Ticker

6/recent/ticker-posts

Namiji Shi Yake Lallaɓa Mace

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Assalamu Alaikum malam kayini lafiya Allah yakaro ilimi mlm tambayata yau ita ce saurayi ne da budurwa suke tare yahana ta kula kowa ko da awayane ko chat duk yahana ta ya ce inhar zatana yi tose su rabu duk tadena amma matsalar a nan ita ce malam kullum tunaninsa tanayi a ɓoye kuma itake kiransa setamai miss calls 5 inkuma yakira baya kusa inyamata miss calls a waya seyayi fushi kuma ita taka sa gane wannan lamarin shi ne take Neman shawara da mufita. mun gode

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

Wa'alaikumus salaam. Shawara ta a nan ta yi hakuri ta rabu dashi, shi ne zaifi mata Alkairi.

Abin da ya sa na ce idan za ta iya yin hakurin shi ne, da alama ita ce ta na ce masa, shi ya sa ma yake mata irin wannan, abin da aka San namiji fa, shi ne zaike lallaɓa mace, ba mace bace zatake lallaɓa namiji ba, duk da dai Allah ya kawo mu wani zamani.

Kalli yadda soja ya je da kwarjini a idon mutane, amma idan ya je gida sai ya lallaɓa matarsa, amma in ban da mace ba wanda soja zai lallaɓa, kawai hukunci yakeyi daidai da yadda ya gadama.

Haka Sarki yana da kwarjini a cikin fadawansa da mutanen gari, amma idan ya shiga wajen matarsa, sai ya kaskantar da kansa.

Haka gwamna ana masa jiniya da sojoji da yan-sanda da sauransu amma idan ya shiga wajen matarsa sai ya risina, Kai kowanene ma haka ne.

Amma ke namiji yana hanaki yadda ya gadama. Sabida haka mace tana da kima a musulunci, ki duba yadda manzon Allah ana cikin tafiya tare da ayarin sahabbansa MAZA da MATA kamar yadda imamu maliku ya fitar a cikin muwadda, babin da yake magana a kan sallar kasaru. Da sarkar ummuna Aisha ta tsinke ta faɗi, sai da manzon Allah ya tsaya aka kwana a wurin tare da sahabbai ana neman wannan sarkar ba’a sameta ba sai daga baya, har sai da manzon Allah ya yi barci a wurin, mutane suka ce da sayyadina Abubakar, Kayiwa Aisha magana ta hakura da wannan sarkar, ta tsayar damu, Sabida ita ce ta tsayar da tafiyar gabaki ɗaya.

Ni banga Dalilin da zaisa namiji yana baiwa mace wahala ba ita kuma ta na ce masa, ta rabu da shi kawai, Sabida wallahi na sani wannan kuma kamar a rubuce yake a wurinki, ko da bayan Ya aureki ya dinga azabtar dake ke nan, sai dai idan kin ga ba za ki iyaba ki ce ya sakeki, nan da nan zai mayar dake ba zawara, ko kuma ki yi ta zama tare da shi 'yan uwanki mata suna kallonki a matsayin yar kwawa da naci.

Sabida haka Ni banga Dalilin da zaisa ki na ce masa ba, kullum ke ce mai bashi hakuri, ke ce mai lallabinsa, ke ce Mai nemansa sai ya gadama zai dauki kiranki ba, idan kuma ya kiraki idan kina da wani uzurin da ya sa baki daga wayar ba, ba zai yi miki uzuri ba, zai dinga miki fada ko yana miki fushi.

Ba mamaki ko kina Addu'ah ne a kan Allah ya zaɓa miki Alkairi, sai Allah yake nuna miki cewar wannan ɗin ba Alkairi ba ne, aka fitar miki da mummunan halinsa da irin zaman da zaku yi bayan ya aureki, amma kuma ke baki gane ba.

Da yawa mutane suna Addu'ah Allah yana karɓa musu yana zaɓa musu Alkairi amma basa ganewa. Sai dai kuma ban sani ba ko kina ganin kamar idan bai aureki ba, ba za ki sami mijin aure ba, Wannna kuma wani abu ne na daban. Allah ya sa mu dace. 🤲

WALLAHU A'ALAM

Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance Damu. . .

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://whatsapp. com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www. facebook. com/groups/336629807654177

𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

https://t. me/TambayoyiDaAmsoshi

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam

Post a Comment

0 Comments