Waƙar Juyin Mulkin Nijer

    1. Salamun a kan wanga sako na kaya,

    Da ni Muda an dakara min a baya,

    Na zancen kawayen da ke yin hamayya,

    Makwaftan ga Nijar da Najeriya.

     

    2. Tasha ta ta Sunna ta sa nai rubutu,

    Na nusar da 'yan al'umata batattu,

    Gudun kar a maishe da bayi matattu,

    Musulmai mazauna na jamhuriya.

     

    3. Akan wanga zance na juyi na mulki,

    Da ke so ya jawo dalili na yaki,

    Tsakanin masoya mazauna na yanki,

    Aminanga Nijar da Najeriya.

     

    4. Ina wanda ke ji da kunnen basira,

    Matso duk bayanin da zan yo ka tara,

    Alakar da tsantsar abota ta haura,

    Tsakaninmu tilas zaman lafiya.

     

    5. Da Nijar da Najeriya ai guda ne,

    Kawai ‘yan’uwa ne da yayu da kanne,

    Alakar mahaifa da nonon uwa ne,

    Uban ma guda ne cikin nahiya.

     

    6. Da yarenmu tilo muke kasuwanci,

    Wajen cinikayya da hirar zumunci,

    Da zakinsa yayyenmu ke yin zawarci,

    Abin kayatarwa cikin kwalliya.

     

    7. Dalilin hakan ne muke auratayya,

    Tsakanin surukkai ko sam ba hamayya,

    Ga mai son mu yo hargitsi ya ji kunya,

    Ba zai nassara ba a nan duniya.

     

    8. Da Nijar da Najeriya babu bare,

    Bakake a fata muna nan a tare,

    Mu kyale bayanin wadancan farare,

    Na yankin kasa ko batun nahiya.

     

    9. Kamar yadda su basu son mu bakake,

    Hadin kanmu ma dole zai sa su yake,

    Dalilin ko in mun hade za mu mike,

    Mu zamto kamar tsintsiya bai daya.

     

    10. Tufafinmu na lura shi ma guda ne,

    Abincinmu ya shafi dangin tuwo ne,

    Matsa gefe can mai fadin wane-wane,

    Halin nan hali ne abin kushiya.

     

    11. Ku ban kunnuwa kunga Nijar kasata,

    Da Najeriya gun bison cibiyata,

    Musulminmu Allahu Yai mana gata,

    Zama tare sai an rike yafiya.

     

    12. Musulmi yaso duk musulmi na gaske,

    Batun bangaranci ya bar tanke-tanke,

    Mu tattaru domin mu tayar da garke,

    Mu zam masu iko cikin duniya.

     

    13. Idan da ace za ku dau shawarata,

    Da Nijar da Najeriya har makota,

    A koma guda dai ƙasa mai nagarta,

    Kamar yadda Turai suke tutiya.

     

    14. Kasashe da dama akai harhadawa,

    Sukai yo Amerika domin kwarewa,

    A yau kunga ikonsu yai tsallakawa,

    Siyasarsu ta mamaye duniya.

     

    15. Idan zamu gane mu dau namu yare,

    Mu maishe shi harshen kasashenmu dore,

    A ofis cikin mankarantu wurare,

    Mu watsar da yare na hauragiya.

     

    16. Farance da Turanci waye ya samu?

    Kayo naka nai nawa shi ke raba mu,

    Idan da suna so mu amfani kanmu,

    Baza ma a faro ba wannan tsiya.

     

    17. Iyayen kwarai basu cuta a kan mu,

    Faransa da Ingila ku ne idon mu,

    Idan ma akwai mai nufin kuntata mu,

    Da karfinku ku sai ku mai tankiya.

     

    18. A hannunku ne ma lagon ‘yan Afirka,

    Idan kunka so sai kasa tai yi mika,

    Idan kunka ce a a ko babu shakka,

     Akwai damuwa ba zaman lafiya.

     

    19. Ku yarje mu zauna kalau mu dukanmu,

    Mu more ku more cikin arzikinmu,

    Idan kunki to Rabbana ya ishema,

     A da ma da shi mu muke fariya.

     

    20. Aboki taho gani zo rungume ni,

    Ka dube ni dube ka mun yo kamanni,

    Ku dan tausaya kanmu ku shugabanni,

    Ku yarje mu zauna zaman lafiya.

    By:

    Mahmud Ahmad Musa (Mahmudul Khalam) +234 902 019 4569

    No comments:

    Post a Comment

    ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

    HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.