Engineer Micheal Siervo, ya yi magana me kama hankali yana cewa "Waye Satoshi Nakamoto mutumin da ya yi Bitcoin kuma ya samar da Bitcoin Blockchain a 2008 wanda har yanzu duniya ta gagara fada da fasahar?", Me ya sa har yanzu duniya bata san hakikanin Satoshi Nakamoto ba?
* Engineer
Siervo ya yi zargi kuma yana fahimtar cewa Professor Nicolas Kakkolis na
jami'ar Stanford University dake United States of America shine asalin Satoshi
Nakamoto da ya yi Bitcoin da Bitcoin Blockchain, sai dai bai bayyana kansa ba sai
akan Pi Network.
Yana fahimtar cewa idan ba Nicolas Kakkolis ne Satoshi
Nakamoto ba toh tabbas ya yi farin sani wa Satoshi Nakamoto. Engineer Micheal
Siervo ya fitar da wasu abubuwa guda uku a matsayin dalilan da ya Gina zaton sa
akan su kamar haka:
1. Na farko, manyan 'daliban Nicolas Kakkolis da suka yi
nasara suka kafu a duniyar Blockchain guda uku, kafuwar da a zahiri ko shi
Nicolas bai yi ba:
~ Vitalik Buterin -
Mai Ethereum.
~ Changpen Zao (CZ) -
Mai Binance.
~ Brad Garlinghouse -
Mai XRP.
Engineer Micheal Siervo ya yi zargin cewa yaya aka yi
'daliban Nicolas Kakkolis suka yi zarra a duniya a cikin harkar shi bai yi ba?
Ya aka yi suka yarda da ilimin sa da Karatun sa, suka Gina manyan Blockchain da
Exchanges da ake ajiye Billions of Dollars, shin ya nuna musu wani aikin da ya
taba yi ne har suka yarda suka yi koyi da irin nasa?
* Idan ya
taba nuna musu toh wane aiki ya nuna musu idan ba Bitcoin da ya gabaci sauran
crypto projects ba?
2. Na biyu, Engineer Micheal Siervo, ya yi tambaya cewa, ya
aka yi Nicolas Kakkolis ne kadai yake koyar da Blockchain a 2013, Blockchains
da suke alaka da crypto currencies, a lokacin da babu wani mutum da ya bayyana
yana koyar da Blockchain a duniya?
* Idan ba
Nicolas ne Satoshi ba yaya aka yi a 2013 yake iya bayanin Lungu da sako na
Bitcoin Blockchain a lokacin da manyan Masana suke kokarin yaya za'a yi su
fahimci abun, a ina ya sani? waye ya koya masa, kuma dukkan videos da Nicolas
ya yi wadannan bayanan suna Nan har yanzu, inji Engineer Micheal Siervo.
3. Abu na uku:
Me ya sa duniya bata San Nicolas sosai ba sai akan Pi
Network? me ya sa Nicolas bai shahara da wani Blockchain ba sai Pi Network?
Sannan ka tambayi kanka, yaya aka yi su CZ da Vitalik suka
san Nicolas ya san Blockchain har suka yarda suka koyi ilimin Blockchain a
wajen sa, ya taba samar da Blockchain ne?
* Sai wata
tambayar da ni zan 'kara akai, wanda itama abar lura ce, itace:
Ko kasan Nicolas Kakkolis ne ya fara samar da Facebook Application
wa Kamfanin Facebook?
Nicolas ya samu Award na girmamawa daga Kamfanin Facebook a
2009, shekarar da duniya kaso 30 dinta bata san Facebook ba, saboda wasu
aiyukan da ya yi masu girma a duniyar fasahar Application, kamar irin aikin da
ya yi na Myspace da sama da mutum Miliyan 20 suka amfana dashi a shekaru biyu a
fadin duniya.
~ Ko babu komai zaka
fahimci zai wahala ace irin wannan mutum ya yi abinda shirme ne a ilimin sa da
duniya ta san shi akai.
It may be kai ka ga
abun kamar shirme musamman idan ba ka wani previous knowledge akan Blockchain
ko Web Application Technology.
* Daga
2018 zuwa yau shekaru biyar babu abinda Nicolas ya baiwa muhimmanci kamar aikin
Pi Network, kuma duk wani masanin technologyn Blockchain a duniya bai yi
gangancin sukan abun ba, saboda yasan waye yake behind the project. Ta yuwu
kaji wani ya soki Pi Network din, but ana maganar sukan masu ilimi akai ba
wadannan basu da shi ba.
Zaka iya tambayar kanka yaya aka yi Jami'ar Stanford da take
matsayi na biyu a duniyar technology ta yarda ta amince da koyar da daliban
University na bangaren Computer 🖥️ Wani course da Nicolas
ya kirkiro, har aka amince a saka Pi Network, theories and technology it
contains.
* Abu ne
me wahala ga wanda yake da ilimi a fagen ya bayyana Pi Network a matsayin
shirme ko wasa.
Lastly, zaka fahimci akwai wani abu me girma da zai zo ya
faru akan wannan abun na Pi Network kamar yadda Professor Mansur Isah Yelwa ya
bayyana kwanakin baya.
* Idan
kana da Pi Network ko kana Mining dinsa ka yi kokarin rike kayan ka, ka tara shi
ka Adana shi, kada ka saka ranka akan sa cewa zaka yi Kudi dashi, but kayi
haƙuri ka adana shi ka bayar da wani lokaci, ko a yanzu da Pi Network bai je
Mainnet ba, already ya zama Kudi, mutane suna siyar dashi, suna amfana...
Allah ya sa mu dace...
Daga
Pi Updates
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.