Kwata kwata kasa faɗin saƙon kawun Fa'iza yai dan shi baiga dalilin da za a ce yaro ya saki yarinya ba sai dai ya ce wa Fajarudden ɗin kar ya tafi ya jira sirikin nasa yana hanya bai kawo komai ba ya jira zatonsa ko mahaifin Fa'iza ɗin na san suyi hotuna ne.
Ko da mahaifin Fa'iza ɗin ya ƙaraso baibi ko takan yayan nasa ba ya hau
tambayar ina waliyyan ango anyi sa'a basu tafi ba ya hau masifa a asakar masa ɗiya ya kuma ƙi faɗin dalili sai da manyan
mutane suka sa baki sannan ya ce.
Sabida yaro baida asali bakuma su faɗa mana ba sun munafurcemu
ran yayan mahaifiyar Fajar ya ɓaci
ya ce kamar yaya yaro da ubansa ace bai da asali mahaifin Fa'iza ya ce in yana
da ina dangin ubansa ina kuma uban ai bana jin mutum da ɗansa ace bazai zo aurensa ba koda kuwa akwai
waliyyi da ya naɗa
sannan ace arasa mutun guda daga danginsa in kuma akwai ina suke sai dai na
matarsa abin ai da mamaki da na kasa yadda sai dai danai nazari na yadda dole
asakar mun ɗiya.
Yah ni abin da me ya sa kukai saurin ɗaura auren nan ba ko ɗam afrikan time ɗinnan ai ya ci kuyi.
Wallahi ɗiyata
bazata zauna da wanda ba'asan asalinsa ba balle ya gudu ya barta kowa ya san
yaron nan iyayansa zuwa sukai da shi sa'annan kowa ya san wanda yake riƙe da
shi baya wani nuna kulawarsa akansa shedar ba ɗansa
bane shi kansa wanda ake iƙirarin shi ne mahaifin nasa baida asali ke nan shege ke riƙe da
shege ina ba zai yiwuba wallahi.
Wani dattijo ya ce anman dai kasan baka kyayta
ba ai da tun sanda ya fara neman aure za ka bin cika mahaifin faiza ya ce
kuskuren da nai ke nan kyawawan halinsa suka ringaye ni na kasa bin cikawa
sedai da aka kawon hujjoji masu karfi na ji araina bai dace da zurriyar mu ba
dan da kaina bazan ma zurriya ta tabo ba.
Dattijon ya kuma cewa kaji ba ka ce yanada
kyan hali hakan be wadatar ba ina aurene wannan ba kasuwanci ba dole asakar min
ɗiya.
Fajar ya ce duda na san akwai abin da
iyayenake boyewa sedai ina da tabbacin su suka haifen sa'annan a musulunce babu
inda aka ce ba'a auren mara uba dan ba shi yai lefin dan Haka wallahi bazan
saki matata ba aure an ɗaura
saidai mutuwa ta rabamu.
Adam ƙanin Fajar cikin kuka ya kira mahaifinsu
ya sanar masa aikuwa rai a ɓace
ya ce ya cema Fajar ɗin
lallai lallai ya sakar musu ɗiya
aikuwa ya ce ina ai shi fa babu saki a tsarinsa dan haka babu saki tsakaninsa
da Fa'iza aiko mahaifin Fa'izan ya shago masa wuya yana masifa ya sakar masa ɗiya shi kuwa ya ce ina
baifa san zance ba.
Jin abin da Adam ya faɗa masa yasashi daurewa ya tawo jami'an dan bai
da nisa da inda yake abin da baiyi zato ba wato zuwa gurin ɗaurin auren Fajar kai tsaye
inda Fajar ke tsaye mahaifin Fa'iza riƙe da wuyansa yai hannu ya sanya ya cire
hannun Mahaifin Fa'iza gami da gyarawa rajar rigarsa.
Kallon Fajar ɗin
yai ya ce Deeni fikin nutsuwa Fajar ya dubeshi in har ka yadda nine mahaifinka
inaso ka saki yarin yar mutumin nan Fajar ya ce anman Abba karka ce komi inaso
inma baka yadda ni na haifekaba inaso ka dubi darajar riƙe ka danai ka saketa dan
Allah karka sake mintuna da auren ta akanka dan Allah ka saketa yai saurin riƙe
hannun mahaifinsa Abba baka buƙatar roƙona.
Wayarsa ya ɗauka
ya turawa Fa'iza saƙo kamar haka.
Assalamualaikum
Abubuwa sun
faru a dedai wannan lokaci ba wannan saƙon naso turo miki ba adai dai wannan
lokacin naso ace turo miki nan ina tayaki farin cikin gami da murnar zamtowa
matar Fajarudden kamar yadda mukai ta mafarki saidai abubuwan da suka faru
yanzu suka sauya wannan saƙo zuwa ga waninsa ba haka naso ba sai dai haka ƙaddara
ta zaɓar mana
Fa'iza ki yi haƙuri aurenmu baida tsawon rai na yanke shi
a yanzu kamar yadda aka ƙullashi baki da iddata ina miki fatan Alheri Allah ya baki
miji nagari.
Tsohon mijinki
mai sanki
FAJARUDDEEN
Ya dubi Abban
Fa'iza karka damu na tura mata saki babu auren ɗiyarka
akaina duka igiyoyin na yanke ya riƙe hannun mahaifinsa sukai waje inda
sauran ‘yan
uwansa suka mara masu baya.
Suka bar sauran jama'a na cece kuce inda wasu
ke faɗin tabbas
mutumin da ya zo shi ne mahaifin Fajar ɗin
dan kamarsu ta isa in banda shekaru ma zakayi tsanmanin yan biyu ne sedai da
yawa sunfi ga eh mahaifinsa ne anman wataƙil ba aure ya haifeshi ko kuma shi ne
mahaifin baida asali kowa dai da abin da yake faɗe.
Fa'iza ce zaune ita da ƙawayenta sun kewaye ta
suna faman tsokanar ta suna jiran shigiwar saƙon angon nata dan mata albishir ɗin an ɗaura.
Jin shigiwar saƙo wayar ya sa sukai gun wayar inda Fatima
ƙanwar
Fajar tai sauri ta ɗauka
dan ita tun da aka fara bikin tana ga gayyar amarya dan ba ta da aminiyar da ta
wuce amar yar yayan ta.
Azuci take karantawa ganin saƙon da ɗan tsawo sukai kanta dalla
malama ki karanta mata ta ji aikinsan bake ya turowa ba kasa karantawa tai inda
ta ji jikinta duk yai sanyi ta miƙawa ummi wayar gami sa zarar hijabinta ta
bar gidan.
Suka bita da kallo kamin su mai da hankalinsu
kan wayar ummi ta hau karantawa jin abin da take karantawa ya sanya Fa'iza tai
zaton kunnuwanta ba dedai suka jiyo mata ba tai saurin fizge wayar ta hau
karantawa sai ganinta sukai luuuuu tai ƙasa inda wasunsu suka kurma ihuuu wasu
kuma sukai kanta....
Shi kuwa
mahaifin Fajar suna barin gurin ya kwace hannunsa daga na Fajar yai waje Fajar
ya bi bayansa yana faɗin
ka tsaya mu tafi tare yai masa banza yai gaba.
Koda Fajar yabar makarantar kasa tafiya yai
sabida tsaɓar ɓacin rai gefen titi ya
parker motar inda ƙaninsa ya ce yah ko za ka fito in jamu batare da musu ba ya
fito inda Adam ya amshi jan motar.
Shi kuwa mahaifin Fajar yana fita ya tsaida
adai daita sahu yai gida.
Kamar yadda gidan biki yake haka ya tadda
gidan nasa mata nata sha'aninsu anata girge girken tarar yan daurin aure ya
shigo duk sunyi mamakin ganinsa ko duk sunyi mamakin ganinsa ko kaɗan bai kama da wanda aka ɗaura auren yaronsa ba.
Salima salima yahau kira tai saurin fitowa
tabi bayansa ganin yai ɗakin
su Adam tana shiga ta ce lafiya dai malam ka dawo yanzu kaida mukai bazaka dawo
ba sai dare ya raba yai shiru yana juya abin da yakesan faɗa mata kafin ya ce Adamu ya
kirani ɗazun yake faɗan iyayan yarinyar nan da
Deeni zai aura sun takura sai ya saketa.
Ta waro ido wane irin saki nima abin da nagani
ke nan hakan ya sa naje gun ɗaurin
auren saidai abin da nagani na yanda mahaifin nata kewa Denin da tijarar da
yake ya tunzurani ya sa dole nasa Deenin ya saketa Malam saki fa ka ce eh haka
ubanta ya nema.
Anman komaine ba ta cancanci saki ba ranar ɗaurim aurenta hakane Salima
ai na sani arayuwata kullin nine mai lefi ba haka bane malam ba haka nake nufi
ba koma me kike nufi na ji ya miƙe zai fice sai dai juwar data ɗebeshi yasashi faɗuwa ƙasa yup tai kansa tana
kuka inda yai dedai da shigiwar su Fajar suka kwasheshi hankali tashe sukai
asibiti.
Suka bar
sauran ‘yan
biki da tunanin kome ya faru.
Su Fajar basu jima da fita ba kawun Fajar ya
shigo wato yayan mahaifiyar su cikin fushi yake kwalawa mahaifin su Fajar ɗin kira danshi ya gaji dole
mahmud ya mance da komai ya sauya shawara ai ba lefin yaransa bane sai dai nan
yasamu mummunan labarin faɗuwar
sirikin nasa.
Matarsa ta tambayeshi me ya faru nan ya faɗa musu komi hankalimsu ya
tashi shi kuma ya fice zuwa asibitin duda kuwa bai san wanne bane sai ahanya
yake tambayar Adam a waya ya faɗa
masa.
Kawun na fita suka hau cece kuce inda da yawa
suke cewa banda abin Mahmud ai ba yaransa sukai masa lefi ba bacin haka tsahon
shekarun da aka shuɗe ya
ci ace ya mance da komai ya rungumi kaddarar sa.
Fatima kuwa ƙanwar Fajar data fito daga gidan su
Fa'iza hankali tashe tai gida dan jin ko gaskene saƙon da ta karanta sai dai
tana zuwa ƙofar
gida taga yayyunta riƙe da mahaifinsu ta mara musu baya sukai asibiti cikin kuka.
Koda kawu yaje asibiti duk sai hankalinsa ya
tashi jikinsa yai sanyi ganin jikin mahmud ɗin
kai bazakai zaton zakaje bakin ƙofa ka dawo ka tadda shi da rai ba duk
sai ya mance da abin da ya faru ɗazun
ya mai da hankali wajen ganin samuwar lafiyar sirikin nasa.
Gidansu Amarya Fa'iza kuwa ihun ‘yan
matan yaja hankalin iyaye akai ciku hankali tashe ake tambayarsu me ya faru
kursum ce ta daure ta ce saki mijin nata ya turo mata har uku juwa ce ta ɗebi mahaifiyarta luuuuu ta
tafi za ta faɗi akai
saurin tareta.
Ƙanwar maman Fa'izan ce ta ɗebo ruwa dan shafawa
Fa'izan saidai shafawar duniya taƙi motsi ala dole aka kwasheta sai asibiti
saida ta yini sir sannan ta san inda kanta yake yayim da duk hankalin iyayanta
ya yashi zaton ko zasu rasa ɗiyar
tasu.
Da kuka ta farka tana faɗin dan Allah kuce masa
wallahi ina sansa karya sakeni mahaifinta yai saurin zuwa ya kamo hannunta ki
yi haƙuri
Fa'iza sakin shi ne mafi alkairi tai saurin kwace hannunta cikin kuka tana
girgiza kanta wallahi Abba bashi ne mafi alkairi ba Abba in babu malam wallahi
bazan iya rayuwa ba mutuwa zan yi cikin fishi mahaifin nata ya daka mata tsawa
ke Fa'iza tai saurin shiga tai taiyinta dolema ki haƙura da shi dan wallahi
aure kedashi sedai bayan raina kina ji na ko ta gyada kai alamar eh ya tashi ya
fice.
Yana fita ta ɓarke
da kuka dakyar aka samu tai shiru abinci kuwa kasa ci tai washe gari aka
sallamesu sukai gida inda tuni yan biki suka watse.
Agida ne mahaifinta ya kirata yake faɗa mata shi ya sa akai sakin
da dalilinsa hankalinta ya tashi ta ce wallahi Abba Fajar ba shege bane kawai
mahaifinsu ne ba me san shiga sabgar abubuwan su ba anman wallahi ba shege bane
dan Allah Abba kayi haƙuri ni wallahi ko shi kaɗai
ya girma ajuji wallahi ina san sa haka wallahi mutuwa zan yi in ba shi .
Ke banfa san rashin ta ido ki mutu ɗin kinji ko anman wallahi
indai wannan yaron ne keda aurensa sedai inna mutu inkinga mutuwar ta fiye ki
mutu wani kikai wa kanki kikaiwa yai ficewarsa yabarta tana faman kuka.
Kwanan Abban su Fajar uku a asibiti baisan
inda kansa yake ba duk sun fidda rai inda hankalun matarsa wato mahaifiyar su
Fajar yafi na kowa tashi dan tuna lokacin Fajar na ƙarami da ya taɓa irin wannan faɗuwar likita yai ta ja musu
kunne kan zasu iya rashi lokacin ma da ƙarfim sa bare yanzu da shekaru suka ja.
Cikin ikon Allah likitoci suka shawo kan abin
inda suka samu daƙyar da taimakon Allah nimfashinsa ya dai daita.
Hankalim iyalin nasa bai kwanta ba sai da
sukaga yana iya buɗe
ido duda baya musu magana saidai alamu sun nuna yana cikin hayyacinsa maganar
ce dai baisan yayi.
Shi kuwa ido kawai yake binsu da shi
tausayinsu duk ya cikasho yana ɗaya
daga dalilin da ya sa baya nuna musu kulawa sabida baya san in ya mutu suyi
rashin wani ginshiƙi arayuwarsu sa'annan baya san su tambayeshi ina danginsa sai
dai yana ganin rashin nuna kulawar bazai rage komai na soyayyar da Allah kan
dasawa yaro na soyayyar iyaye ba agaresu.
Umman Fa'iza ce zaune ta rafka tagumi abin
duniya duk ya isheta tun wayewar garin yau ba ta sanya Fa'iza a idon ta ba
batajin ko Sallar asuba tayi bare azahar ga mangariba na kawo kai gashi
mahaifinta ya ce afita sabgarta intaga ana nuna damuwa da damuwarta saita fi ƙin
warewa da wuri.
Sai dai ance soyayyar uwa daban ce ga yaranta
ganin shiru ya sa umman Fa'izan zuba abinci tai ɗakin
faizar dan kai mata dan ita kam bazata bari yunwa ta illata mata ɗiya ba dame zataji da yunwa
ko kuwa da rashin mijin da ta gama tsara rayuwarta ko da shariyar iyaye.
Tana shiga ɗakin
ta saki farantin abincin tai ciki da gudu mai za ta gani Fa'iza ce kwance shame
shame da alama ma ta mutu gefenta kwalbar fiya fiya ce da takardar maganin ɓera da alamu su ta haɗe guri guda ta shanye
ummanta ta hau girgizata cikin kuka sai dai ina ba ta ko motsi.....
Thank you for
reading😍
💞
Don't forget to vote and Comment 💞😍
Fatan zaku mun
afuwa na rashin posting akai akai na san sosai kuna haƙuri da ƙailula
ta na gode da karantawa 😍
Fajar ne zaune
kamar ko yaushe agefen gadon mahaifinsa kamar yadda suka saba tun fara jinyar
sa shirune abokin hirarsu basa ce masa komai kamar yadda ko ido in ba lokacin
sallah ba baya buɗewa.
Deeni! Deeni!! Fajar ya tsinkayi muryar
mahaifin nasu na kiran sunansa yai saurin matsawa kusa da shi yana faɗin Na'am Abba mahaifin nasu
ya miƙo
hannunsa miƙon
hannunka Fajar yai saurin kamo hannun mahaifin nasa.
Kuma mai-maitawa yayi Deeni fajar ya ce na'am
Abba na san kai mai haƙuri ne tun da ka taso kake haƙiri da yanayin da ka taso ka cince mu
ciki inaso ka ƙara kan wanda kake da shi na san bakaji daɗin yadda iyayan yarin
yarnan suka hanaka aurenta ba sedai inaso kasani bakanka ne farko ba kamar
yadda ba kanka ne ƙarshe ba.
Ya kuma riƙo hannun mahaifin nasa da kyau wallahi
Abba ni guna komai ya wuce dan Allah kaima ka daure ka mance dan Allah ka cire
damuwa aranka ko kasamu sauƙi.
Deeni da gaske kana san in samu sauƙi yai
saurin gyaɗa kai eh
Abba to shi ke nan kamin wannan alfarmar matsayina na mahaifinka inma baka
yadda kamar da muke ta isar maka hujja na nine mahaifinka ba inaso kamin
alfarma matsayin wanda ya riƙeka.
Abba wallahi koda bama kama bazan taɓa yadda bakaine mahaifina
ba baka buƙatar
neman alfarma ta sedai kawai kaban umarni inyi inaso kasa amaidawa mutanen nan
kayan jerensu sannan inaso dan Allah ka daure in zakai aure ka je ka nemo me taɓo arayuwarta ta yadda bame
maka gori adanginta dan Allah in sonane ka je ka nemo aure gidan marayu ko
wadda kasan ba ta da uba.
Yai saurin kallon mahaifin nasa ya gyaɗa masa kai na san kajini
indai ba haka kayi ba ina tabbatar maka da tabbas kuwa mutane bazasu dena kashe
maka aure ba ni kuma bazan iya dena shiga damuwa ba kamar yadda bazan iya
bayyana maka tambayoyin da kake ma mahaifiyarka ba.
Fajar ya ce shi ke nan Abba insha Allahu zan
yi duk abin da kake so mahaifin nasa ya ce na gode Deeni Allah ya maka albarka
ya mai da idanunsa ya rufe fajar ya ce amin Abba.
****
Ita kuwa umman
Fa'iza ganin ganin ɗiyar
tata taƙi
motsawa ya sa tai waje tana kuka a farfajiyar gidan taci karo da Bashir yana ƙoƙarin
shigowa da hanzari hankali tashe yake faɗin
mami lafiya cikin kuka take faɗin
Fa'iza tana nuna cikin gida mai ya sameta yake tambaya hankali tashe ganin
mamin taƙi
faɗa masa yai cikin
gida aguje.
Kai tsaye ɗakin
su Fa'izan ya nufa yadda ya ganta ya tada masa da hankali bai tsaya wata wata
ba ya sa hannunsa a ƙirjinta zuciyarta ba ta bugawa hankalinsa ya tashi yai saurin
kamo hannunta dan duba pulse kaɗan
kaɗan yake jin bugun
da alama da ranta yai saurin kamo gefen rigarsa ya goge mata sauran maganin
dake bakinta.
Seda ya ba ta temakon gaggawa yai ɗauketa mami ta mara masa
baya sukai asibiti ko gidan ba ta rufe ba.
Asibitin malam suka kaita har aka shigar da
ita ɗalin duba marasa
lafiya masu buƙata ta gaggawa ummanta ba ta dena kuka ba danma kawai Bashir
ya nace ba ta mutu ba anman itakam tasan ta mutu.
Likitan ya jima a ciki kafin ya fito yana cire
safar hannu ta asibiti ya dubi Bashir biyoni office yabishi shida mamin Fa'iza ɗin.
Munyi sa'ar ceto ranta sakamakon ba wani me
yawa sosai tasha ba sannan kun ba ta temakon gaggawa agida tasamu temporary
heart failure ne hakan ya sa nunfashinta yake ɗan
samun matsala sabida maganin ɓera
data sha Alhamdulillah yanzu komai yazama normal muna saka ran zuwa gobe ta
farka mami ta hau godiya.
Shikuwa Abban su Fa'iza koda ya dawo ya tadda
gida a buɗe ya shiga
ba kowa yahau masifa wato dan wulaƙanci salon azo amasu sata shi ne zasu
fice subar mai gida na kowa.
Wayar umman Fa'izan yahau kira sedai ga
mamakinsa wayar na gida hankalunsa ya kuma tashi.
Koda suka fito daga office ɗin Bashir ya ce bari ya
kira Abban su Fa'izan ya faɗa
masa mami ta ce to.
Koda ya kirashi suka gaisa ya ce Abba daman
mami ta ce in faɗa
maka Fa'iza ba ta da lafiya muna asibiti yai tsaki banace karta shiga sabgar
yarinyar nan ba wato ban isa aji maganata ba ko to maza kaɗauko su sudawo ta mutu.
Bashir yai saurin cewa dan ganin Abban zai
kashe Abba guba Fa'izan tasha bama tasan inda kanta yake ba innalillahi Abba
yahau kira murya na rawa yake tambayar ko suna wane asibiti ne nan Bashir ya faɗa masa ko wayar bai kashe
ba bare ya rufe gidan yai waje.
Kotakan motarsa baibi yai bakin titi dan
baijin zai iya jan mota ayadda yake jin ransa hankalinsa yai ƙololuwar
tashi wato mutuwar da take cewa zatayi yana cewa ta mutum ita da gaske take
shikam indai za ta farfaɗo
zai faɗa mata shi dan
ta cire wannan yaron aranta ne yake faɗin
haka yana kumayin haka ne dan farin cikinta.
Ko a asibiti yadda yaganta kwance kamar gawa
ya kuma tada masa da hankali.
***
Shi kuwa Fajar
koda Adamu ƙaninsa
ya zo ya shirya yai gida seda yai wanka sannan ya faɗawa ummansa cewar Abba ya ce amaidawa su
Fa'iza kayan jerensu umman ta ce nima nai tunanin haka da naso a aika musu suzo
anman tun da ya nuna a mai da musu ka samo mota ya ce to umma ya fice.
Komai nasu aka sanya a mota kalifa ƙanin
fajar ya musu jagora.
A farfajiyar
gidan aka ajiye kayan seda aka gama shigar dasu sannan kalifa yahau sallama dan
faɗa musu an ajiye
kayan shirun da yaji yasashi fitowa da ƙanwar Fa'iza ɗin ya ci karo ta taso daga islamiyya ya ce
yawwa kadija sakamakon duk ya sansu in kin shiga kice ka ummanku ga saƙo nan
inji ummanmu ta ce to yah kalifa tai ciki shikuma yai gida.
Thanks for reading 😍
Rubutawa
Faɗima Fayau
No comments:
Post a Comment
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.