Ticker

6/recent/ticker-posts

Tsakure daga Wakar Camfi da Bori ta Alhaji Mudi Sipikin Kano

Akwai masu gasgata kayan da babu

Su sa musu suna su ambaci gaibu

In wai ka ce babu to ka yi aibu

Hakika shirinsu akwai ta'ajibu

Zan wo bayaninsu don ku jiya.


La'alla ƙarancin sani shi ya sanya

Suke aika wannan rashin gaskiya

Koko dai sun bi son zuciya

Suna ta ɓatar da mutan duniya

Dare du da rana zuwa safiya.


Shi ne nake so mu taru mu gane

Camfi da ƙage rashin ilimi ne

Tsafi su bori rashin hankali ne

Aminci da su kuwa hanyar ɓata ne

Da wauta da shirme da sharholiya.


Ku gane mutane fa ba wata Inna

Da ke shanye hannu, ƙafa, a ina?

Rashin lafiya ne kawai ku shina

Wajen likitoci akwai magana

Ku zan tambaya don sanin gaskiya 


Sa'an nan ku gane fa babu fatalwa 

Shirme kawai ne ku daina kulawa

Kar dai ku yadda da masu ɓatarwa

Su maishe ku bol duk suna ta bugawa

Ga ku da ranku cikin duniya.


Wallahi tallahi babu Nakada

Kar ma ku ce za ku nem wata shaida

Matsafa kawai ne suke farfaganda

Su ja hankalinku zuwa kasada

Su sa ku a hanyar rashin gaskiya.


Sun ce a bori akwai alhaji

Ya jama'a duk kuna nan kuna ji

Sun yi dabara su ɓata haji

Wallahi tallahi du kar ku ji

Karya suke muku bakidaya.

www.amsoshi.com

Daga:
Zauren Makaɗa da Mawaƙa

Post a Comment

0 Comments