Ticker

6/recent/ticker-posts

Ikon Allah

Rana da ta ke da zafi,
Zafin da ya ke da ƙuna,
A birnin duniyarta,
Wa ye Ke sansayayata.

Ta haskaka duniyarmu,
Ba ta ƙone gonakinmu,
Ko tai illa gare mu,
Ban da Jalla Ubangijina?

Lokutan ɗari da zafi,
Damina bazara da girbi,
Na baran bara waccan,
Na yanzu da gobe jibi.

Wa ye Ke sarrafa su,
Ban da Haliƙu Al-Azizu,
Ikon Allah a kullum,
Ke sanya wata da zara.

Su haska dare a daji,
In da ba kyandir da sola.
Ƙorama kogi da teku,
Ruwansu dabam - daban ne.

Rijiyoyi ma yawansu,
Ɗanɗano na ruwan cikinsu,
Haske launinsu lura,
Kan sha bambam da juna.

Ruwa da baƙi da ja ma,
Da mai haske fari fes,
Ban da Allah zo faɗa min,
Mai ikon tsara komai?

Duwatsu tsaunika ma,
Launika da tsayi da ƙarfi,
Wasu masu aman wuta ne,
Wasu ko haƙuri gare su.

Ba sa illa ga kowa,
Koguna ne ma.cikinsu,
Wani dutsen ko na gwal ne,
Wasu ko ƙarfen tama ne.

A duwatsu ga tagulla,
Azurfa ga gilashi,
Akwai dutse na kwalli,
Da nau'o'in na kanwa.

Launika na ƙasa da yashi,
Marmara da taɓo da laka,
Wa Ke azurta bayi,
Da su baki ɗayansu?

Ikon Allah ka sanya,
Bishiyoyi can a daji,
Su tsuro da yawa su yaɗu,
Da yawansu suna da 'ya'ya.

Wasu 'ya'ya na da zaƙi,
Wasu ko bauri gare su,
Suna maganta cuta,
Ga dabbobi mutane.

Ikon Allah a fili, 
Na zana mai idanu,
Mai imani ya gansu,
Na miƙa wuya ga Allah.

Ni Khalid ban da ja ni,
Cewa Allah Ta'ala,
IkonSa akwai a teku,
Ya nashe duniya duk.

Imam baban Jamilu,
Ɗa ga Maryamu 'ya ta Hauwa,
Jika na Abubakar ne,
A Kano aka haifi Khalid.

Malam Khalid Imam
08027796140
khalidimam2002@gmail.com

Post a Comment

0 Comments