusau,
inda aka gana da mutanen da ke gudanar da wannan sana'a ta ƙira domin jin yadda suke gudanar da ita a
jiya da kuma yau. An kuma nemi sanin hanyoyin da suke bi
wajen samun kayan sarrafawa, da abubuwan da suke sarrafa na wannan sanaa.
1.4 MATSALOLIN BINCIKE
A
lokacin da mai bincike yake gudanar da aikin bincike, dole ne ya ci karo da
wasu matsaloli, kamar yadda sunan ya nuna. Matsala na nufin duk wani ƙalubalen da mutum ya samu a wajen aikin bincikensa, ko kuma duk wani
cikas da mutum ya ci karo da shi. A lokacin da wannan bincike yake gudana, an
samu matsalolin da suka haɗa da; rashin
samun haɗin kan wasu daga masu sana’ar ƙira. Wasu
masu sana’ar kuma ba su iya fito da dukkan bayanai na sana’ar ba saboda a nasu
zato ana kwasar sirrin sana’ar ne don a yi masu kishiya ko a fi su ƙwarewa lura da cewa ni ɗalibi ne mai koyon
abubuwa.
A yayin
da binciken yake gudana, an samu ƙarancin lokaci, ga
waɗanda aka yi hira da su, saboda sai sun yi aiki a ranar,
kana su ci, ko su ciyar da iyalinsu.
Ya sa hankalinsu ke
rabuwa biyu, sai kuma ƙarancin kayan aiki. Kasancewar
wannan bincike na sana’ar ƙira ne. Akwai buƙatar shigowa da
hotunan wasu ababe, domin ganin
wasu kaya da ake ƙerawa sakamakon tasirin zamani. Sai kuma matsalar rashin tsaro, da ake fama da ita wadda
ta addabi jahar Zamfara, da ma Arewacin
Nijeriya baki ɗaya.
1.5 MUHIMMANCIN BINCIKE
Muhimmancin bincike shi ne a gano
wani abu da yake ɓoye, wato a fito da shi a fili, kuma a bayyana shi, domin
a shawo kan wata matsalar, ko kuma a walwale wata matsala.
Duk wani bincike da za a gudanar a fagen ilimi, abu ne
mai muhimmanci a rayuwa, musamman wanda ya shafi sana’a. Kasancewar babu wata
al’umma da zata rayu a bisa doron ƙasa, face sai ta
samu sana’ar da take dogaro da ita. Daga muhimmancin da ke ga wannan bincike
akwai:
i.
Nusar
da matasa kan su tashi su koyi sana’o’in hannu da za su rage masu zaman banza
ko dagaro ga wani daban.
ii.
Su yi
amfani da damar da suke da ita wajen koyon sana’o’in zamani musamman abin da ya
zamani ya zo da shi don amfanin al’umma.
iii.
Binciken
ya zama
wani abin amfani ga ɗalibai masu nazarin al’adu da sana’o’in Hausawa.
1.6 HANYOYIN GUDANAR DA BINCIKE
Domin samun sauƙin gudanar da
wannan bincike bisa tsari mai kyau, an zaɓi a bi wasu hanyoyi da za su taimaka
wajen ganin an kammala wannan bincike cikin tsari mai kyau. Hanyoyin da aka bi
wajen tattara muhimman bayanai domin aiwatar da wannan bincike suna da yawa. Misali:
1.6.1
HANYOYIN TATTARA BAYANAI NA FARKO
Akwai
wasu hanyoyi da suka dace wannan bincike ya bi ta kansu. Kuma su waɗannan hanyoyi su ne
za a fara tuntuɓa kafin a je ko’ina. Hanya ta hira da aƙalla mutum biyar ko fiye daga cikin masu sana’ar ƙira a
cikin garin Gusau. Don haka waɗannan hanyoyi sun haɗa da; Hira da
tattaunawa da kuma ziyara.
1.6.1.1
HIRA
Kasancewar
sana’ar ƙira tana da matuƙar amfani wajen samar da kayayyakin aiki na tafiyar da
rayuwa ya sa na niƙa gari na samu wasu har a bakin aikinsu na kuma nemi mu
tattauna da su domin jin ta bakinsu. Don haka na yi hira da wasu masu sana’ar ƙira a
garin Gusau a lokuta mabambanta. Ga dai wasu da bincike ya samu zantawa da su.
MUTANEN DA AKA YI HIRA DA SU
S/No |
Suna |
Shekaru |
Matsayi |
Adireshi |
Rana |
1 |
Maƙera Aliyu Barau |
67 |
Sarkin Maƙeran Sarkin Katsinan Gusau |
Sabuwar Kasuwa Gusau |
12/7/2023 |
2 |
Ummaru Maƙeri |
60 |
Maƙeri |
Gadar Zangila |
13/7/2023 |
3. |
Bala Musa |
35 |
maƙeri |
Fonfon Maishanu Gusau |
14/7/2023 |
4. |
Hussaini Maƙeri |
46 |
maƙeri |
Bakin Silma |
15/7/2023 |
5. |
Mal. Lawali Umar |
64 |
Maƙeri |
Sabuwar kasuwa, Gusau |
16/7/2023 |
1.6.1.2
ZIYARA
A ziyarar da aka kai a wasu makarantun ƙasar nan domin samun damar ganin wasu ayyuka da suka haɗa da
karance-karancen bugaggun littattafai da kundaye da muƙalu da Mujallu domin zaƙulo wasu bayanai masu nasaba da wannan bincike an kai
ziyara ɗakunan karatu da suka haɗa da;
·
Kwalejin
Ilmi da Ƙere-ƙere ta Gwamnatin Tarayya da ke Gusau, (F.C.E.T),
·
Ɗakin karatu na
Kwalejin Kimiya da Fasaha da ke Gusau, watau ZACAS
· Ɗakin karatu na Jami’ar Tarayya da ke Gusau wato F.U.GUS
1.6.2
SAURAN
HANYOYIN TATTARA BAYANAI
Bincike ya tattauna da wasu masu ilmi kan harakar sana’a
musamman lura da zamani ya yi
tasiri a wasu sana’o’in inda
aka samu damar tattauna wasu muhimman batutuwa da suka shafi binciken.
1.7 NAƊEWA
Wannan babi shi ne babi na farko wanda aka yi gabatarwa ta gaba ɗaya. An bayyana dukkan abin da aka yi bincike a kai tun daga babi na farko har zuwa na biyar. Babin yana ɗauke da manufar bincike da tambayoyin bincike da muhimmancinsa. An kuma zo da hanyoyin da za a bi domin gudanar da wannan bincike kamar dai yadda aka gani a sama.
BABI NA BIYU
BITAR AYYUKAN DA SUKA GABATA
2.0 GABATARWA
Duk da irin yadda ake ganin cewa ba a yi wani abin da ya
taka kara ya karya dangane da tasirin zamani a Sana'ar ƙira ba, to ba za a rasa wasu abubuwa da suka yi kama da
hakan ba, musamman idan aka yi la'akari
da irin bincike da masana da ɗalibai suka gabatar a kan sana'ar ƙira.
Wannan fasali ya waiwayi ɗan abin da ya
samu, domin mu
ga yadda yanayi ya kasance game
da bitar ayyukan da suka gabata, waɗanda suka haɗa da bitar
littattafan da aka wallafa, da kundayen
bincike, da muƙalu da mujallu, da
hujjar cigaba da bincike da hasashen bincike,
daga ƙarshe kuma sai a naɗane wannan babin.
2.1 BITAR AYYUKAN DA SUKA GABATA
Babu shakka ya zama wajibi ga duk wanda zai aiwatar da
bincike, ya tsaya ya dubi ayyukan magabata domin samun haske game da yadda suka
gabatar da nasu ayyukan. Don ta yin haka
ne za a fahimci inda aka kwana da kuma inda za a tashi.
Wannan ne ya tilasta a waiwayi aikace-aikacen ayyukan da masana suka aiwatar domin samun ƙarin haske, Daga cikin aikace-aikacen da a gudanar waɗanda aka yi bitar su, sun haɗa da: Bugaggun littattafai, da kuma muƙalu, tare da kundayen bincike, kamar yadda za mu gani ɗaya bayan ɗaya.
2.2 WALLAFANFUN LITTATTAFAI
Masana da dama sunyi rubuce-rubuce,
musamman a kan sana'ar ƙira, inda suka tofa
albarkacin bakinsu, musamman a kan ma'anar ƙira da kashe-kashenta da muhimmancinta da kuma gudummuwar da take bayarwa ga al'umma, daga cikin waɗannan masana akwai.
Alhasan, (1982) Shi ma a cikin littafinsa mai suna
"Zaman Hausawa" ya yi bayani
wasu sana'o'in gargajiya tare da bayyana muhimmancinsu, daga cikinsu
akwai ƙira, kayan da ake
amfani da su a wajen gudanar da sana'ar ƙira, ya kuma kawo
kayan da maƙera ke ƙerawa, haka kuma ya yi bayanin kashe-kashenta. Littafin
Alhassan ya taimaka wajen sanin kayan da maƙera ke kerawa. Haka kuma littafin bai ce komai a kan
Gusau ba. Bai kuma yi bayanin tasirin zamani ga sana’ar ƙira ba. Da wannan
na samu damar ci gaba da aiwatar da wannan bincike.
Bagari, (1986), a cikin littafinsa
mai suna "Sana'o'in Hausawa Na
Gargajiya" masanin ya yi ƙoƙarin bayar da gudummuwarsa dangane
da sana'o'in gargajiya na Hausawa, kamar
jima, fawa, gini, saƙa, ƙira, noma da sauransu,
masanin ya yi tsokaci a kan sana'ar ƙira, da masu
gudanar da ita, kayan aikin ƙira, da kayan da maƙera ke ƙerawa, gudummuwar
da maƙera ke bayarwa ga al'umma, da sauransu. Wannan littafi na
Bagari ya taimaka matuƙa wajen samun tudun dafawa dangane
da wannan bincike.
Gusau, M.B. da Gusau, M.S (2012). A cikin littafinsu mai
take: Gusau Ta Malan Sambo sun kawo
bayanin sunan Gusau da kirarinta, da
ma'anar kalmar Gusau, Haka kuma an yi
bayanin kafuwar Gusau da haɓakar ta wanda ya kunshi tarihin garin Gusau da mutanenta
na farko da bunƙasarta da tsarin sarauta da mulki,
da kuma tarihin rayuwar sarakuna tun daga jiya har yau, Haka kuma an kawo yanayin sana'o'in da ake yi
a cikin garin Gusau wanda sana'ar ƙira na ɗaya daga cikinsu.
Madobo,(Shekara babu) A cikin littafinsa mai suna "ciniki da sana'o'in
a ƙasar Hausawa"
masanin ya fara da kawo ɗan taƙaitaccen tarihin ƙira, inda ya bayyana ƙira da tsohuwar sana'a ce, ya kuma yi bayanin kashe-kashenta da kuma
kayan aikin ƙira tun daga wajen da maƙera ke zama su aiwatar da aikinsu da kuma abubuwan da
suke ƙerawa, kamar fartanya, galmar shanu, takobi, manjagara da
sauransu.
2.3 MUƘALU DA MUJALLU
Muƙalu da mujallu su ne takardu masu ɗauke da bincike na
ilimi, mafi akasarin waɗannan ana gabatar
da su ne a lokuttan tarurrukan ƙara wa juna
sani. game da sana'o'in gargajiya wanda ƙira tana daga cikinsu, a matakai daban-daban, an gabatar da muƙalun da dama da
suka haɗa da:
Muhamud. R. (2018) ya gabatar da muƙalu mai taken Sana'ar Ƙira a Gariin Gusau,"
ya kawo muhimman abubuwan da suka shafi sana'ar ƙira. Wannan muƙala ta taka muhimmiyar rawa wajen fito da bayanai a kan
sana'ar ƙira a garin Gusau, ya kuma fito fa abubuwa kamar: Tarihin ƙira a garin Gusau, wurare ko mazaunin da ake yin ƙira a Gusau, mutane da ke yin ƙira a garin Gusau, kKashe-kashen ƙirar da ake yin a Gusau, kayan da ake ƙerawa a Gusau da sauransu,
Mujallar al'ummar Hausawa, wannan mujallar sun gabatar da muƙala mai taken "Sana'ar Ƙira a Wajen Bahaushe" sun fara gabatar da yadda ake aiwatar da
wannan sana'ar ta ƙira da kuma yadda ake sarrafa ƙarafa, Haka kuma
sun kawo kayayyakin da sana'ar ƙira take samarwa ga
al'umma don tallafawa rayuwar Hausawa. Haka kuma sun yi ƙarin bayani a kan tasirin zamani da kimiyya a kan sana'ar
ƙira, kamar gyararren
ƙarfe da na'urar gutsure ƙarfe, da ruler, da wanda maƙera ke amfani da shi.
2.4 KUNDAYEN BINCIKE
Abubakar. B. da
wasu (2004). sun yin nazari ne a kan "sana'ar ƙira a garin Gusau"
wanda suka gabatar a sashen Turanci da Hausa na kwalejin ilimi ta maru
jahar zamfara, sun kawo ma'anar ƙira da
kashe-kashenta da muhimmancin ƙira a cikin al'umma
da kuma kayan da ake ƙerawa a garin Gusau da wuraren da maƙeru suke a cikin garin Gusau da sauransu.
Ɗankande da wasu (2017). sun gabatar da bincikensu ne a
kan "Nazari a Kan Tasirin
Siddabarun Maƙera a Sana'ar Ƙira" wanda
suka gabatar a sashen Hausa na Tsangayar Harsuna na kwalejin ilimi da ƙere-ƙere ta Gwamnatin
Tarayya da ke Gusau jahar zamfara, sun
fara da ba da tarihin maƙera a ƙasar Hausa kamar haka: Samuwar ƙira a ƙasar Hausa, nau'o'in
maƙera a ƙasar Hausa, tasirin
ƙira ga al'umma, kayan aikin ƙira, al'adun maƙera, abokan wasan
maƙera da siddabarun maƙera, da sairansu. Wannan bincike na Ɗankande ya taimaka wajen gina wannan aiki.
Shafa'atu da wasu (2016). sun gabatar da nazarinsu ne mai taken "Nazari a kan Wasanni Tsakanin Maƙera da Wanzamai a Yankin Zamfara" wanda suka gabatar a sashen Hausa na
Tsangayar Harsuna na kwalejin ilimi da ƙere-ƙera ta Gwamnatin
Tarayya da ke jahar zamfara, sun fara ɗora aikinsu nr a kan asalin
wanzamai, daga nan suka cigaba da kawo abubuwa kamar haka: Ma'anar wanzanci, kayan
aikin wanzamai, ire-iren wanzamai, abokanan
wasar wanzamai, ma'anar ƙira, ire-iren maƙera, ma'anar wasa, cigaban da wasanni ke haifarwa
tsakanin masu sana'ar gargajiya, matsalolin da wasa ke haifarwa tsakanin masu
sana'o'i, da yadda za a magance matsalolin da wasa ke haifarwa ga masu
sana'o'i, da sauransu.
2.5
HUJJAR CI GABA DA BINCIKE
Idan muka yi la'akari da bayanan da suka gabata, a inda muka yi tankaɗe da rairaya a kan
nazarce-nazarcen da aka aiwatar a ƙoƙarin mu na
kwatanta ƙudurin wannan bincike da abin da magabata a fagen nazari
suka aiwatar, za a lura cewa har yanzu
ba a ci karo da wani bincike da aka gudanar dangane da tasirin zamani A Sana'ar
Ƙira a Garin Gusau" ba, sai dai alaƙa da wannan bincike,
wanda aka gabatar (2004) haka kuma shima wannan binciken sun mai da akalarsu ne a kan sana'ar ƙira ne a garin Gusau, ba su yi wani bayani a kan tasiri
zamani a sana'ar ƙira a garin Gusau ba,
Kowane al'amari na rayuwa yana buƙatatar hujja a wajen cigaba da aiwatar dashi, wannan bincike da ake kan gudanarwa yana da
matuƙar muhimmanci, domin a iya bincikena ban yi karo da wani
bincike mai irin wannan taken aikin da nake gudanarwa sai dai mai alaƙa da shi Saboda haka, cigaba da wannan binciken zai
taimaka wa masu sha'awar bincike irin wannan, wajen sauƙin fahimtar tasirin da zamani ya yi wa sana'ar ƙira a garin Gusau.
2.6 HASASHEN BINCIKE
Hausawa na cewa " maiki
mai hangen nesa"
A bisa wannan hasashen da kuma tsinkaya da aka yi ko kuma a bisa wannan ƙudirin da na yi domin bunƙasa ko haɓaka harshen Hausa na ga ya da ce nayi wannan bincike
domin ƙoƙarin taskace bayanai ganin yadda
abubuwa sukan sassauya ta yadda matasa masu tasowa, za su riske shi.
Bugu da ƙari kuma na yi
wannan bincike ne domin ganin cewa akwai karanci littafai na Hausa musamman na
adabi wanda ya shafi ire-iren waɗannan mashahurar sana'o'i na gargajiya na Hausawa, Shi ya sa na yi tunani da hangen nesa na
ganin cewa irin wannan bincike ko nazari a kan waɗannan sana'o'i zai ƙara bunƙasa adabin Hausawa. Abu na gaba kuma duk a bisa wannan
hasashen shi ne ina ganin cewa wannan bincike zai zama abun dubawa a makarantun
na gaba da sakandare, Domin a saka shi a cikin ɗakin karatu don na baya su karanta kuma suƙaru.
Haka kuma wannan hasashen ana saran zaƙulo abubuwa sabbi dal da kimiyyar zamani ta kawo wa
sana'ar ƙira a cikin garin Gusau, domin
amfanin al'ummar wannan garin da ƙasa baki ɗaya.
2.7 NAƊEWA
Wannan babin ya fara ne da gabatarwa tare da bayyana irin ayyukan da aka yi bita a binciken da ya gabata, domin waiwaye a kan ayyuka masu ƙarin haske, ko kuma masu shige da irin wannan aiki da suka haɗa da bugaggun littattafai masu alaƙa da wannan aiki, da kuma muƙalu, da mujallu, da kuma kundayen bincike, duk waɗannan ayyuka babu mai take irin wannan aiki, sai dai alaƙa.
BABI NA UKU
LUGUDEN MA'ANONIN TUBALAN TAKEN BINCIKE
3.0 SHINFIƊA
Wannan babi yana bayani ne a kan ma'anar zamani, da kuna
ma'anar sana'ar ƙira, da ma'anar Gusau, da kafuwar
Gusau, da Haɓakar garin Gusau, da Ganuwar Gusau, da kuma unguwannin
garin Gusau, da ƙarshe wannan babin ya zo da naɗewa,
1.1 MA'ANAR ZAMANI
Zamani shi ne sauyawar ɗabiu, halaye, al'adu, da kuma zamantakewar al'umma a
cikin lokaci. Haka kuma ana iya
fassara zamani da shuɗewar lokaci ko ƙarni ko wa'adi ko
kuma sa'a. A wata
ma’anar kuma, ana iya kallon zamani a matsayin sabon yanayi ko kuma shigowar
sabbabbin abubuwa a cikin lokaci da ake ciki.
Haka kuma masu iya magana na cewa zamani riga, Ta hanyar
zamani ne ake samun tasirin sabbin abubuwa, waɗanda kan shafe
tsofaffin abubuwa a daina amfani da su gaba ɗaya, shi kuwa
tasiri yakan shigo da da sabbin abubuwa ne, domin samun cigaban rayuwar ɗan Adam ta yau da
kullum.
3.2 MA'ANAR SANA'A
Sana'a wata hanya ce da ɗan Adam kan ta'allaƙa a kanta domin samun abin masarufi, wadda ta shafi
sha'anin kasuwanci, wato sha'anin saye da sayarwa. Ga Bahaushe sana'a ita ce ƙashin bayan tattalin arzikinsa.
Garba, (1991) ya bayyana sana'a da
cewa ita ce ginshiƙin rayuwar tattalin arzikin yau da
kullum na Hausawa, tare da manyan hanyoyin gano martabar mutum da kuma ƙasaitarsa da matsayinsa a cikin al'umma. Baya ga noma da
ya kasance ruwan dare, Hausawa da wasu sana’o’i domin samun abinci a lokacin
rani.
Madabo (1976) A ra'ayinsa ya bayyana sana'a a matsayin daɗaɗɗiyar
al'ada da ta nuna Hausawa a idon duniya, ta kuma bunƙasa ƙasar Hausa ta yadda
baƙi suke zaune a cikin jin daɗi sakamakon
sana'o'i daban-daban.
3.3 NAU'O'IN SANA'O'IN A GARIN GUSAU
Sana’a
dai ita ce aikin da mutum ke yi don samun abinci. CNHN (2006:386) Sana'o'in gargajiya su ne sana'o'in da
Hausawa suke yi tun kafin saduwarsu da baƙin al'umma kamar Larabawa da Turawa da sauransu. Hausawa
sun tashi tsaye da yin sana'o'in gargajiya daban-daban, kuma kowace ƙasa daga cikin ƙasashen Hausa akwai
sana'o'in da suka fi
shahara da su. Mutanen garin Gusau ba kanwar lasa ba ne a wajen gudanar
sana'o'i tun tali-tali, Allah ya
albarci garin Gusau da al'umma masu sana'o'in na gargaji daban-daban,
daga cikin Sana'o'in mutanen Gusau suka fi
shahara da su, akwai
- Ƙira
- Saƙa
- Rini
- Noma
- Jima
- Kiwo
- Aski
- Dukanci
- Sassaƙa da sauransh.
3.4 MA'ANAR ƘIRA
Masana da dama sun tofa albarkacin bakinsu dangane da
abin da ake nufi da ƙira.
Galadanci da wasu, (1992) Sun bayyana ƙira a matsayin "Sana'ar sarrafa ƙarfe domin samar da wasu abubuwan amfani.
Alhassan H. (1982) ya bayyana mas’anar ƙira da cewa: “ƙira sana'a ce ta fasahar sarrafa ƙarfe da ke da alaƙa ta kut-da-kut da
wasu fitattun sana'o'i a ƙasar Hausa. Masu wannan
suna'ar su ake kira maƙera. Ƙira aiki ne na sarrafa ƙarfe a mayar da shi makami da sauran kayan amfanin ado,
Ana narke karfe ko tama ko azurfa ko zinari, a mayar da su wani abin amfani,
kayan Ƙira kuwa sune zuga-zugi da uwar maƙera da guduma da masaba da sallata da awartaki da
sauransu.
Sallau, (2010) ya ce "Ƙira sana'a ce da aka fi yinta a lokacin rani domin
tanadar kayan aikin noma, Amma duk da hakan ana yinta a kowane lokaci na
Shekara domin samar da kayan amfanin gida na yau da kullum, Ke nan za a iya kallon Ƙira a mastsayin sana'a ta sarrafa karfe domin samarwa
al'umma wasu kayayyakin aiki domin biyan buƙatunsu na yau da kullum, a gida ko daji, ko na kare kai.
3.5 NAU'O'IN ƘIRA A GARIN GUSAU
Sana'ar Ƙira ta zauna da
gindinta sosai a garin Gusau domin akwai Maƙeran fari da Maƙeran baƙi
a) Maƙeran fari:- su ne waɗanda suke aiki da waɗansu irin ƙarafa kamar farin ƙarfe da azurfa da
tagulla da jan ƙarfe da zaiba da goran ruwa da dalma
da gaci. Su ke ƙera kananan kaya adon mata kamar
zobe da munduwa da kayan dawaki da sauransu.
Maƙerun farfaru waɗanda aka sani kuma shahararru a
cikin garin Gusau, su ne:
1.Maƙerar Bugau
2.Maƙerar Ali Sarkin Fada
3.Maƙerar Haido, da sauransu.
b) Maƙeran baƙi:- su ne
waɗanda suke aiki da baƙin ƙarfe kawai, su ke ƙera kayan noma da na yaƙi da na farauta da fawa da aski da sauransu
Maƙeran baƙi shahararru da aka
sani, sun haɗa da:
1.Maƙerar Masari
2.Maƙerar Ɗanmagaji
3.Maƙerar Kofa
4.Maƙerar Jibo
5.Maƙerar Ɗangado
6.Maƙerar Ibrahim Na'indo
7.Maƙerar Maigari da sauransu.
3.6 MA'ANAR KALMAR GUSAU
Gusau shi ne sunan babban birin jihar Zamfara CNHN,
(2006:177). Akwai bambancin ra'ayoyi a tarihance dangane da asalin kalmar
Gusau, Wasu na ganin asali ko ma'anar
kalmar Gusau ta samu ne daga ‘gusa’ wato tafi ko matsa ko ƙaraba, kamar ka ce, gusa daga nan, ko tafi daga nan, ƙaraba gaba ko matsa gaba da makamantansu. A luggance
kalmar tana nufin gurgusawa daga wani wuri zuwa wani waje, A ma'anar isɗilahi wato ta
zahiri ko ta aro kuwa kalmar tana nufin sunan gari.
Haka kuma akwai wasu dalilai da dama waɗanda masana tarihi
da ilmin harshe suka bayyana game da sunan Gusau, daga cikinsu akwai
Muhammad, M.D. da wasu (1956) sun bayyana cewa alokacin
da mutanen Gusau suke zaune a Rawayya tare sarkinsu malam Abdulƙadir, sai suka fitini mutanen Rawayya, Daga garinsu don
su sami sakewa, An ce sun fahimci mutanen Wonaka (Gusau) ba su son gori, sai
suka sami daidaituwa ra'ayi na su yi masu gori saboda ba su iya yaƙi da su, Don haka, a sakamakon wani abu da ya faru
tsakanin mutanen Gusau da mutanen Rawayya, sai suka ce masu su gusa su ba su
garinsu, ai ga nasu garin can ya za a kufai, wanna magana ta hasguɗa mutanen Gusau,
sai da sannu-sannu suka bar Rawayya, suka fawo tsohon wurinsu, To, sai suka kira
wannan wuri da suka dawo masa daga Rawayya, Gusau, wato sun gusa daga Rawayya zuwa Gusau, wurin
da aka dawo gareshi.
Ɗanƙarami, (1978) ya nuna an samo wannan suna na Gusau daga wani maharbi da ake kira Gusau inda ya ce, "a lokacin da malam Muhammadu Sambo ya baro 'Yandoto da nufin hijira, da izinin Shehu Usmanu, sai ya yi yamma da shi da jama'arsa, ya tarar da wani maharbi a wajen wanda ake ce masa Gusau, sai suka ajiye kayansu da nufin nan ne wurin da Shehu Usmanu ya yi masu ishara. Lokacin da Malam Muhammadu Sambo ya yi umurni da a ajiye kaya, sai shi ko Maharbi nan ya tashi ya ƙara gaba, bayan tashin sa ne sai suka kira wurin 'yargusau.
3.6.1
KAFUWAR GUSAU
Wasu bayanai da suka bayyana cewa akwai wata bishiya da
ake kira “Tsamiyar Tara” ta hanyar Rawayya, nan ne dogarai ke zama masu rakiyar
jama'a zuwa Rawayya saboda kare kai daga 'yan samame da 'yan fashi, Akwai ƙawurin Goga wanda yake babban zango na masu zuwa lokoja
da ikko. Ana sa ran daga nan ne aka fara kafa sansani kwanci tashi har ya zama
gari wanda a yau ake kira Gusau. Bayani da ya gabata cewa sunan garin ya samu
ne daga “gusa” sai aka gusa daga ainihin wajen da aka fara zama.
Gusau tana cikin jahar Zamfara ta yanzu, kuma tana ɗaya daga cikin
manyan ƙasashenta, sannan tana tsakanin
Sakkwato da Zariya, Kilomita 176 ne daga Zariya zuwa Gusau, daga Gusau zuwa
Sakkwato Kilomita 210 ne, Daga gabas ta yi iyaka da Ƙasar Katsina da Kwatarkwashi, daga Arewa ta yi iyaka da Ƙasar Kauran Namoda, Ta kuma yi iyaka da Ƙasar Bunguɗu ta wajen Yamma, Sannan ta yi iyaka da Ƙasar Ɗansadau ta ɓangaren Kudu.
Haka kuma Gusau tana ɗaya daga cikin
manyan gundumomin Zamfara guda goma sha huɗu (14) da suka
kunshi yankin Sakkwato Gabas a zamanin mulkin Turawa.
Yanayin ƙasar Gusau, Ƙasa ce shimfiɗaɗɗaiya wadda take a kan tudu, ba ta da yawan kwararra ko
duwarwatsu, sai dai Dutsin marbe da na kantawa, Har wa yau ƙasar tana da tsaununka jefi-jefi a wurare daban-daban,
kamar tsaununkan da ke tsakanin 'yandoto da langa-langa, akwai su kuma a Mada
da tsaunen Tutari, ita kuma Wanke dukanta tsaunuka ce, sannan akwai su a
labbo-maikomo, manyan gulaben da suka ratsa cikin ƙasar Gusau su ne, gulbin Sakkwato wanda ya fito daga ƙauyen Ɗandume ya biyo ta
Kwaren Ganuwa da Rijiya da Gidan Fakkan da Gidan Malamai ya faɗo Gusau ya zarce
zuwa Bunguɗu da Maru har zuwa Sakkwato, sai gulbin Gagare wato na
Wonaka wanda ya koma Kauran Namoda.
Haka kuma akwai ta da yanayi ƙasar noma mai laka da fadama da mai damɓa-damɓa, akwai kuma inda
ta ke da jar ƙasa wadda ba a rasa ba mai jigawa.
Akwai tsameku da suke da muhimmamcin a ambace su saboda abubuwan tarihi da suka
auku a wajensu, MISALI Tsamiyar Hasau ta Dabbakal wadda kaura Hasau, Sarkin yaƙin Sarki Maraɗi Ɗanbaskore ya ajiye
sansanin ya ƙinsa a ƙarƙashita lokacin da
kawo yaƙi Gusau inda ya kwana goma sha huɗu bai sami nasara
ba ya tashi, sai kuma Kuka-Mai-Sheka wadda ta zama kamar rimi a tsakar gari. Duk
inda aka ɓullo wa Gusau sai an gan ta. Wato ta shanye sauran
itatuwa, waɗannan itatuwa da wasunsu akan yi masu camfin ajiye
iskoki, irin su Ɗantsatsumbe da jita-kukku da
sauransu.
3.6.2 HAƁAKAR GARIN GUSAU
Wasu daga ciki hanyoyin da matakai waɗanda su ka daɗa bunƙasa garin Gusau sun haɗa da Ganuwa da kofofin da lamurran ilimi da kasuwanci. Garin Gusau tun a zaliyan, wanda ya kafa shi Shehin malami ne, wanda ya na ɗaya daga cikin
manyan almajiran Shehu Ɗanfodiyo, wato malam Sambo Ɗan Ashafa. wanda ke maƙaftaka da garin Gusau sun daɗa haɓaka birnin Gusau ta
sanadiyar shigowarsu neman ilimi. Gusau, gari ne da Allah ya albarkata da
malamai na addinin musulunci, dalilin haka ne ya sa al'umma daga garuruwa
daban-daban kawo 'ya'yansu almajiranci.
Gusau, gari ne da
ake hada-hada ta kasuwanci musamman kayan amfanin gona da dabbobi, wannan ya daɗa jawo ra'ayin yan
kasuwa domin shigowa wannan gari saye da sayarwa, shigowar baƙi 'yan kasuwa ya ƙara haɓaka wannan gari na
Malam Sambo.
Da yake garin Gusau, gari
ne da yake da kasuwanci na saye da sayarwa da arziki, an samu wasu baƙi sun zo da nufin kasuwanci kuma suka share gari suka
zauna. Akwai ƙabilu da dama musamman daga Kudancin
Nijjeriya waɗanda suka zo Gusau suka samu wuri suka zauna kuma suka
hayayyafa a cikin garin. Wasu baƙi musamman Yarubawa
sun shigo a Gusau ta hanyar layin dogo
3.6.3 GANUWAR GARIN GUSAU
Samun ganuwa ga kowane irin gari alama ce ta samun kariya
ga mazauna wannan gari, domin takan ƙara jawo masa
bunkasa da haɓaka ta hanyoyi da yawa, Don haka yana da kyau mu faɗi irin matsayin da
ganuwar Gusau ta ɗauka zuwa lokacin da ta ruguje a sannu-sannu.
A lokaci zaman farko an shirya wa garin ganuwa ne ta
hanyar kewaye shi da shingen ƙaya. Wannan kuwa ya
auku ne tun zamanin malam Muhammadu Sambo ɗan ashafa har zuwa
farko da tsakiyar sarautar sarkin Katsina Abdulƙadir. (Gusau, B.M da Gusau S.M 2012).
A zamanin sarkin Katsina Abdulƙadir, lokacin sarautarsa Sarkin Musulmi Amadu Atiku ya yi
wa sarkin Katsinar a lokacin da ya je yi masa mubaya'a bayan naɗa shi sarkin
musulmi, alƙawarin ya sa a gine garin malam
Muhammadu sambo ɗan Ashafa da ganuwa, Don haka, ya umurci sarakunan
garuruwan da ke makwabtaka da Gusau da su taimaka wajen gine garin na Gusau da
ganuwa, Daga cikin sarakunan da suka turo mutanensu, akwai sarkin Fulanin Bunguɗu Muhammadu da
mutanen Kwatarkwashi, Kai har da na Rawayyada sauransu, duk sun zo sun taimaka ƙwarai wajen wannan aiki na gina ganuwa. Wannan shi ne
lokaci na farko da Gusau ta fara samun ganuwa ginanna da ƙasa wato yamɓu mai ƙwari tare da yi
mata ƙofofi (Gusau, B.M da Gusau S.M 2012).
Bayan haka a zamanin sarkin Katsinan Gusau Muhammadu
modibbo aka sake faɗaɗa ganuwar a sanadiyyar zuwan wasu mutane, shi wannan ƙari ya haɗa da unguwar da ake kira Rahaji wadda ta kunshi mutanen
abarma da janyau da wasu Rahazawa. A lokacin ne aka sami ƙofar Tahaji, Haka kuma an daɗa faɗaɗa ganuwar ta ɓangaren kudancin
garin yayin da Haza da abokinsa shantali da ɗan uwansa malam
Ummaru suka zo Gusau.
A zamanin sarkin katsinan Gusau Muhammadu Tuɓuri an samu ƙara bunkasa garin da saka shiyar Birnin Ruwa ta zama
cikin ganuwa, amma a lokacin sarkin Katsinan Gusau Muhammadu Giɗe ne aka haɗe Birnin Haza da
Birnin Ruwa suka zama shiyya ɗaya da sunan Birnin
Haza, Haɗewar ta auku ne aka haɗe Birnin Haza da
Birnin Ruwa suka zama shiyya ɗaya da sunan Birnin Haza, Haɗewar ta auku bayan
dawowar Haza Gusau, a sa'ilin da ya bar ta a zamanin Muhammadu Tuɓuri (Gusau, B.M da
Gusau S.M 2012).
Akwai wani rikicin iyaka da sarkin kiyawa na Kauran
Namoda Umaru ɗan Mamuda ya tayar a zamanin sarkin musulmi, Abdurrahaman
na ƙoƙarin ya ƙwace Dokau da Mareri a ƙarƙashin rikon Gusau,
ya nuna ya sami kyautar waɗannan garuruwa ne daga Sakkwato, sarkin kiyawa ya yi yunƙurin yaƙar Gusau har ya haɗo mayaƙa daga Birnin Gora ta ƙasar Maradun, amma sarkin musulmi ya hana shi, wannan
rikicin ya ci gaba har zamanin sarkin Katsinan Gusau, Muhammadu Murtala (1900-1916)
a lokacin da sarkin kiyawa ya turo sardaunansa wanda ya sauka a mareri, lokacin
da mutanen wurin suka ƙi bin umurnin sarkin kiyawa, sai ya
hana su noman gonakinsu a shekarar, Bayan da dattijan garin suka gaya wa sarkin
Katsinan Gusau, Muhammadu Murtala, halin da ake ciki, sai ya ba su wurare a
cikin Gusau, daga nan kuma ya rubuta wa sarkin musulmi takarda yana mai bayyana
masa halin da ake ciki, Daga bisani aka warware matsalar, garuruwan suka tabbata a ƙarƙashin Gusau. (Gusau,
B.M da Gusau S.M 2012).
Ganuwar garin Gusau ta sake samun bunƙasa da haɓaka a zamanin sarkin Katsinan Gusau Muhammadu Murtala a
shekarar (1900-1916) ƙarin ya auku ne ta wajen yamma maso
arewa wanda ya haɗa da maƙabarta da kuma
gandun sarki. Zuwa wancan lokacin ganuwar garin Gusau ta sami ƙofofi har huda tara (9) kamar haka:
-Kofar Kwatarkwashi
-Kofar Dogo
-Kofar Tubani
-Kofar Yamma
-Kofar Jange
-Kofar Matsattsa
-Kofar Rawayya
-Kofar Katsaura
-Kofar Goje
(Gusau, B.M da Gusau S.M 2012).
3.6.4 UNGUWANNIN GARIN GUSAU
Kamar yadda muka bayyana a baya, Birnin Gusau ya yi ta
samun bunƙasa da haɓaka da ƙare-ƙaren gunuwa saboda
zuwan wasu mutane baƙi, A sakamakon ƙaruwar Gusau an sami shiyoyi da unguwoyin da yawa fa suka
tsiru wato sababbi, unguwoyin sun haɗa:
BIRNIN HAZA
Kamar yadda aka faɗa baya, Haza wani sahhararren mutun
ne mai dukiya da bayi da dabbobi masu yawa. Haza ya zo Gusau ne tare da ɗan uwansa malam
Umaru da abokinsa shantali a zamani sarkin Katsinan Gusau Muhammadu modibbo
(1867-1876). A lokacin da Haza ya zo Gusau ne aka yi wani ƙarin ganuwa wanda ya kunshi birnin Haza. ita wannan
unguwa da Haza ya kafa, ita ake kira da sunansa, Har yanzu kuma zuriyar Haza
tana nan a Gusau (Gusau, B.M da Gusau S.M 2012).
SHIYAR RAHAJI
An kafa wannan unguwa ne a zamanin sarkin Katsinan Gusau,
Muhammadu modibbo (Nadama, 1972) A halin yanzu ba a kiran unguwar da wannan
suna, sai dai kofar jange kuma tana cikin rikon Galadima. (Gusau, B.M da Gusau
S.M 2012).
BIRNIN RUWA
An kira wannan wuri da suna birnin Ruwa ne saboda wuri ne
mai dausayi da ni'imar sanyi, wuri ne har ko da yaushe ba ya rabo da ruwa a
lokacin damina. A zamani sarkin Katsinan Gusau, Muhammadu Tuɓuri aka kafa ta, a
nan ne kuma aka yi wa mutanen da aka turo daga jos zuwa aikin kuza masauki,
lokacin kuma da aka fara aikin B.C.G.A. har wa yau, nan leburorin jinari suke
yi wa kansu ɗakuna bacci, Daga
nan, unguwar ta bunƙasa har a zamanin sarkin Katsinan
Gusau Muhammadu Giɗe ya haɗe ta da shiryar birnin Haza a matsayin riƙon hakimi ɗaya Unbandawaki Buharin Haza. (Gusau, B.M da Gusau S.M
2012).
'YARLOKO
Wannan unguwa ta tsiru ne a zamanin sarkin Katsinan
Gusau, Ummaru mala (1917-1929). Mutane
sun fara zama a wurin a shekarar 1929, lokacin da masu aiki tashar jirgin ƙasa suka kafa ɗakunan baccinsu a wurin. Daga cikin ma'aikatan jirgin ƙasan akwai ƙabilar Farlomi da sauran
wasu mutane, unguwar tana cikin Sabon Gari. (Gusau, B.M da Gusau S.M 2012).
SABON GARI
Wannan unguwa wani mutumin Saraliyon ne wanda ake ce wa
Morgan ya fara zama a cikinta, kuma ya riƙa mai unguwarta,
kafin ta sami hakimi, a lokacin sarkin katsinan Gusau, Muhammadu mai'akwai
(1929-1943). Morgan shi ne ya fara karɓar haraji a wurin, daga baya, ta
sami magaji Muhammadu Taula wanda aka ɗauko daga mada ya zama hakiminta na
farko, Da tafiya ta miƙa aka sami ƙabilu daban-daban
suka zauna a wannan unguwa ta sabon gari. Daga cikinsu akwai igbo da yorobawa
da wasu Hausawa da sauransu. (Gusau, B.M da Gusau S.M 2012).
FILIN GUNZA
An kafa unguwar filin Gunza a zamanin sarkin katsinan Gusau, Muhammadu mai'akwai, mafarin
wannan suna kuwa, Gunza ne zaune wurin yana sayar da goro da sauran kayayyaki,
amma shi Gunza mutumin Rawayya ne wanda aka taso da kakaninsa daga Rawayya wato
lokacin da mutanen Gusau suka taso daga Rawayya, suka zo Gusau a zama na biyu,
tana ƙarƙashin rikon mayana.
(Gusau, B.M da Gusau S.M 2012).
SABON FEGI
A zamanin sarkin katsina Gusau, Muhammadu mai'akwai aka
yayyanka gonaki aka ba mutane fegi-fegi don su samu wurin zama. su Hassan
mairangwaɗa Basakkwace da Mamman Audu Bazazzagi, mai ɗinkin tela, su ne
suka fara zama wurin da kuma Halilu Emos Bakatsine da sauransu, Ana kiran
unguwar da wannan suna saboda fegogi ne sababbi aka rarraba wa jama'a, Tana ƙarƙashi rikon
Galadima. (Gusau, B.M da Gusau S.M 2012).
TASHAR MOTA
Mutanen da suka kafa wannan unguwa a zamanin sarkin kudun
Gusau, Alhaji Sulaiman, waɗanda suka fara zama a cikinta su ne maikatoɓara da Ibrahim Ɗannukko da Adamu Gummi da sauransu. inda aka yi
Randabawul na Bello bara'u yanzu, nan ne
mota ta fara tsayawa a Gusau, amma unguwar da zaman mutane ba ta kafu ba, sai
zamanin sarkin kudun Gusau Alhaji Sulaiman, Tana ƙarƙashin riƙon Galadima. (Gusau, B.M da Gusau S.M 2012).
FILIN TANKO
Tanko wani mutum ne mai teburi, yana sayar da itace da
goro, iyayensa daga garin kwatarkwashi suka zo, suka haife shi a nan Gusau,
saboda shaharar da ya yi a nan unguwar, sai aka riƙa kiran ta da sunansa. An tsiri wannan fili ne a lokacin
sarkin kudun Gusau, Alhaji Sulaiman, yanzu haka gabacin unguwar na aikin rikon
Sabon Gari ne, yamma kuwa na cikin riƙon mayana. (Gusau,
B.M da Gusau S.M 2012).
UNGUWAR TOKA
Ita wannan unguwa wata Bagobira ce ta fara zama a
cikinta, a zamanin sarkin kudun Gusau, Alhaji Sulaimanu. Da ma can wannan wuri ne da aka fi zubar da
shara da tokar dafuwar abinci. Don haka ne
da mutane suka zauna a wurin, suka dinga kiran ta da sunan Unguwar Toka,
unguwar tana cikin riƙon magajin sabon gari. (Gusau, B.M
da Gusau S.M 2012).
UNGUWAR MANGWARO
A lokacin da aka kafa wannan unguwa cike take da itacen
mangwaro, don haka, ta sami wannan suna. Malam Mammam wurno da Ɗanmunci mai sayar da magungunna da wasu gandirobobin
Gidan yari su ne suka fara zama wurin, An kafa wannan unguwa a zamanin sarkin
kudun Gusau Alhaji Sulaimanu, yanzu tana ƙarƙashin riƙon mayana. (Gusau,
B.M da Gusau S.M 2012).
SHIYYAR TUDUN WADA
Lokacin da aka yi ƙarin kasuwa da
asibiti aka tayar da mutanen da ke wurin wato Unguwar Ka-Fama-ni aka mayar da
su Tudun Wada a (1958) Da mutane suka koma wurin sai suka yalwata, suka wadata,
sai suka riƙa kiran ta da sunan Tudun Wada, wurin
da yake shimfiɗɗiyar ƙasa kan tudu,
unguwar Tudun Wada ta kafu ne a zamanin Sarkin Kudun Gusau, Alhaji Sulaimanu, aka
kuma haɗe ta da Unguwar
Mareri da Damɓa. (Gusau, B.M da Gusau S.M 2012).
3.6.5 NAƊEWA
Alhamdulilah, a nan muka kammala wanann babi, babin da ke ɗauke da ma'anar
zamani, da kuma ma'anar sana'a, da nau'o'in sana'o'in a garin Gusau, da ma'anar
kalmar Gusau, da kafuwar Gusau, da haɓakar Gusau, da ganuwar garin Gusau,
da ƙarshe aka kammala wannan babi da unguwanin garin Gusau.
BABU NA HUƊU
TASIRIN ZAMANI GA
SANA’AR ƘIRA A GARIN GUSAU
4.0 SHIMFIƊA
Wannan babi ya ƙunshi bayani a kan
tasirin zamani ga sana’ar ƙira a garin Gusau da kafuwar maƙeran farko a garin Gusau da hanyoyin samar da kayan
sarrafawa da kayan aikin ƙira abubuwan da ake
ƙerawa da muhimmancin ƙira ga al’ummar Gusau da bunƙasar maƙera da sauyawar
zamni a Gusau da tasirin zamani a kan kayan sarrafawa sai zamani da abubuwan
sarrafawa da sauye-sauyen zamani a kan kayan da ake ƙerawa
4.1 ƘIRA A
GARIN GUSAU KAFIN ZUWAN TURAWA
Garin Gusau, gari ne mai albarka da ɗinbin tarihi wanda
ake aiwatar da sana'ar ƙira tun kafin zuwan Turawa 'yan kama
wuri zauna a ƙasar Hausa. Sana'ar ƙira sana'a ce da ake sarrafa tama da ƙarafa, zinariya ko azurfa da sauran nau'o'in ƙarfe domin mayar da su abin amfani na yau da kullun. Ana
kiran mai sana'ar ƙira da maƙeri haka kuma ana ƙiran farfajiyar da
ake ƙira suna da maƙera.
Sana'ar ƙira a garin Gusau
ta kasu kashi biyu. Akwai maƙeran babbaƙu da kuma maƙeran farfaru. Wasu kuma sukance sana'ar baƙi da kuma fari.
Maƙeran babbaƙu: su ne maƙeran asali, da suke
sarrafa tama domin samar da ƙarfe ko ƙarafa. Haka kuma su ne maƙeran da suke amfani da baƙin ƙarfe domin samar da
abubuwa daban-daban domin tallafawa rayuwar al'umma ta yau da kullum. Kayan da
suke ƙerawa sun haɗa da lauje, kibiya, gatari, wuƙa, fartanya, galma, murhu, tukunya, shebur, kura ta janyo
guga da sauransu.
Maƙeran farfaru: Maƙeran farfaru kuwa, su ne maƙera na farin ƙarfe da suke amfani
da goran ruwa ko farin ƙarfe domin samar da wasu ƙananan abubuwa amma masu matuƙar muhimmanci ga rayuwar al'umma. Ire-iren abubuwan da
suke samarwa sun haɗa da: ludayin sha da ludayin miya da zobba da kuyafa da
sauran kayayyakin adon mata kamar ɗankunne, awarwaro, kwankwaɗo da sauransu. Waɗannan sune nau'o'in maƙera a garin Gusau.
4.2 KAFUWAR MAƘERAN FARKO A GARIN GUSAU
Kamar yadda tarihi ya nuna, ƙira ta shigo garin Gusau ne a sanadiyar yaƙi. Haka kuma wanda ya fara sana'ar ƙira a garin Gusau shi ne JIBO Ɗanmama da ƙanensa Baƙo. Jibo Ɗanmama ya zauna ne
a Tabkin Kuraki watau Unguwar da ake kira da Bakin Silma ko kuma Ƙofar Yarima a yanzu. A wannan unguwar Jibo Ɗanmama ya ci gaba da aiwatar da sana'arsa ta ƙira, amma kuma bayan bayyanar Jibo da ƙanensa Baƙo a matsayin maƙera na farko a
wannan garin na Gusau. Sai kuma Allah ya tada wasu gidaje guda uku da suma suka
kama wannan sana'ar ta ƙira, gidajen kuwa sune kamar haka:-
1. Gidan Mande Gyasa wanda ya ke a Unguwar Dogon Dabino
2. Gidan malam Barau, shi kuma a shiyar Mayana
3. Gidan Walico shi kuma a Ƙofar Jange. (Gusau, B.M da Gusau S.M 2012).
Waɗannan su ne gidaje na farko da suka fara aiwatar da
sana'ar ƙira a garin Gusau. Bayan waɗancan gidaje kuma
an samu ƙarin wasu gidaje daga baya, da suma
suka kama wannan sana'a ta ƙira gadan-gadan
kamar haka:-
1. Gidan Mani ƊanBiba
2. Gidan Sani Ɗangata
3. Gidan Yahaya Dundu da sauransu.
(Gusau, B.M da Gusau S.M 2012).
A haka dai sana'ar ƙira ta samu kafuwa
da gindinta a wannan garin na Gusau. yanzu haka ‘ya’yan waɗannan mutane da
jikokinsu su ne suka mai da ta abar gado wanda sanadiyar riƙonta hannu biyu-biyu da suka yi ya daɗa bunƙasarta matuƙa a wannan
gari.
4.3 HANYOYIN SAMAR DA KAYAN
SARRAFAWA
Kira ita ce tsantsar kimiyya da fasaha irin ta Bahaushe.
Domin sana’a ce da ake tafiya mai nisa domin samo sinadarin yin ta (tama). Daga
nan, za a zo ayi ta bai wa tamar nan wuta da zugazugi har sai ta nade, kuma,
kumfa ta rufe ta. Daga nan za a bambare
kumfar, a sami tsurar karfen.
Wannan karfe shi ne za a guggutsira shi da kurfi, sannan
a bashi wuta, a sa hantsaki ko awartaki a ɗauko shi. A ɗora kan uwar maƙera, a doddoke shi, sannan a lauya shi irin yadda ake so
domin samar da ire-iren abubuwan da ake samarwa ta hanyar wannan sana’a domin
tallafawa rayuwar al’umma ta yau da kullum.
Haka kuma, ƙira sana’a ce da
take haifar da gudanar da wasu sana’o’i na zamantakewar Bahaushe ta yau da
kullum. Daga cikin irei-ren kayayyakin da maƙera suke kerawa domin tallafawa rayuwar al’umma sun haɗa da:
KAYAN
YAƘI:- Gabanin zuwan Turawa ƙasar Hausa, tarihi ya nuna cewa Hausawa da sauran ƙabilu na wannan shiyya suna zaune ne zama na ɗar-ɗar ko kuma mu ce
zama irin na doya da manja. Domin akan samu yaƙe-yaƙe a tsakanin ƙabilu daban- daban ko tsakanin wannan gari da wancan gari
domin mamaya da ƙara girman ƙasa ko kuma domin samun bayi. Ire-iren wannan yaƙe-yaƙe ana gudanar da su
ne da wasu makamai na musamman waɗanda akasarin su maƙera ne suke ƙera su. Makaman da ake samarwa sun haɗa da:- sulke da
mashi da adda da wuƙa da tsitaka da gatari da takobi da
sauran kayayyakin dawakan da ake yaƙi a kansu. Kamar
irin su linzami da likkafa da garkuwa (karafuna ne da aka rufe fuskar doki da su).
(Gusau, B.M da Gusau S.M 2012).
Hotunan Kayan Yaƙi
Hoton Takobi da Mashi da Bindiga
Sana’ar ƙira tana tallafa wa
rayuwar Bahaushe domin samar da kayayyakin gudanar da yaƙe-yaƙensu na wancan zamani.
Duk da cewar yanzu an daina ire-iren waɗannan yaƙe-yaƙe har yanzu Hausawa
na cin moriyar sana’ar kira domin samar da wasu nau’o’i na makamai kamar irin
su barandami da lauje da bisalami da fate-faten takobi da sauran duk makami mai
tasarifi da karfe.
Kayayyakin Gudanar Da Wasu Sana’o’i: Bayan samar da
kayayyakin yaƙi da kayayyakin gudanar da wasu
mashahuran sana’o’in Hausawa na gargajiya, kamar irin su noma da su da wanzanci
da farauta da fawa da malanta da jima dasassaka da sauransu. Idan muka ɗauki noma zamu ga
cewa akasarin kayayyakin gudanar da sana’ar ta noma tun daga gyaran amfanin
gona har zuwa yankan amfanin gonar, duk Maƙera ne suke ƙera su kamar su
magirbi da garma da kalmi da fatanya da dundurusu da lauje da wuƙa da sauransu.
Haka ma Idan aka ɗauki su (kamun kifi) ƙugiya da sauran duk nau’in ƙarfe da ake amfani da shi wajen kamun kifi da yankawa, hatta sarrafashi ko dai banda ko gashi ko suya ko makamancin hakan sai an yi amfani da kayayyakin da maƙera suka ƙera.
Haka abin yake ga sauran sana’o’in Hausawa na gargajiya
kamar irin su wanzanci da farauta da malanta da fawa. Duk askar da wanzami yake
amfani da ita wajen gudanar da sana’ar sa ta wanzanci, za a tarar cewa maƙera ne suka ƙera ta. Haka abun
yake ga mafarauta duk maƙamin da mafarauci yake
amfani da shi wajen gudanar da sana’arsa ta farauta za a tarar maƙera ne suka yi su. Misali, takobi da wuƙa da adda da barandami da tsitaka da Sauransu.
Idan aka ɗauki sana’ar jima, suna amfani da wuƙa da kartagi wajen aiwatar da sana’ar su, waɗanda duk maƙera ne suke ƙera su. Haka abun
yake ga masu sana’ar fawa, wuƙaƙen da jantaɗin da suke amfani da su duk maƙera ne suka yi su. Haka abin yake ga masu sana’ar sassaƙa, duk nau’in kayayyakinsu akwai hannun Maƙera a ciki, kamar su gizago da tsirya (karama ko babba)
da gatari da mahuri da sauransu. Hatta malamai suna gudanar da sana’arsu da
kayan ƙira, domin tauwadar da suke amfani da ita ana yin ta ne
da kwan maƙera (tokar karfen kira), Domin samar
da tauwada ta rubutu don ya yi rangadau.
Saboda haka, ƙira gaskiya ne ta
fi noman raggo kai! Har ma wanda ba raggo ba. Domin tana taimakawa wajen samar
da kayayyakin gudanar da wasu sana’o’i na gargajiya domin samun abin masarufi
daya jibinci ci da sha da sutura da muhalli.
MUHALLI:- Muhalli dai, shi ne wata ‘yar farfajiya da mutum zai
mallaka domin samun makwancinsa da na iyalansa. Bisa al’ada, a da can tarihi ya
nuna cewa Hausawa suna zama ne a cikin kogon dutse. Wani kaulin kuma cewa yayi,
su suke rarake dutsen su shiga ciki domin maganin ruwa da rana da abokan gaba.
Da tafiya ta yi tafiya, suka fara yin amfani da itatuwa da karare da shifci da
sauran nau’o’in itatuwa da ganyaye domin samar da muhalli.
Haka kuma, lokaci ya zo da Hausawan suke samun dandankuwa
da babarkiya ko ɓurji domin yin tubalan da za su gina muhallinsu. Wannan
ya haifar da sanya abubuwa kamar su kofa da taga, waɗanda duk maƙera ne suke ƙera su. Hatta
abubuwa kamar su alharga da danta duk maƙera ne ke yin su.
Saboda haka, a nan ƙira na tallafa wa
rayuwar Bahaushe dangane da abin da ya shafi muhalli, domin Maƙera ne suke samar da ƙofofi da tagogi da sauran nau’o’in mukullai domin su zama
kariya ga muhallin Hausawa. Haka kuma abubuwa kamar su kwankwado domin tare
gashin ka na mata da ɗanɓaro abin kadawa da baki domin samar da amo mai armashi
duk maƙera ne suke samar da su.
4.3 KAYAN AIKIN ƘIRA
Kamar yadda aka sani cewa, kowace sana'a na da nata kayan
aiki. Haka ita ma sana'ar ƙira na da kayan
aiki. Kuma ana sarrafa ƙarfe zuwa nau'o'in daban-daban, don
haka, zamu ɗauko kayan aikin ƙira ɗaya bayan ɗaya mu yi bayaninsu
kamar haka:
1. MASKO:- ƙarfe ne mai ɗan tsawo kimanin kamu ɗaya, yana da faɗin kai. Zubinsa iri
ɗaya ne da masaba,
amma shi yana da faɗin kai, kuma mariƙinsa alailaye yake,
shi ma ana dukan ƙarfe ne yadda ake son a yi da shi, ya'Allah mai faɗi ko mai tsawo ko
gajere.
2. HANTSAKI/AWARTAKI:-karfe
ne mai kama da almakashi, wato ƙarfe ne da aka ginɗaya shi da wani ƙarfe a ƙulle shi a tsakiya,
bakinsa yana buɗewa ya kuma rufe, Da shi ne ake riƙe ƙarfe da aka ɗauko daga wuta
domin sarrafawa, yana taimakawa maƙera wajen ɗauko ƙarfe a cikin wuta ba tare da sun sa hannuwansu ba ko wani
abu.
3.
KURFI:- ƙarfe ne gajere, kutukurkuri mai faɗin kai da faɗin baki. Ana amfani
da shi ne domin datse ƙarfe kuma gutsuntsura shi, haka kuma
ana amfani da shi ne ana datsa ƙarfe da shi duk
yadda ake so, dogo ko gajere da sauransu.
4.
MADOSHI:- Ana amfani da shi ne
wajen huda ƙota, juma madoshi iri biyu ne, akwai
babba kuma akwai ƙarami, karfe ne milmulalle amma kuma
siriri, yanada ƙotar itace, kuma da shi ne ake huda ƙofofi kamar nasu fartanya da magirbi da sauransu, haka
kuma yana taimakawa wajen huda ƙarfe yadda ake so
ba tare da ansha wuya ba.
5.
MAGAGARI:- shi kuma, ƙarfe ne mai ɗan tsawo da faɗi, haka kuma yana da ƙurzunu-ƙurzunu a jikinsa,
da shi ne ake wasa ko koɗa ƙarfen da aka ƙera ko a sararrafa shi. Misali: wuka, takobi, lauje da
sauransu. Haka kuma shi ne yake saka ƙarfe ya yi haske, wato ya yi ƙyalli.
5.
KALAMBA:- karfe ne kantararre da
mariƙai guda biyu, wato dama da hagu yana da kaifin gaske, da shi
ne ake datse karfe idan ya yi tsatsa ko kuma ya yi baƙi domin a sabunta shi ko kuma domin ya yi fari ko haske.
A nan shi ne yana mai da tsohon ƙarfe sabo wato ya
sabunta shi ya tashi daga dattin da ya yi ya koma sabo.
6.
GIZAGO:- ƙarfe ne mai kaifi
da ake maƙala shi a wata kantararriyar kota,
maƙera na amfani da shi ne wajen sarrafa ƙotoci, amfanin shi ya sarrafa ƙota zuwa fannin da ake so.
7.
ZIGA-ZIGI:- wato wani abu ne na
fatakamar jaka, ana sanya masa wani bututun ƙarfe ne, kuma yana da hannaye guda biyu, da shi ne ake
rura wutar yin ƙira. Ana haɗe hannayen sa a buɗe su domin kwarfar
iska, iskar ta rinƙa fita bututun da ke sanye da jikin
tubalin bakin wutar domin rura wuta ba sai maƙeri ya yi wahalar fifitata damafeci ko wani abu da za ya
bada iska ba, idan aka yi amfani da ziga-zigi to ya isar.
8. TURU
NA MAƘERA:- wannan ba wani abu ba ne, illa ɗan wani kwari ne da
ake hura wutar maƙera a ciki, wato a nan ne ake zuba
gawayi, a kuma zuro tubalin bakin wuta, gindin wannan turu na maƙera ne domin rura wuta.
Haka kuma, shi wannan turu aikin shi ne idan aka zuba garwashi a cikin
to idan a lokacin iska ne ko da iska ya buga to yana ƙarewa domin ka da garwashin ya yi baltsi domin yana iya
haddasa gobara idan ba a yi hattara ba.
9.
TUBALIN MAƘERA/TUBALIN
BAKIN WUTA:- wannan ba wani abu ba
ne, illa ƙasa ce da ake kwaɓawa ta bushe,
sannan a yi mata babban baki da kuma mofa a zururu ta nan ake sako bakin
ziga-zigi domin hura ko rura wutar maƙeri, haka kuma yana
hana iska idan ya buga wuta ta yi baltsi.
10.
ICCEN BAKIN TUBALI:- Itace
ne na kuka da ake fera shi a kuma daidaita shi domin ya zauna a bakin tubalin
bakin wuta, ta nan ne iskan zuga-zigi take biyowa zuwa kwarin maƙera domin rurar wutar yin ƙirar, haka kuma itacen muka sunfi ƙwarin tare wutar da ake ƙira da ita.
11.
RUWA:- Maƙeri na amfani da ruwa kusa da shi ne domin tsoma masari
ko matsoni in ana aikin wuta domin ka da ta lalace ko ya naɗe ko ya kare,
amfanin ruwa ga maƙeri shi ne ya taimaka ma shi kada
abun da yake aiki da shi ya samu matsala.
12.
KUJERA:- Maƙeri na amfani da kujera domin ya zauna don ya yi aikin da
zai yi, haka kuma kujera na taimakawa maƙera domin su samu
wurin zukunno (wato wurin da za su zauna da mazauninsu domin aiki ya yi masu
sauƙi).
Waɗannan abubuwa da muka zayyana su a baya, su ne kayayyakin
da ake amfani da su domin gudanar da sana'ar ƙira, ita dai wannan sana'a ta ƙira sana'a ce ta maza akasari. Haka kuma mata na yinta,
amma ba su yi wata shahara ba a kanta. Domin a ƙasari da zarar mace ta kai wani munzali na shekara, ta
kan zauna ne a gida har lokacin gabatar da ita ya yi sannan a kaita gidan
mijinta. Da wannan dalili ne ya sa maza suka fi yin sana'ar ƙira domin kuwa mata a gida aka san su domin gudanar da
hidimar iyali.
4.4 ABUBUWAN DA AKE ƘERAWA
Ƙira dai kamar yadda muka sani, sana'a ce da ta jiɓinci sarrafa tama
zuwa ƙarfe daga nan kuma a samar da abubuwan tallafa wa rayuwar
bil'adama, musamman Bahaushe. Haka kuma, sana'a ce da take haifar da wasu
sana'o'i na zamantakewar Bahaushe ta yau da kullum. Daga cikin ire-iren kayayyaki da maƙera suke ƙerawa domin tallafawa rayuwar Bahaushe sun haɗa da:
1.
KAYAN YAƘI:- Gabanin zuwan Turawa ƙasar Hausa, tarihi ya nuna cewa Hausawa da sauran ƙabilu na wannan yanki suna zaune ne zama na ɗar-ɗar ko kuma mu ce
zama irin na doya da manja, domin a kan samu yaƙe-yaƙe a tsakanin wannan
gari da wancan gari domin mamaya da ƙara girman ƙasa ko kuma domin samun bayi, ire-iren wannan yaƙe-yaƙe ana gudanar dasu
ne da wasu maka-mai na musamman waɗanda akasarin su maƙera ne suke ƙera su, makaman sun haɗar da:
Suke da mashi da adda da wuka datsitaka da gatari da
takobi da sauran kayayyakin dawakan da ake yaƙi a kansu. kamar irin su linzami da likkafa da garkuwa
(karafuna ne da aka rufe fuskar doki dasu).
saboda za muga cewa ƙira tana tallafawa
rayuwar Bahaushe domin samar da kayayyakin gudanar da yaƙe-yaƙensu na wancan
zamani, Duk da cewa yanzu an daina
ire-iren waɗannan yaƙe-yaƙe amma har yanzu Hausawa na cin moriyar sana'ar ƙira domin samar da wasu nau'o'in na makamai kamar irin su
barandami da lauje da bisalami da fate-fate da takobi da sauran duk wani makami
mai tasarifi da ƙarfe.
Hotunan Kayan Yaƙi da Maƙera ke ƙerawa a wannan zamani
2. KAYAYYAKIN GUDANAR DA WASU SANA'O'I:-
Bayan samar da kayayyakin yaƙe-yaƙe da kayayyaki
gudanar da wasu mashahuran sana'o'in Hausawa na gargajiya, kamar su noma da
wanzanci da farauta da fawa da malanta da jima da sassaƙa da sauransu.
Idan muka ɗauki noma zamuga cewa akasarin kayayyakin gudanar da sana'ar
ta noma tun daga gyaran amfanin gona har zuwa yankan amfanin gonar, duk maƙera ne suke ƙera su, kamar
magirbi da garma da kalmi da fartanya da dundurusu da lauje da wuka da
sauransu.
Haka kuma idan aka
ɗauki masu (kamun
kifi) kugiya da sauran duk nau'in ƙarfe da ake amfani
da shi a wajen kamun kifi da yankawa, hatta sarrafashi ko gashi ko suya da dai
makamancin haka sai anyi amfani da kayayyakin da maƙera suka ƙera ne. Haka abin
ya ke ga sauran sana'o'in Hausawa na gargajiya kamar wanzanci da farauta da
malanta da fawa, da askar da wanzami yake gudanar da sana'ar sa ta wanzanci. Za
a tarar cewa maƙera ne suka ƙerata. Haka abin yake ga mafarauta duk makamin da
mafarauci yake amfani sa shi wajen gudanar da sana'arsa ta farauta za a tarar
maƙera ne suke yin sa. Misali, takobi da wuƙa da adda da barandami da tsitaka da sauransu.
Idan aka ɗauki sana'ar jima kuwa, zamuga suna amfani da wuka da
kartagi wajen aiwatar da sana'ar su, waɗanda duk maƙera ne suke ƙerasu. Haka abin
yake ga masu sana'ar fawa, wuƙaƙen da jantaɗin da suke amfani da su duk maƙera ne suke yin su. Haka abin yake ga masu sana'ar sassaƙa, duk nau'in kayayyakinsu akwai hannun maƙera a ciki, kamar su gizago da tsirya (ƙarama ko babba) da gatari da mahuri da sauransu. A
malanta kuwa, malamai suna gudanar da sana'ar su da kayan ƙira, domin tauwadar da suke amfani da ita ana yin ta ne
da kwan maƙera (tokar ƙarfen ƙira), Domin samar
da tauwada ta rubutu don ya yi ran-gaɗaɗau.
Saboda haka, ƙira gaskiya ne tafi
noman raggo kai! har ma wanda ba raggo ba, domin tana taimakawa wajen samar da
kayayyakin gudanar da wasu sana'o'i na gargajiya domin samun abin masarufi da
jiɓinci ci da sha da sutura da muhalli.
4.5 DANGANTAKAR MAƘERA DA AL'UMMA
Hausawa na cewa "Zama lafiya ya fi zama ɗan sarki" Abu
ne a bayyane maƙera mutane ne da suke zaune da
jama'a zama na salama, da iya mu'amula cikin mutuntawa da kowa. Sanin kowa ne
maƙera mutane ne da suke aiwatar da sana'ar su a waje ɗaya. Haka kuma
sukan karɓi baƙuncin jama'a
daban-daban a kullun safe ta Allah domin saye da sayarwa. Wannan gangantakar ta
cinikayya tsakanin maƙera da al'umma. Dangantaka ce ta
gaskiya da riƙon amana da kuma fahimtar juna. Irin
wannan dangantakar ce har ta haifar da wasanni tsakanin maƙera da al'umma. misali, wasa tsakanin Buzaye da wanzamai
da kuma sharifai.
1. WASA TSAKANIN BUZAYE DA MAƘERA
Wannan wani nau'i ne na wasar barkwanci da yake gudana
tsakanin waɗannan jama'a. Asalin wasan ya samu ne ta inda maƙera suke ikirari da cewa sune iyayen ɗakin Buzaye domin
sun ce, sune suka kafa gari, bayan sun kafa sai Buzaye su zo su raɓu da su domin samun
abin masarufi. Haka kuma mutane ne masu ta'ammali da nau'o'in abubuwa da maƙera suke samarwa kamar takobi da azurfa da sauransu.
Wannan shi ne ya haifar da wasa tsakaninsu.
Haka kuma, maƙera suna cewa sune
suke baiwa Buzaye maganin wuta, wanda shi kuma buzu ya ke cewa shi sharifi ne,
ya kuma riƙa wasa da wuta ana bashi kuɗi, Daga bisani maƙera sai su karya asirin maganin wutar da suke baiwa
Buzaye, saboda haka, idan buzu ya je yi wasa da wuta sai ya ƙone, sai ya zu ya bawa maƙera hakuri da 'yan kuɗi sannan kuma ya
yarda cewa shi yaron ko bawan maƙera ne, sannan maƙerin zai sake bashi wani magani, wannan shi ne irin wasan
da yake gudana a tsakanin maƙera da Buzaye a
Bahaushiyar al'ada.
2. WASA TSAKANIN MAƘERA DA WANZAMAI
Kasancewar sana'ar wanzanci sana'a ce da ta jiɓinci tuje gashi da
gyaran fuska da sauransu, waɗannan ayuka ba sa
gudana sai da aska da koshiya da matsagi da sauransu. Haka akwai ire-iren wasa
na barkwanci da kuma nuna tsatsuba tsakanin maƙera da wanzamai, maƙera kan ce:
"idan ba don su ba da wanzamai ba za su ci abinci ba". sai su kuma wanzamai su ce ba haka zancen
yake ba, nan da nan za a ga wanzami ya tugo zangarniyar dawa ko gero ko kuma ya
ɓalli reshen wata
itaciya ya yi irin nasa tsatsibar ya kuma yi aski da shi, wannan shi ne irin
wasan da yake wanzuwa tsakanin jinsin al'ummar guda biyu.
3. WASA TSAKANIN MAƘERA DA SHARIFAI
Bahaushe ya yarda cewa duk mutumin da aka kira da suna
sharifi, to mutum ne babba mai daraja, wanda kuma jika ne ga Annabin Muhammadu (S.A.W.). Haka kuma, Bahaushe ya haƙiƙance cewa wuta bata cin sharifai
domin tsatson da suka fito ya rabauta daga ƙunar wuta. ga
sudai ba sharifai ba ne, wannan shi ya haifar da wasa tsakanin sharifai da maƙera, tun da kowa yana tinƙaho da wasa da wuta.
4.6 MUHIMMANCIN ƘIRA GA AL'UMMA A YAU
Muhimmancin ƙira ga al'umma a
bayyane ya ke, domin kuwa dukkan wata sana'a a doron duniyar nan galibin
aikace-aikacen su bashi yiyuwa sai da taimakonta. Amfaninta kuwa baya lissafuwa sai dai mufaɗi abin da ya sauwaƙa daga ciki, kayan noma dana faw da sassaƙa da wanzamai da sauransu, dayawa daga ciki waɗannan
aikace-aikacen su basu yiyuwa sai da maƙeri ya sa hannunsa
sa'annan suke yiyuwa. A taƙaice dai rayuwar ɗan adam ba zata yiyuba ba maƙera ba, domin kuwa sune suke yin kayan faɗa na abokan gaban
cikin gida wato yunwa. haka kuma sune suke yin kayan faɗa na abokan waje
wato maƙiya. Da yunwa da maƙiya kuwa ba za su bar ɗan adam ya rayu ƙalau ba.
4.7
TASIRIN ZAMANI A SANA'AR ƘIRA A
GUSAU
Babu ko shakka zamani ya taka muhimmaiyar rawa a kan
sana'ar ƙira a garin Gusau. Domin kuwa zamani
ya zo mata da ababe sabbi waɗanda suka ƙara haɓaka wannan sana'a a
wannan lokaci da muke ciki. Kamar yadda bayani ya gabata cewa ƙira ita ce sana'a ta tsantsar hikima da fikira da basira
da fasaha irin ta Bahaushe domin samar da duk nau'o'in abubuwan tallafawa
rayuwa ta yau da kullun da ke tasarifi da ƙarfen kimiyya da ƙere-ƙere irin na zamani, ya yi matuƙar tasiri mai a fani a kan wannan sana'a, domin kawo sauƙi wajen aiwatar da ita wannan sana'a. Ire-iren tasirin da kimiyya da ƙere-ƙeren zamani ke da
shi kan sana'ar ƙira sun haɗar da:
SAMAR
DA GYARARREN ƘARFE:- Bisa ga al'ada ta maƙera, sukan yi tafiya mai nisan gaske kafin su haƙo tamar da za su sarrafa, ta zama ƙarfe domin gudanar da sana'arsu. Amma a yanzu saboda
mikiyya da ƙere-ƙere irin na zamani. Maƙera a garin Gusau ba sai sun je garuruwa masu nisa da
Gusau ba sannan su samo tama ko ƙarfe ba. a yanzu
haka zamani ya kawo ƙarafa daban-daban daga matattun
motoci wuza tsofaffin injinan mota cikin sauƙin kuɗi da kuma ba sai an sha wahalar haƙo tama ba.
Haka kuma, maƙera kan sha wahalar
gaske wajen gutsuttsura ƙarafa da daddatsa
su, amma yanzu haka kimiyya irin ta zamani ta zo da wata irin na'ura mai fitar
da iskar gas wai ita (carbide) da ake amfani da ita wajen daddats ƙarfe cikin kankanin lokaci da kuma sauƙi. A nan kimiyya da ƙere-ƙere irin na zamani
ya yi tasiri a kan sana'ar ƙira a wannan gari
na Gusau, domin akasarin maƙera a nan Gusau sun
koma amfani da irin wannan na'urar domin sauƙaƙawa kansu wajen gudanar da sana'ar
su ta ƙira.
Bugu da ƙari kuma, a da maƙera a wannan gari
na Gusau basa amfani da ajiyayyen ma'auni wajen auna tsawon ko faɗin kayyakin da suke
samarwa, amma a yanzu haka kimiyya irin ta zamani ta zo da wasu abubuwa da ake
amfani da su wajen auna tsawon abin da ake son a ƙera. Misali (Ruler da tape) maƙera na amfani da su yanzu musamman a wajen auna tsawo da
faɗi na ƙofa ko taga da
sauran kayayyakin da suke ƙerawa.
Haka kuma, sauran na'o'in ƙarafuna da a da. maƙeranmu basa amfani
dasu, amma a yanzu, sakamakon ɓullowar kimiyya da ƙere-ƙeren na zamani ya samar wa maƙera irin waɗannan ƙarafa, Misal
(bronze da alminium), wato farin ƙarfe da goran-ruwa
duk yanzu maƙera na amfani da su wamen sarrafawa
da samar da ingantattun abubuwan domin tallafawa rayuwar Bahaushe irin ta yau
da kullum.
Haka kuma yanzu haka, maƙera a nan Gusau kan kwaikwayo wasu sassa na ɓangaren wasu
na'urar casar gyaɗa da maƙeranmu kanyi
kwaikwayon irin wannan rariya ta na'urar casar gyaɗa da sauran sassa
na garmar shanu. Misali fika-fikai da baki da kuma ƙundu na galmar shanun kanta. Haka kuma, a yanzu maƙera na yin abubuwa daban-daban kamar irin su kwangirin
zuba abincin dabbobi da tsuntsaye waɗanda suka kwaikwayo daga Turawa.
Haka ma walda. hanya ce ta sarrafa ƙarafa da zamani ya zo da shi, duk da cewa masu walda a
nan Gusau ba ainihin maƙeran asali ba ne, itama dai walda
tayi matuƙar tasiri a kan sana'ar ƙira a nan Gusau. Haka kuma tasirin zamani bai tsaya a nan
ba, domin kuwa ya ƙara samarwa masu sana'ar ƙira a nan Gusau. Wasu hanyoyi don sauƙaƙa aiwatar da wannan sana'a. Misali,
za mu ga cewa samar da ƙarfen kangarwa wanda ake wasu 'yan
dabaru domin ya riƙa bada iska, ya rage masu wahala
wajen amfani da ziga-zigi.
Haka kuma tasirin zamani ya samarwa da maƙera wani kalar gawayi wanda baya saurin mutuwa ko zama
toka, irin wannan gawayi ana kiransa da suna (magic coal). Sannan kuma a wasu
wuraren suna amfani da batira su jona su da abin yuyawa me dauke da 'yar fanka
(motar domin ya ba da iska ciki sauƙi.
4.7.1 BUNƘASAR MAƘERA DA
SAUYAWAR ZAMANI A GUSAU
Babu shakka sauyawar zamani da kimiyyar ƙere-ƙere a wannan
duniyar da muke ciki ya taka muhimmiyar rawa a wajen bunƙasar maƙera da sauye-sauye
a garin Gusau, domin kuwa zamani ya kawowa maƙera kayan aiki na zamani da suke gudanar da sana'ar su ba
tare da wata doguwar wahala ba, Misaɓi kamar na'urar gutsuntsura ƙarfe da daddatsa shi a cikin ƙanƙanin lokaci, ƙarfen kangarwa wanda ake amfani da shi domin bada iska ya
rage masu wahala a maimakon aiki da zuga-zigi, magic coal, sabon gawayin d
zamani ya zo ma maƙera shi wanda ba ya saurin zama toka
da saurauransu.
Haka kuma, sauyawar zamani ya ƙarawa sana'ar ƙira a nan Gusau ta
gomashi a kan kayan da ake ƙerawa wayan da suka
kwaikwaya daga Turawa, domin kuwa kayan da maƙeranmu na gargajiya suka kwaikwayo daga Turawa suka ƙera nasu sunfi nagarta da aminci a idanun al'umma,
wananan dalilin ne ya sa jama'a da dama ke tururuwar sayen kayan da maƙeranmu suka ƙera da kuma waci da
kayan da Turawa suke shigowa da su.
Haka kuma, fatara da rashin aikinyi da ya yi katutu a nan
Gusau ya saka matasanmu 'yan gado da ma wayan da ba gadar sana'ar sukayi ba
tsunduma cikin wannan sana'ar ta ƙira domin samun
abin rufin asiri.
4.7.2 TASIRI ZAMANI A KAN KAYAN
SARRAFAWA
Zamani ya yi tasari sosai a kan kayan sarrafa da Hausawa
suke amfani da su na yau da kullum, domin kuwa kayan da maƙeranmu ke ƙerawa, zamani bai
barsu ba sai da ya ratsara takansu, Misali, zamani ya zo ma sana'ar wanzanci
wani sabon al'amari a ɓangarin aski, wato amfani da Reza a maimakon aska da muka
sani tun talili, kuma wannan reza tayi tasiri sosai a wurin jama'a, yanzu haka ƙididdiga ta nuna saba'in a cikin ɗari na wanzaman
wannan zamani sun dena amfani da aska wurin aski sun koma amfani da reza. haka
kuma binciken da nayi na gano cewa jama'a da dama a wannan garin na Gusau sunfi
buƙatar aimusu aski da reza a maimakon amfani da reza. haka
kuma wani dalilin da na gano na kyamar saki da saka da jama'a keyi, shi ne wai
gudun kamuwa da wata cuta ko rahin lafiya da aski da aska ke haifarwa na yi ma
mutum aski fiye da ɗaya da aska ɗaya.
Haka kuma a ɓangaren noma na duƙe tsohon ciniki,
zamani yazo wa manoma wani sabom mashin na aikin noma a maimakon amfani da
galmar shanu, wannan mashin ɗin yana iya ɗaukar awanni yana aiki ba tare da wata matsala ba, haka
kuma, aikin wannan mashin ya lunka aikin da ake yi da galmar shanu nesa ba kusa
ba, haka kuma masu wannan aikin da wannan mashin ɗin sunce sunfi
samun sauƙin aiki da sari da kuma rage masu
wahalhalu da wannan mashin ɗin saɓanin aiki da galmar shanu, haka kuma wani bincike da na
gudanar mutane da dama musamman a karkaru ko ƙauyika sun rungunmi amfani da wannan mashin ɗin saɓanin aiki da galmar
shanu musamman inda matsalar tsaro tayi ƙamari.
Haka abin ya ke ɓangaren sare ciyayi, domin kuwa
zamani ya zo da wani mashi na yanke ciyayi saɓanin amfani da adda
ko lauje, wannan mashi ɗin shima ya yi tasiri ƙwarai da gaske a sha'anin yanke ciyayi musanman a cikin
birane, domin kuwa makarantu da ma'aikatun Gwmnati duk sun rungumi aiki da
wannan mashin ɗin, domin kuwa ɗaiɗaiku ne kawai ke
amfani da adda ko lauje duk ankoma amfani da wannan mashin na yanke ciyayi
domin rage wahalhalu da kuma sauri a wurin aiki.
4.7.3 ZAMANI DA ABUBUWAN SARRAFAWA
Mallam Bahaushe na cewa "Zamani riga" shakka
babu zamani ya yi tasiri a kan abubuwan sarrafawa, domin kuwa samun injinin
surfe da na niƙa da kimiyyar ƙere-ƙere ta zamani ya
samar wa Hausawa ba ƙaramin rage masu wahalhalu ba ya yi,
domin kuwa a da can matanmu na Hausawa sukan sha baƙar wuya kafin su samar da garin da za a yi amfani da shi
wurin tuwo ko fura ko dambu ko kunu, amma kimiyyar zamani ta samar da injinonan
markaɗe daban-daban domi sauƙaƙawa al'umma.
Haka a ɓangaren more rayuwa, kimiyyar ƙere-ƙere ta zamani ta
samar wa al'umma wata na'urar firji manya da ƙanana domin samar da ruwan sanyi da ƙanƙara domin amfani da
su wajen more rayuwa wanda a da can baya Hausawa ba su da su. haka kuma wannan
na'urar ta firjin ɗin ana aje kifi ko nama da abinci domin gudun lalacewa.
4.7.4 SAUYE-SAUYEN ZAMANI A KAN
KAYAN DA AKE ƘERAWA
Zamani ya kawowa sana'ar ƙira sauye-sauye da dama a kan kayan da ake ƙerawa, zamani ya
zo da wani sabon al'amari ta ɓangarin muhalli, domin kuwa tagogi da kofofi da makullai
da maƙeranmu ke samarwa sun zama tsohon ya yi, gidaje da
makarantu da ofisoshi na Gwamnati da ake sanyawa duk anyi watsi da tagogi da ƙofofi da maƙeranmu ke samarwa,
ankoma amfani da wayan da zamani ya samar domin sunfi kyalkyali da ado,
Haka a ɓangaren sarar itace, zamani ya samar da injinin yanke
itace wanda aikinsa ya zarce aikin da ake yi da gatari, domin kuwa aikin wannan
injini ya sha gaban na gatari nesa ba kusa ba domin kuwa a cikin ƙanƙanin lokace zai
yanka itace mai tarin yawa.
Haka abin ya ke a ɓangaren dafa abinc,i zamini ya taka
muhimmiyar rawa a wajen rage amfani da murahunmu na gargajiya da maƙeranmu ke ƙerawa, domin kuwa
zamani ya samar da wata tukunya da ake kira da suna (Silinda) wadda ake sakawa
iskar gas a cikinta domin amfani da wurin dafa abinci ko abin sha, mutane da
dama sun karkata ga wannan silinda domin da abinci acikin sauri da rage
wahalhalu ga mata gida.
Haka kuma an samu sauyi a ɓangaren ludayi da
muke amfani da shi a wurin shan fura ko kunu, domin kuwa zamani ya zo da ludayi
na robobi da kuma kawar da ludayin da maƙeranmu ke ƙerawa.
4.8 NAƊEWA
Wannan bani na huɗu mun kammala shi ne ta hanyar kawo
asalin ƙira a garin Gusau kafin zuwan
Turawa, da kafuwar maƙeran farko a Gusau, da hanyoyin
samar da kayan sarrafawa, da kayan aikin ƙira, da abubuwan da
ake ƙerawa, da dangantakar maƙera da al'umma, da muhimmancin ƙira ga al'umma a yau, da tasirin zamani a sana'ar ƙira a Gusau, da tasirin zamani a kan kayan sarrafawa, da
kuma zamani da abubuwan sarrafawa, da sauye-sauyen zamani a kan kayan da ake ƙerawa, sai kuma kammalawar babin ya zo a ƙarshe.
BABI NA BIYAR
KAMMALAWA
5.0 SHIMFIƊA
Wannan babi ya kalli
yadda sakamakon wannan bincike ya kasance. Kowa ne biciki yana da sakamakon yin
sa domin gano ko binciken wani abu, tare da bayyanar da sakamakon gudanar da
shi. Wannan babin shi ne babi na ƙarshe a wannan
aikin inda an fara da shimfiɗa da kuma sakamakon binciken da kuma shawarwari daga ƙarshe sai naɗewa.
5.1 SAKAMAKON BINCIKE
Sakamakon wannan bincike ya sa an ƙara fahimtar muhimmancin sana’ar ƙira, a
cikin garin Gusau tare da taimakon ta ga al’umma. Haka kuma sakamakon
wannan bincike ya sa an gano yadda ake gudanar da aikin sana’ar ciki da
wajensa. Sakamakon bincike ya bayyana matsayin sana’ar ƙira da irin tasirin da zamani ya zo da shi. Wanda kuma
zamanin ya ƙara bunƙasa tattalin arziki
da kuma hana zaman banza. Bincike ya gano cewa, mafi yawan masu aiwatar da
wannan sana’a a Gusau. Zamani ya shiga wannan sana’a kuma an samu ƙarin inganci da
kayan amfani na wannan sana’a. Sana’ar ƙira a wannan
lokaci, zamani ya samar mata da wasu kayan aiki baya ga waɗanda aka sani a
dauri. Haka kuma kayan da ake samu a sana’ar ƙira sakamakon tasirin zamani sun haɗa da: murhun gawai,
murhun icce na zamani da ake yi da rodu, bindiga mai tashi fiye da ɗaya, asusun ajiya,
mabuɗan shago, ƙofofin ɗakuna, tagogi na ƙarfe, jiragen wasa na yara, motocin wasa na yara. Daga ƙarshe sakamakon
bincike ya sa wannan bincike zai zama wani fage na nazari da kuma faɗaɗa bincike.
5.2 SHAWARWARI
Ganin wannan bincike ya kammala wannan yana nuni da cewa
babu shakka akwai wasu abubuwa da mai bincike ya hango waɗanda yake son ya
nusar da al’umma ta hanyar ba su shawara. Da wannan na ga ya dace in zo da
waɗannan shawarwari da za su taimaka. Waɗannan shawarwarin
sun haɗa da:
a)
Ya
kamata a ci gaba da wannan bincike daga inda aka tsaya domin samar da
ingantaccen nazari a kan tasirin
zamani ga sana’ar ƙira.
b)
Yaɗawa tare da bayyana
wannan bincike a duniyar Hausawa domin samun masaniya a kan muhimmancin wannan sana’a.
c)
Ya
kamata wannan aiki ya shiga cikin rumbun ilimi domin masu nazari
d)
Lallai
wannan bincike zai ƙara ba masu sana’ar ƙwarin guiwa don intanta sana’arsu
e)
Masu
wannan sana’a ya dace su tanadi kayan aiki na zamani da za su sauƙaƙa wajen wannan sana’a.
f)
Mutanen
da suka gaji wannan sana’a da waɗanda suka yi haye,
ya dace su yi aiki kafaɗa da kafaɗa don bunƙasa sana’arsu.
g)
Akwai
buƙatar hukuma ta fito da bayar da tallafi ga duk masu
wannan sana’a.
5.3 Naɗewa
Wannan babi wanda shi ne babi na ƙarshe a wannan bincike, inda aka bayyana
sakamakon bincike da kuma shawarwari tare da naɗewa.
MANAZARTA
Abubakar A.T (2015)Ƙamusun Harshen
Hausa, Zaria: Northan Nigeria publishing company limited.
Alhasan, M.H (1982) Zaman Hausawa,University Press.
Abubakar, B. (2004) Sana’ar ƙira a jahar Zamfara.
Bayero, K. (2006) C.N.H.N Ƙamusun Hausa Ahmadu Bello University press limited.
Cary ,H.B (1989) Modern Welding Technology: printed in
the United state of America.
Ɗankande, da wasu (2017) Nazari akan tasirin siddabarun maƙera a sana’ar ƙira.
Garba, C.Y (1991) Sana’o’in Gargajiya a ƙasar Hausa, Ibadan: Spectrum Book Limited.
Gusau, S.M. (1999) “Muhimman Garuruwan Ƙasar Hausa: Waiwaye a Kan Tarihin Kafuwarsu a Taƙaice”. The West
African Journal of Language, Literature
and Criticims (A Multilingual
Bi-lingual) Vol. 1 No. 2
Skinner, N. (1978). ƙamusun Turanci da Hausa.Zaria: Northern Nigeria
publishing company.
Shafa’atu, da wasu (2016) Nazari a kan wasanni
tsakanin maƙera da wanzamai a jahar Zamfara.
Zurmi, Y.S (2010) Matakin Nazarin Hausa: Kano Printing
Press .
http/www.ansoshi.com
(2018/12) Matsayin Sana’ar Gargajiya na Hausawa html.
http/www.amsoshin.com
(2019/01/) Noma Igiya madora kaya inyi ba-da-kai. Html
https/www.amshoshin.com (2020/01) wanda ya tuna bara bai da tanadi html
MUTANEN DA AKA YI HIRA DA SU
S/No |
Suna |
Shekaru |
Matsayi |
Adireshi |
Rana |
1 |
Maƙera Aliyu Barau |
67 |
Sarkin Maƙeran Sarkin Katsinan Gusau |
Sabuwar Kasuwa Gusau |
12/7/2023 |
2 |
Ummaru Maƙeri |
60 |
Maƙeri |
Gadar Zangila |
13/7/2023 |
3. |
Bala Musa |
35 |
maƙeri |
Fonfon Maishanu Gusau |
14/7/2023 |
4. |
Hussaini Maƙeri |
46 |
maƙeri |
Bakin Silma |
15/7/2023 |
5. |
Mal. Lawali Umar |
64 |
Maƙeri |
Sabuwar kasuwa, Gusau |
16/7/2023 |
No comments:
Post a Comment
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.