Addu’ar Khatmul Ƙur’aan

    𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

    Assalaamu Alaikum Wa Rahmatul Laah. Allaah-gafarta-malam! Wai addu’o’in da suke rubuce a ƙarshen Mus-hafin Alƙurani dukkansu ingantattu ne? Kuma ko za a iya amfani da su?

    𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

    Wa Alaikumus Salaam Wa Rahmatul Laahi Wa Barakaatuh.

    Al-Imaam Ibn Abi-Daawud a cikin littafinsa Al-Masaahif ya riwaito athari da isnadai sahihai guda biyu daga Ƙataadah cewa:

    كَانَ أَنَسُ بْنُ مَالِكٍ - رَضِيَ اللهُ عَنْهُ - إِذَا خَتَمَ الْقُرْآنَ جَمَعَ أَهْلَهُ وَدَعَا

    Anas Bn Maalik (Radiyal Laahu Anhu) idan ya zo sauke karatunsa na Alƙur’ani yana tara iyalinsa, ya yi addu’a.

    Kuma ya ƙara riwaitowa da isnadi sahihi daga Tabiin nan mai daraja Al-Hakam Bn Utaibah cewa: Mujaahid da Abdah Bn Abi-Lubaabah (Rahimahumul Laah) sun gayyace shi, suka ce:

    إِنَّا أَرْسَلْنَا إِلَيْكَ لِأَنَّا أَرَدْنَا أَنْ نَخْتِمَ الْقًرْآنَ ، وَالدُّعَاءُ يُسْتَجَابُ عِنْدَ خَتْمِ الْقُرْآنِ

    Mun gayyace ka ne domin muna son sauke karatun Alƙur’ani, kuma addu’a ana karɓar ta a lokacin sauke karatun Alƙur’ani.

    Sai kuma ya sake riwaitowa da isnadi sahihi daga Mujaahid (Rahimahul Laah), yana magana a kan malamansa cewa:

    كَانُوا يَجْتَمِعُونَ عِنْدَ خَتْمِ الْقُرْآنِ ، يَقُولُونَ : تَنْزِلُ الرَحْمَةُ

    Sun kasance suna taruwa a lokacin saukar karatun Alƙur’ani, suna cewa: Rahama tana sauka a lokacin.

    Al-Imaam An-Nawawiy (Rahimahul Laah) ya kawo wannan a cikin Al-Azkaar, kuma As-Shaikh Saleem Al-Hilaaliy (Hafizahul Laah) ya sahhaha waɗannan riwayoyin a cikin: Sahih Al-Azkaar An-Nawawiyyah, shafi: 103.

    Lura da irin waɗannan riwayoyin daga irin waɗannan manyan malaman ne wataƙila masu buga Mas-hafofin suka sako waɗansu daga cikin addu’o’in da suka zo daga Annabi (Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallam). Domin ko ba komai lafuzzan da suka fito daga bakinsa mai tsarki (Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallam) sun fi na wanda ba shi ba.

    Amma kuma waɗansu malaman ba su yarda a yi amfani da waɗannan addu’o’in a irin wannan wurin ba ko da kuwa sun inganta daga Annabi (Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallam), saboda dalilai kamar haka:

    1. Domin maganar Annabi (Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallam) cewa:

    « الدُّعَاءُ هُوَ الْعِبَادَةُ »

    Addu’a ita ce ibada. (Sahih Abi-Daawud: 1479)

    Ibada kuwa ba ya halatta a yi ta sai tare da samun bayani a kan adadi da wuri da lokaci da kuma surar yadda ake yin ta, bayan an tabbatar da sahihancin riwayar da ta kawo ta.

    2. Annabi (Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallam) da ya ambaci waɗanda ya ambata daga cikin waɗannan addu’o’in bai sanya su daga cikin addu’o’in da ake yi a bayan sauke karatun Alƙur’ani ba. Domin ba a riwaito hakan daga aikinsa ko daga maganganunsa ko kuma tabbatarwarsa ga maganganu ko ayyukan da Sahabbansa suka yi a gabansa ba.

    Kuma ko su kansu su Anas (Radiyal Laahu Anhu) da Mujaahid (Rahimahul Laah) da suka riƙa yin adduoin a lokacin sauke karatun ba a riwaito cewa da irin waɗannan kalmomin ne suka yi amfani ba. Kai! Ba a ma ambaci irin kalmomin da suka yi amfani da su ba, ballantana malamai su duba su ga ko ingantattu ne ta fuskar riwaya daga wurinsu, ko kuwa ba ingantattu ba ne.

    Shi ya sa manyan malaman Sunnah irin su As-Shaikh As-Shuƙairiy (Rahimahul Laah) a cikin As-Sunan Wal Mubtadi’aat, shafi: 201 ya ce:

    وَالدُّعَاءُ الَّذِي فِي آخِرِ الْمُصْحَفِ لَا يَجُوزُ التَّعَبُّدُ بِهِ قَطْعًا ، بَلْ هُوَ مَذْمُومٌ وَمَمْنُوعٌ شَرْعًا ، لِأَنَّهُ مُخْتَرَعٌ وَلَيْسَ مَأْثُورًا ، بَلْ كُلُّهُ بِدَعٌ ضَلَالَاتٌ ، وَتَوَسُّلَاتٌ مَوْضُوعَاتٌ ، فَلَا تَحِلُّ قِرَاءَتُهُ ، بَلْ وَلَا كِتَابَتُهُ فِي آخِرِ الْمَصَاحِفِ

    Addu'ar nan da ta ke a ƙarshen Mus-hafin Alƙur'ani bai halatta a yi ibada da karanta ta ba sam! Kai! Amfani da ita ma abin zargi ne kuma abin hanawa ne a shari'a, domin ita ƙirƙirarriya ce kuma ba a ciro ta daga magabata ba. Kai! Dukkan ta suna cikin bidi'o'i ne na ɓata, kuma ƙarin kusanci ne da ƙirƙirarrun hadisai na ƙarya. Don haka bai halatta a karanta ta ba, haka ma ko rubuta ta a ƙarshen Mus-hafoffin.

    Amma idan wani musulmi ya zauna a bayan sauke karatun Alƙur'anin shi kaɗai ko tare da iyalinsa ko makusantansa ya ɗaga hannuwa ya yi waɗansu addu’o’in neman biyan buƙata daga Allaah Ta'aala, domin koyi da irin waɗancan malaman magabata, ina ganin babu laifi in shaa'al Laah matuƙar dai ya kiyaye waɗansu ƙa'idoji kamar haka:

    1. Kalmomin addu’ar su zama kyawawa kuma da kuɓutattun lafuzza, kamar daga cikin wani hadisi saheeh ko da'eef ko kuma daga cikin fahimtar wani malaminsa ko shi kansa.

    2. Kar ya kafe ko ya na ce a kansu, ya mayar da su kamar waɗansu kafaffun zikirori ko addu’in ibadar da ba dama a sauya su da waɗanda ba su ba.

    3. Kar ya koyar da iyalinsa ko ɗalibansa waɗannan kalmomin, ko ya bari su riƙa kwaikwayon sa wurin amfani da su ba tare da ya yi musu cikakkun bayanai a kan matsayin hakan ba.

    Addu’o’in da aka kawo a ƙarshen Mus-hafin Alƙuranin da ya shahara a hanun alumma a yau kamar Mus-haful Madeenah guda goma ne. Kuma na lura cewa guda bakwai duk suna nan a cikin littafin Addu’aa’u Minal Kitaab Was Sunnah na As-Shaikh Al-Ƙahtaaniy (Rahimahul Laah) kuma ya amince da sahihancinsu a cikin sharhin da Maahir Bn Abdilhameed (Hafizahul Laah) ya yi masa. ¹

    Sauran guda ukun (lamba ta 1 da 3 da 9) kuwa bayaninsu a taƙaice shi ne kamar haka:

    (1). Addu’a ta farko: Al-Imaam Al-Iraaƙiy a cikin Takhreej Al-Ihyaa’: 1/369 ya nuna cewa: Mu’udal ne, watau a cikin isnadinsa an kayar da maruwaita har guda biyu ko fiye kuma a jere!

    (3) Addu’a ta-uku: Al-Imaam As-Sakhaawiy a cikin Al-Maƙaasidul Hasanah: 92 ya kawo shi, kuma ya ce: Yana da hanyoyi da yawa.

    (9) Addu’a ta-tara: Al-Imaam At-Tabaraaniy a cikin Al-Mu’ujam Al-Awsat: 3398, kuma As-Siyuutiy a cikin Al-La’aali’ul Masnuu’ah: 9/46 ya nuna cewa, maruwaicinsa Abu-Ma’amar mai tsananin rauni ne. Kuma Al-Haithamiy a cikin Majma’uz Zawaa’id: 10/160 ya faɗa a kan wata riwaiyarsa cewa: A cikin ta akwai Abdussamad, kuma shi mai rauni ne.

    Daga baya-bayan nan na ga sun cire wannan addu’ar ta Khatmul Ƙur’aan daga cikin Mus-haful Madeenah ɗin. Al-Hamdu Lil Laah

    Allaah ya ƙara mana fahimta a cikin addininmu.

    Sheikh Muhammad Abdullaah Assalafiy

    Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance Damu. . .

    𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

    https://whatsapp. com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G

    𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

    Https://www. facebook. com/groups/336629807654177

    𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

    https://t. me/TambayoyiDaAmsoshi

    ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

    **************************

    Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

    Question and Answers in Islam

    No comments:

    Post a Comment

    ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

    HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.