Takarda da aka gabatar a taron ƙara wa juna ilimi na ɗalibai masu karatun Digiri na Uku (PhD) a Sashen Harsunan Nijeriya, Jami’ar Usmanu Ɗanfodiyo, Sakkwato, Satumba, 04-09, 2023.
UMAR MUHAMMAD
+234 806 057 0930
Tsakure
Maƙasudin rubuta wannan
takarda shi ne gano irin wainar da ake toyawa a kan tasirin addinin Musulunci
kan sunayen Hausawa na gargajiya, kasancewar addinin Musulunci ya ratsa
dukkanin ɗangarorin rayuwar ɗan Adam baki ɗaya. Domin cimma
nasarar wannan takarda, bayan gabatarwa an yi ƙoƙarin gano su wane ne
Hausawa? Kuma a ina suka fito? Sai kuma mu ɗan yi ratse game da ma’anar addini da sunayen
Hausawa na gargajiya na Bahaushe da kuma bayani kan addinin Musulunci, uwa-uba
sai bakandamiyar aiki da ke nuna tasirin addinin Musulunci ga sunayen Hausawa
na gargajiya kuma da ita ce aka naɗe wannan aikin.
1.0 Gabatarwa
Kasancewar addinin
Musulunci shi ne addini na Allah Maɗaukakin Sarki mai kowa da komai da ya aiko
Annabin rahama. Annabi Muhammad (S.A.W.) da shi ga dukkanin al’ummun duniya
baki ɗaya domin ya zama
shiryarwa ga mutane bisa ga kyakkyawar hanyar bauta masa da gaskiya.
Bisa ga wannan haƙƙin ne al’ummar
Hausawa suka rungumi kiran nasa sau da ƙafa har ya yi tasiri
ta kowace irin rayuwa ta Bahaushe, kamar yadda ya yi tasiri ga sauran al’umma
baki ɗaya.
Bisa wannan dalilin
ne wannan bincike zai mai da hankali kan tasirin addinin Musulunci a kan
sunayen Hausawa na gargajiya ta yadda wannan tasirin na addinin Musulunci ya
fitowa Bahaushe da sunaye kyawawa nagartattu da suka ƙara fitowa da ƙima da darajar
Bahaushe a matsayin mai addinin da Allah ya aiko Manzonsa Annabi Muhammad
(S.A.W.) don musanya Bahaushe da sunansa na ƙwarai “Bahaushe” ba
“Bamaguje” ba.
2.0 Ƙasar Hausa Cikin Tarihi A Taƙaice
Masana da manazarta
sun tofa albarkacin bakinsu dangane da muhallin da ake kira ƙasar Hausa, amma zan
taƙaita
kan wasu daga cikinsu.
Habib da wasu (1980:iv)
sun ruwaito Adamu ya ce, ƙasar Hausa ta asali ta faro ne daga Lalle Asadu can
Arewa-maso-Gabas da Agadas daga nan ne Gobirawa suka taso da kaɗan-kaɗan har suka iso inda
suke a yau Nijeriya, a yanzu kuma Hausa tana yaɗuwa ne tana ƙoƙarin komawa har zuwa
gidanta na jiya. Ƙarshen iyakar ƙasar Hausa a Kudu shi
ne Yauri da Zaria da inda Bauchi ta yi iyaka da Kano.
Garun Gabas (wato
Birom) ita ce iyakar ƙasar Hausa daga Gabas. A Yamma kuma Filinge, ya kuma ƙara da cewa, ƙasar Hausa ita ce
inda ba a buƙatar naɗa Sarkin Hausawa. Wato, wannan bayani ya ware duk wasu
zango-zango inda ake Magana da Hausa. Dangane da yanayin ƙasar Hausa kuwa,
galibinta shimfiɗaɗɗiya ce, mai yawan
sarari, akwai ta da tsaunuka da tuddai jifa-jifa kuma duk yawan wannan ƙasa manyan koguna
biyu suka ratsa a cikinta da Kogin Rima da Kogin Haɗeja, Kogin Kwara ya
zama kamar iyaka daga Yammacin ƙasa, Kogin Rima shi ne ya ratso daga ƙasar Zamfara ya
gangara ya yi Arewa zuwa Nijar sannan ya karkata Kudu ya bi ta Yamma da
Sakkwato ya je ya faɗa cikin Kogin Kwara.
Shi ma Kogin Haɗeja ya fara ne a ƙasar kano daga nan ya
gangara Gabas ya bi ta Gashuwa da Gaidam
ya je ya haɗe a Tafkin Chadi. Ƙasar Hausa tana da
dazuzzuka iri biyu Sahel daga ɗangaren Arewa, sai kuma Kudu akwai dajin Sabana. Haka
kuma, yanayin shekara a ƙasar iri biyu ne lokacin damina da rani, wato hunturu da
zafi.
2.1 Su Wane
Ne Hausawa?
Masana ilimin
kimiyyar harshe da tarihi da adabi da al’ada sun tofa albarkacin bakinsu kan
asalin su wane ne Hausawa?
A ra’ayin wani
masani, ya bayyana cewa Hausawa su ne waɗanda suke zaune a ƙasar Hausa tuntuni,
kuma suna magana da harshen Hausa a matsayin harshen uwa (Ibrahim, 1992:2).
Wani masani kuma yana ganin Hausawa sun haɗa da mutanen nan waɗanda saboda ƙaura da magabatansu
suka yi daga ƙasar Hausa zuwa wasu sassa da ke maƙwabtaka ta kusa ko ta
nesa da ƙasar Hausa, ko da kuwa ba sa magana da harshen Hausa ko
yin al’adu ko abubuwan Hausawa, sun ɗauke su Hausawa ne. Misali: Abakwariga da
kuma wasu waɗanda suke iƙirarin su Hausawa ne
da suke zaune shekaru da daɗewa da suka gabata a ƙasashen Cote de Voire
da Burkina Fasa da Mali (Adamu, 1978:3).
Akwai kuma waɗanda saboda zama
cikin ƙasar Hausa sun manta da harshensu da al’adunsu na asali,
sun ɗauki na Hausa a taƙaice. Sun koma
Hausawa a harshe da al’ada da adabi. Misali: Kambarin Barebari da Barebarin
Katsina da Buzaye (Sallau, 2007:71).
Magaji (1986:33) ya
bayyana Hausawa don su ne mutane waɗanda harshensu shi ne Hausa, sannan dukkan
al’adunsu da tadodinsu na Hausawa ne. haka kuma, addinin Musulunci ya yi
cikakken tasiri a kansu. Hausawa dai su ne mazauna ƙasar Hausa tun asali,
masu Magana da harshen Hausa, kuma ba su da wani harshe in ba Hausa ba. Idan
suka saɗa haka, to barbarar
yanyawa ne. (Bunza, 1990:12).
A nawa ra’ayi,
Hausawa su ne waɗanda Hausa ita ce
harshensu na asali, ba su da wata ƙasa in ba ƙasar Hausa ba.
3.0 Ma’anar Addini
Safana (2010) ya
fassara addini da cewa hanyar bautawa wani abu wanda mutum yake tsammani shi ne
zai biya masa buƙatun rayuwar yau da kullum. Addinin farko da mutanen ƙasar Hausa shi ne
addinin gargajiya, wato tsafi, ta hanyar bautar Iskoki ko mutanen ɗoye sai kuma
takwarorinsa Bori da camfi. Irin wannan addini ya faru ne ta bin wasu hanyoyi
da mutane suka ƙago wa kansu na bautar waɗansu abubuwa don cimma biyan buƙatunsu na rayuwa.
Wannan hanyar bauta, ta daɗe ƙwarai da gaske a duk sassan duniya ba ƙasar Hausa kawai ba,
har ma da sauran ƙasashen duniya baki ɗaya. (Safana, 2010).
3.1 Addinin
Hausawa Na Gargajiya Kafin Zuwan Musulunci Ƙasar Hausa
Mafarin addinin
gargajiya shi ne bautar gumaka, wato addinin gargajiya ya wanzu ne ta bin wasu
hanyoyi da mutane suka ƙago wa kansu ta bautar waɗansu abubuwa don cimma biyan buƙatunsu. Irin wannan
hanyar bauta ta daɗe ƙwarai a duniya.
Mutane da suka fara zama a duniya su suka ƙago ta, daga nan kuma
abin ya zama al’ada ga sauran ƙabilun da suka biyo bayansu. Da haka
abin yana tafiya har ya zo kan Hausawa. Sai dai irin wannan addinin yawanci
idan Allah Maɗaukakin Sarki ya aiko
wani Annabinsa zuwa ga ƙabilar da aka aiko shi, bayan an sha gwagwarmaya, sai ka
ga ya yi sauƙi, amma da wuya a bar shi gaba ɗaya ba tare da
tasirinsa ya dinga bin wannan ƙabilar ba (Muhammad, 1982).
Al’ummar Hausawa na
addininsu na gargajiya ne ta hanyoyi guda uku, tsafi, bori, camfi. Amma tsafi
shi ne babban jigo kuma yana cikin hanyoyin bauta a cikin addinin gargajiya na
Hausawa. Sai dai irin wannan bauta ba wani gunki ake sassaƙawa ana bauta masa
ba. Amma da yake yanzu yawancin Hausawa duk sun shiga cikin addinin Musulunci,
rayuwar waɗanda ba su shiga ba
su ake kira Maguzawa, kuma su ne har yanzu suke bin wannan addini. Ta hanyar
tsafi Maguzawa sukan bauta wa wani aljani, wanda yawanci sukan ce yana zaune a
kan wani dutse ko a kogon wata bishiya, tsamiya ko kuka. Haka kuma, kowane
tsafi a kan sami wani mutum wanda yakan zama mai kula da shi. A taƙaice dai, addinin
gargajiya kafin shigowar Musulunci shi ne ya shafi tsafi, bori da kuma camfi
(Muhammad, 1982).
3.2 Sunayen Hausawa Na Gargajiya Kafin
Zuwan Musulunci
Wannan ɗangaren zan ɗan waiga baya ne
kawai mu ga sunayen Hausawa na gargajiya a al’adar Bahaushe kafin zuwan
Musulunci. Hausawa a gargajiyance, yawanci sukan dubi lokacin da aka yi haihuwa
ko halin da aka yi haihuwa ko yanayi su samo sunan, daga nan su sanya wa abin
haihuwa.
Haka kuma, yawancin
Hausawa sukan sami sunaye iri biyu: sunan yanka da na kakanni, amma kusan
dukkaninsu iri ɗaya ne kuma ta hanya ɗaya ake samunsu. Ga
kaɗan daga cikin sunayen
Hausawa (Maguzawa) kamar haka:
1. Sammako – yaron da
aka haifa da sassafe
2. Ranau – yaron da aka
haifa da rana idan mace ce ta-rana
3. Na-hantsi – yaron da
aka haifa da hantsi
4. Dare ko Ɗandare – yaron da aka
haifa da dare
5. Shuka/Shukkau – yaron
da aka haifa lokacin shuka
6. Nomau – yaron da aka
haifa ana noma
7. Damina/Damana – yaron
da aka haifa da damina
8. Malka – yaron da aka
haifa lokacin tsululin ruwa
9. Anaruwa – yaron da
aka haifa lokacin tsululin ruwa
10. Ci-gero/Maigero – yaron da aka haifa lokacin
cin sabon gero
11. Ci-wake/Roro – yaron da aka haifa lokacin cin
wake
12. Ƙosau – yaron da aka
haifa lokacin ƙoshi
13. Wadata – yaron da aka haifa lokacin wadata
14. Ɗari/Taɗari – yaro ko yarinyar
da aka haifa lokacin ɗari
15. Kaka/Ɗankaka – yaron da aka
haifa lokacin kaka
16. Maidamma – yaron da aka haifa ana ɗaura damman hatsi
17. Ajuji/Ayas/Ayashe – yaro ko yarinyar da aka
haifa bayan an yi ta haihuwa suna mutuwa (ana wabi).
18. Mairiga – yarinyar da aka haifa da rigar
haihuwa (ta fito cikin yanar rigar haihuwa).
19. Shekarau – yaron da ya shekara a cikin ciki
20. Tanko/Namata/Mati – yaron da aka haifa bayan
haihuwar mata
21. Magawata – yaron da aka haifa bayan wata ya
tsaya
22. Gagarau – yaron da aka haifa bayan an yi ƙoƙarin zubar da cikinsa
abu ya gagara.
23. Mantau – yaron da ya daɗe a ciki kafin a
haife shi
24. Cindo//Mai Cindo – yaron da aka haifa da yatsu
shida
25. Cibi/Maicibi – yaron da aka haifa da cibi
26. Kanta – yaron da aka haifa tare da mace
27. Auta – yaro ko yarinyar da aka haifa a ƙarshen haihuwa
28. Maigiya – yaro ko yarinyar da aka haifa ana
dafa giya
29. Malka – yarinyar da
aka ana tsuga ruwa
30. Kande/Dela/Deluwa/Barauki/Ige – yarinyar da
aka haifa bayan an haifi maza da yawa.
31. Kumatu – yarinyar da aka haifa da kaurin
kumatu
Kaɗan ke nan daga cikin sunayen Hausawa na gargajiya da suke ambaton ‘ya’yansu kafin Musulunci. Hausawa sun ci gaba da amfani da waɗannan sunaye ko bayan shigowar Musulunci domin kuwa kusan dukkanin sunayen ba su da wata alaƙa da Musulunci.
4.0 Addinin Musulunci
A wannan gaɗa, ya kamata a yi ɗan bayani a taƙaice dangane da
ma’anar Musulunci.
Gusau (1999: 1)
ya ce, “Addinin Musulunci shi ne addinin da Allah mai girma da ɗaukaka ya aiko Annabi
Muhammad tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, da shi domin ya shiryar
da mutane zuwa ga kyakkyawanr hanyar bauta Masa. Da wannan, mun tabbatar cewa
shi Musulunci addini ne da ya zo daga Allah kuma ya wanzu ta hanyar Annabi
Muhammad (S.A.W.). Haka kuma, shi addini bai nuna wata wariya a cikin al’umma
ba, wai ko don kana shugaba, amma ya yi tanadi a yi wa shugaba ɗa’a gwargwadon hali,
in dai bai kauce wa shari’ar Musulunci
ba.
Gusau (1991:2) ya ƙara da cewa Musulunci
shi ne gaskatawa da miƙa wuya zuwa ga abin da Manzon Allah (S.A.W.) ya zo da shi
daga wurin Allah Subhanahu wata ala,
sannan da aiki da shi.
4.1 Tasirin
Addinin Musulunci Ga Sunayen Hausawa Na Gargajiya
Kafin mu tsunduma ga
wannan bakandamiyar aiki wato tasirin addinin Musulunci ga sunayen Hausawa na
gargajiya, kamata ya yi mu san kalmar ‘tasiri’ ita kanta.
Tahar (1990) ya
bayyana tasiri da cewa karɗuwa da amincewa kuma da mamaye kowace irin harka da ta
shafi rayuwar wasu jama’a, Wasagu (2002) ya fassara kalmar tasiri da nufin
sauyin da ake samu a cikin wani abu dalilin wani abu.
Bayan addinin Musulunci
ya shigo ƙasar Hausa ya yi ƙarfi da tasiri ga
kowane ɗangaren rayuwar
Bahaushe, sai ya zama sunayen da Bahaushe yake amfani da su a gargajiyance idan
an yi masa haihuwa suka ƙara yawa, har suka sauya zuwa ga sunayen Musulunci.
Ga dai sunayen manyan
bayin Allah kamar Annabawa da Sahabbai da mutanen kirki (waliyyai) da ma
matansu da na ‘ya’yansu. Ga kuma sunayen Mala’iku da suke sa wa yaransu. Duk waɗannan sunayen suna sa
musu ne don neman albarka. Ban da waɗannan kuma, Hausawa sun ci gaba da amfani da
sunayen gargajiya irin na asali don yi wa yaro laƙabi. Wato, a taƙaice dai, idan an
haifi yaro a ranar suna za a sa masa suna wanda zai zama ko sunan Annabi ko na
Sahabi ko na mutanen kirki (waliyyai) ko na Mala’iku ko kuma in mace ce, a sanya mata sunan matar wani Annabi
ko ‘yarsa ko matar Sahabi ko ‘yarsa, to bayan wannan suna kuma, sai a sami
sunan gargajiya wanda yawanci kakanni ko waɗanda ba za
su faɗi sunan ba, saboda kunya irin ta al’adar Hausawa
za su sa wa yaro ko yarinya shi. Ga misalan sunayen yanka na Hausawa kamar
haka:
Muhammadu, amma
saboda suna son sunansa da yawa, mutum ɗaya yakan iya sa wa ‘ya’yansa maza goma (10)
duk sunan “Muhammadu” sai dai zai bambanta a cikin Larabci ya ce Muhammadu na ɗaya ko na biyu ko na
uku har zuwa na goma (10). Misali:
1. Muhammadu Auwalu
2. Muhammadu Sani
3. Muhammadu Salisu
4. Muhammadu Rabi’u
5. Muhammadu Hamisu
6. Muhammadu Sadisu
7. Muhammadu Sabi’u
8. Muhammadu Saminu
9. Muhammadu Tasi’u
10. Muhammadu Ashiru
Sauran sunayen
Annabawa da Hausawa kan sa wa ‘ya’yansu su ne:
1. Adamu
2. Nuhu
3. Idrisu
4. Salihu
5. Hudu
6. Ibrahim
7. Yakubu
8. Isma’ila
9. Yusuf
10. Yusha’u
11. Iliyasu
12. Yahaya
13. Zakariya’u
14. Dawuda
15. Suleiman
16. Musa
17. Isa da sauransu.
Sannan
sukan sanya sunayen Sahabbai kamar:
1. Abubakar
2. Umaru
3. Usmanu
4. Aliyu
5. Abbas
6. Zubairu
7. Sa’adu
8. Abdullahi
9. Abdurarrahman da
sauransu.
A cikin sunayen
Waliyyai kuma, sun fi sa sunayen:
1. Abdulƙadir
2. Ahmadu Tijjani (ruwayar
‘yan ɗariƙa ce)
3. Ahmadu Rufa’i
4. Usmanu da sauransu.
A cikin mata kuma,
sukan sa:
1. Aminatu
2. Faɗimatu
3. Maryamu
4. Ummul Kulsumi
5. Zainabu
6. Ruƙayyatu
7. Hindu
8. Hindatu
9. Habibatu
10. Maimunatu
11. Halimatu da sauransu.
A cikin
Mala’iku kuma sukan sa:
1. Jibrilu
2. Mika’ilu
3. Ridwanu
4. Maliki
Daga cikin waɗannan sunaye akwai waɗanda Hausawa suke faɗarsu daidai, kamar
yadda suke a cikin littafi, akwai kuma waɗanda suke jirkitawa. Misalin waɗanda suke faɗa daidai su ne:
1. Hudu
2. Nuhu
3. Musa
4. Isah
5. Hindu
6. Asama’u
Misalin sunayen da
suke jirkitawa su ne:
1. Adamu – Ado
2. Idrisu – idi
3. Salihu – Sale
4. Ibrahim – Iro, Ibran,
Buraima, Ibro, Ibra
5. Zakariya’u – Zakari,
Ya’u
6. Abubakar – Abu, Habu
7. Abdullahi – Audu,
Abdu
Abdurrahman da
sauransu
8. Zainabu – Abu
9. Hadijatu – Dije,
Dija, Dijama
10. Maimunatu – Maimuna, Munari, Muna
11. Rukayya – Rakiya, Ruke
Haka
kuma har wa yau, bayan zuwan Musulnci, an sami sunayen da ake sa wa ‘yan
tagwaye (’yan biyu) kamar haka:
Al-Hassan – Na
littafi
Alasan – sunan ɗan tagwayen da aka fara haihuwa namiji
Hassan – yadda
Hausawa kan faɗa
Al-Hussaini – na
littafi
Usaifi – na Hausa
Alhassanatu – na
littafi
Hasana – na Hausa
Alhasanatu – na littafi
Usaina – ‘yar
tagwayen da aka haifa daga ɗangaren mace.
Dangane da sunayen
gargajiya kuma Hausawa sun ci gaba da amfani da sunaye na da, amma ban da
irinsu Maigiya da Shagiya da Ramau da Taroro, waɗannan sai Maguzawa kawai suke amfani
da su. Haka kuma, Musulunci ya sa Hausawa sun ƙara ƙago waɗansu sababbin sunaye
irin na gargajiya. Ga misalin irin sunayen da Hausawa suke amfani da su bayan
Musulunci a matsayin sunayen kakanni, ko sunayen rana kamar haka:
1. Dogara (Na dogara ga
Allah)
2. Alabura (Allah ya
bari)
3. Nabara (Na bar wa
Allah)
4. Dangana (Na dangana
ga Allah)
5. Bawa (Bawan Allah)
6. Barmini (Allah ya bar
mini)
Sunayen yara maza da
aka haifa bayan an yi ta haihuwa suna mutuwa (‘yan wabi).
1. Sadau – yaron ko yarinya da aka haifa bayan mace
ta koma ɗakin mijinta.
2. Sodangi – Yaro ko
yarinyar da aka haifa bayan iyayensa sun dawo cikin dangi, ko a lokacin da
dangi suka taru don yin wani sha’ani.
3. Korau – yaron da aka sa wa sunan wani mutum, amma
ba a daɗe ba sai mutumin ya
mutu.
4. Wada/Dawada/Maiwada/Ɗanyalwa – yaron da
aka haife shi lokacin wadata ko kuma wanda iyayensa suka sami wadata bayan
haihuwarsa.
5. Tawada/Yalwa/goshi –
yarinyar da aka haifa lokacin wadata ko kuma aka sami wadata bayan haihuwarta.
6. Maikuɗi – yaro ko yarinyar
da iyaye suka sami kuɗi ranar haihuwarta,
ko kuma waɗanda aka haifa ranar
Talata.
7. Sallau/Nasalla/Maisalla/Tasalla/Tasalluwa
– yarinya ko yaron da aka haifa lokacin salla.
8. Labaran/Ɗanazumi/Azumi –
yarinyar da aka haifa a watan azumin watan Ramalana.
9. Ladan/Maisalla/Mai
salati – yaron da aka haifa lokacin da ladan yake kiran salla.
10. Gambo – yaro ko yarinyar da aka haifa bayan
haihuwar ‘yan tagwaye.
11. Kadarko – yaro ko yarinyar da aka haifa a
tsakanin haihuwar ‘yan tagwaye.
12. Gwamma (Gwamma ita da babu) Hakama (Haka ma
ina so) – yarinyar da aka haifa bayan an sa ran haihuwar namiji.
13. Bakuso – yaro ko yarinyar da aka haifa bayan an saki
uwarsa ko uwarta.
14. Yawale – yaron da aka
haifa a hanyar zuwa Makka.
15. Yabi – yarinyar da aka haifa a hanyar zuwa
Makka.
16. Talle – (Tallafin marayun Allah) – yaro ko
yarinyar da uwarsa ta mutu a wurin haihuwarsa ko bayan haihuwarsa kaɗan.
17. Alhaji/Baita – yaron da aka haife shi a
lokacin shagalin salla babba.
18. Hajiya/Kyauta (kyautar Allah) – yaro ko
yarinyar da aka haifa bayan uwarsa ko ubansa sun fitar da rai da samun haihuwa.
19. Tunau/Ɗantune – yaron da aka
haifa bayan uwarsa ko ubansa sun fitar da rai za su kuma samu haihuwa.
20. Tune – yarinyar da aka haifa bayan uwarsa ko
ubanta sun fitar da rai za su kuma samun haihuwa.
21. Makwashi – yaron da bora ta haifa.
22. Kilishi – yaro ko yarinyar da aka haifa bayan
an ci sarauta.
23. Dawai – yaron da aka haifa bayan kome (mace ta
dawo ɗakin mijinta).
24. Dawo – yarinyar da aka haifa bayan kome.
25. Sharubutu – yaro ko yarinyar da uwarsa ta sha
rubutu da yawa kafin ta haife shi.
26. Sutura/Mairiga – yarinyar da aka haifa da
rigar haihuwa.
Sunayen Ranakun Mako
Kafin zuwan Musulunci
kusan in ban da su “yau, gobe, jibi, citta, jiya da shekaranjiya Hausawa basu
da sunayen ranaku, sai dai su kira kowace rana da sunan garin da kasuwarsa take
ci a wannan rana. Misali, ranar Ɗanbatta, ranar
Ma’aduwa, ranar Bakori, ranar Maƙarfi da sauransu. Da Musulunci
ya zo, sai ya kawo musu sunayen ranakun mako kamar:
1. Assibit – Asabar
2. Al-Ahd – Lahadi
3. Al-thnain – Litinin
4. Al-thulatha’a –
Talata
5. Al-Arba’a – Laraba
6. Al-Khamis –
Alhamis
7. Al-juma’at – Juma’a
Daga waɗannan sunaye ne
Hausawa suka ƙago sunayen da za su sa wa yaron da aka haifa a waɗannan ranaku kamar
haka:
1. Ɗanasabe/Ɗan’asibi – yaron da
aka haifa ranar Asabar.
2. Ɗanladi/Lado/Nalado –
sunayen yara maza da aka haifa ranar Lahadi.
3. Ladi/Ladidi/Ladingo/Ladigo
– sunayen yara mata da aka haifa ranar Lahadi.
4. Ɗanliti/Ɗantani/Liti – sunayen
yara maza da aka haifa ranar Linitin.
5. Tanin/Liti – sunayen
yara mata da aka haifa ranar Linitin.
6. Ɗantala/Ɗantata/tatu/Maitala/Maitalata
– sunayen yara maza da aka haifa ranar Talata.
7. Talatuwa/Talatu/Tatu/Lantu
– sunayen yara mata da aka haifa ranar Talata.
8. Bala/Balarabe/Ɗanbala/Ɗanlarai – sunayen
yara maza da aka haifa ranar Laraba.
9. Larai/Balaraba/Laraba/Balarabiya/Tabawa
– sunayen yara mata da aka haifa ranar Laraba.
10. Ɗanlami/Na Lami –
sunayen yara maza da aka haifa ranar Alhamis.
11. Lami/Laminde/Lamisuwa
– sunayen yara mata da aka haifa ranar Alhamis.
12. Jume/Jumare/Wajume/Ɗanjuma/Ɗanjimmai/Na-Jimmai –
sunayen yara maza da aka haifa ranar Jumu’a.
13. Juma/Jummai/Aljumma – sunayen yara mata da aka
haifa ranar Jumu’a.
Gwargwadon
hali, waɗannan su ne misalan
sunayen da ake kiran Hausawa da su bayan shigowar addinin Musulunci ƙasar Hausa da suka
danganci ranakun mako.
5.0 Naɗewa
Tun kafin bayyanar
addinin Musulunci a ƙasar Hausa. Al’ummar Hausawa suna da sunayen da suke
sanyawa ‘ya’yansu ta hanyar dubin lokaci da yanayi ko halin da aka yi haihuwar
ko dai wani dalili na daban, su sanya wa abin haihuwar suna. Da addinin
Musulunci ya shigo ƙasar Hausa, sai ya sauya waɗannan sunayen na Maguzanci zuwa na
Musulunci ta hanyar inganta su da ƙara masu yawa kan
tsarin koyarwarsa. Kan haka, wannan bincike mai taken “Tasirin Addinin Musulunci
Kan Sunayen Hausawa na Gargajiya” ya cimma burinsa gwargwado, ya yi ƙoƙarin sanin al’ummar
Hausawa da ƙasarsu, sai kuma taƙaita bayani kan
addinin Hausawa na gargajiya, da na Musulunci da kuma kawo sunayen Hausawa na
gargajiya gwargwadon hali. Sai kuma uwa-uba hasashen aikin da ya shafi tasirin
addinin Musulunci kan sunayen Hausawa na gargajiya inda binciken ya zayyana su
dalla-dalla tare da misalai ingantattu.
Sakamakon Bincike
Bayan gabatar da ƙumshiyar wannan
bincike a taƙaice, ba zan naɗe wannan ‘yar takarda ba, sai na ɗan yi tsokaci kan
wasu abubuwa da wannan binciken ya gano kamar haka:
1. Binciken ya yi ƙoƙarin gano tasirin
addinin Musulunci kan sunayen Hausawa na gargajiya ta fuskoki da dama.
2. Binciken ya kuma yi ƙoƙarin gano dangantakar
al’ummar Hausawa da Larabawa da ma sauran maƙwabta malamai wanda
dalilin su ne Bahaushe ya karɗi Musulunci har ya sauya suna daga “Bamaguje” zuwa
“Bahaushe”.
3. Haka kuma, dalilin
addinin Musulunci ya sauya sunayen Bahaushe na haihuwa ta la’akari da lokaci da
yanayi da rana, ya ba shi sunayen Musulunci ta ɗangarori daban-daban.
4. Binciken ya waiwayi
sunayen Bahaushe na gargajiya ya kwatanta su da na shi, ya ɗebe tsaki da tsakuwa
ya fitar da gari don ya gyara wasu sunaye ya daidaita su da na shi, ya zubar da
na zubar wa irin sunan “Shagiya” da “Kumatu” da sauransu.
Manazarta
Alti,
K.M. (2012). “Wasu Dabarun Gargajiya na Kawar da Talauci A Birnin Katsina.
Kundin Digiri na Biyu (M.A. Hausa). Sashen Nazarin Harsunan Nijeriya, Sakkwato:
Jami’ar Usmanu Ɗanfodiyo.
Amfani,
A.H. (2011). “Hausa da Hausawa da Kuma Ƙasar Hausa Jiya Da
Yau”Takardar Da Aka Gabatar a Taron Ƙara wa Juna Sani,
Assembly Hall Ahmadu Bello University, Main Campus Zaria, Kaduna State.
Aliyu,
A.Y. (1973). “Asalin Hausa” A Cikin
Littafin Makon Hausa. Kano: Jami’ar Bayero.
Augie,
A.R. Da Wasu (1991). Nazari
a Kan Tarihin Al’ummar Ƙasar Zuru Gabanin Kafa Mulkin Mallaka Na Turawa. Ƙungiyar Raya Ci Gaban
Ƙasar
Zuru (ZED).
Bunza,
A.M. (1990). “Hayaƙi Fidda Na Kogo: Nazarin Siddabaru Da Sihirin Hausawa”.
Kundin Digiri na Biyu (M.A. Hausa) Sashen Koyar da Harsunan Nijeriya.
Kano: Jami’ar Bayero.
Bunza,
A.M. (2008). “Gadon Feɗe Al’ada”. Jerin Littafan
Cibiyar Nazarin Al’adun Hausawa, Lagos: Tiwal.
Bunza,
A.M. (1995). “Magungunan Hausa a Rubuce: Nazarin Ayyukan Malamin Tsibbu”.
Kundin Digiri na Uku (Ph.D Hausa) Juzu’i na Ɗaya. Kano: Jami’ar
Bayero.
Gobir,
Y.A. (2002). “Iskoki a Idon ‘yan Bori da Masu Ruƙiyya”. Kundin Digiri
na Biyu (M.A.Hausa) Sashen Koyar da Harsunan Nijeriya. Sakkwato: Jami’ar Usmanu
Ɗanfodiyo.
Gobir,
Y.A. (2013). Tasirin Iskoki Ga Cutuka da Magungunan Hausawa. Kundin Digiri na
Uku (Ph.D Hausa) Sashen Koyar da Harsunan Nijeriya. Sakkwato: Jami’ar Usmanu Ɗanfodiyo.
Gobir,
Y.A. (2023). Laccar Kwas Hau: 933 Mai Taken. “Hausa Culture and Islam” Sashen
Koyar Da Harsunan Nijeriya. Sakkwato: Jami’ar Usmanu Ɗanfodiyo.
Ibrahim,
Y.Y. da Wasu (1986). “Jagoran Nazarin
Hausa”. Northern Nigeria Publishin Company Zaria.
Magaji,
A. (1989). “Gudummuwa a Kan Ƙoƙarin da Ake Yi Na Samar
Da Cikakken Tarihin Hausawa da Harshensu” Maƙala, Kano: Takardar
da Aka Gabatar a Sashen Koyar da Harsunan Nijeriya, Jami’ar Bayero.
Magaji,
A. (2002). “Wasu Al’adun Hausawa da Yanaye-Yanayensu a Ƙasar Hausa”. Kundin
Digiri na Uku (Ph.D Hausa) Tsangayar Fasaha da Addinin Musulunci. Kano: Jami’ar
Bayero.
Nafisa,
M.G. (2014). “Kutsen Baƙin Al’adu Cikin Hidimar Aure a Sakkwato” (M.A. Hausa)
Kundin Digri na Biyu. Sashen Koyar da Harsunan Nijeriya. Sakkwato: Jami’ar
Usmanu Ɗanfodiyo.
Sama’ila,
A.K. (2019). “Al’adun da Addinin Musulunci ya hana Aikatawa, Kuma Ake yi a Wasu
Masarautun Ƙasar Hausa”, Takardar da Aka Gabatar a Taron Ƙara wa Juna Sani,
Kwalejin Share Fage da Karatu Mai Zurfi Yelwa-Yauri.
Safana,
B.Y. (2001). Maguzawa Lezumawan (Babban kada) Gudummuwar Safana a Jihar
Katsina. Kundin Digiri na Farko (B.A. Hausa) Sashen Koyar Da Harsunan Nijeriya.
Sakkwato: Jami’ar Usmanu Ɗanfodiyo.
Sallau,
B.A.S. (2009). “Sana’ar Wanzanci da Sauye-Sauyen Zamani Jiya da Yau”. Kundin
Digiri na Uku (Ph.D Hausa) Sashen Harsunan Nijeriya. Kano: Jami’ar Bayero.
Tahar,
M.A. (1990). “Siddabaru a Ƙasar Hausa Yadda Yake da Yadda Ake Yin
Sa”. Kundin Digiri na Biyu. (M.A. Hausa). Sashen Koyar Da Harsunan Nijeriya. Kano:
Jami’ar Bayero.
Tukur,
A. (2015). “Sana’ar Saƙa a Ƙasar Hausa”. Kundin Digiri na Farko.
Sashen Harsunan Nijeriya. Kano: Jami’ar Bayero.
Umar, M. (2015). “Zumuntar Tsafe-Tsafen Hausawa da Dakarkari (M.A. Hausa). Sashen Harsunan Nijeriya. Sakkwato: Jami’ar Usmanu Ɗanfodiyo.
Umar,
M. (2017). “Tasirin Zuwan Turawa ƙasar Hausa”. Takardar
Da Aka Gabatar a Taron Ƙara wa Juna Ilimi. Kwalejin Share Fade Da Ilimi Mai Zurfi
Yelwa-Yauri.
Wushishi,
B.J. (1998). “Dangantakar Magani Da Wasu Sana’o’in Hausawa Na Gargajiya”.
Kundin Digiri na Biyu. Sashen Harsunan Nijeriya, Sakkwato: Jami’ar Usmanu Ɗanfodiyo.
Waziri,
M. (2013). “Tasirin Sarautun Hausawa a kan Ƙabilar Kare-Kare da
Sayawa”. Kundin Digiri na Biyu (M.A. Hausa). Sashen Koyar Da Harsunan Nijeriya,
Sakkwato: Jami’ar Usmanu Ɗanfodiyo.
Zaruma,
(1983). A Culture Magazine of Sokoto State.
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.