Gabatarwa:
"Haihuwa maganin
mutuwa, ba dan ke ba da iri ya ƙare"
Haihuwa ita ce mataki na biyu cikin matakan rayuwa na kowane abu mai rai sai dai kowace al'umma da nata al'adun da suka amince da su wajen gudanar da matakan rayuwarsu. Haka suma al'ummar Hausawa suna da Al'adun da suka amince da su wajen gudanar da matakan rayuwarsu na Aure da Haihuwa da Mutuwa, ba a buƙatar ko jin sunan Haihuwa matuƙar aure bai riga ta ba. Wannan ya nuna Hausawa sun ƙyamace miyagun halaye tun kafin su karɓi addinin musulunci.
Addinin Musulunci Addini ne
da ya riske Hausawa suna bautar iskoki, Kasancewar Hausawa masu sauƙin al'amari da nagartattun halaye, ya sa
suka karɓi
Addinin Musulunci hannun biyu har ake ganin duk mai magana da Hausa musulmi,
suma kan su Hausa ke kallon wasu al'ummomi da suka karɓi
addinin musulunci Tubabbu saboda nashewar da addini ya yi cikin al'adun
Bahaushe ta kowace fuska cikin al'adun Hausa. Kuma shi kan shi Bahaushe duk
inda ya samu kan shi yana tafiya da abubuwa biyu addini da al'ada haka yake
tafiya dasu har a kasa bambancewa tsakanin addini da al'ada. Irin daɗewar
da Bahaushe ya ya da addini sai ya haifar da Bahaushe ya shigar da addini sosai
cikin dukkan al'amurransa ciki har da sha'anin haihuwa.
Manufar wannan aikin ita ce
bayar da ma'anar haihuwa da muhimmancin haihuwa da bayyana tasirin da addinin
musulunci ya yi a sha'anin haihuwa tun daga shigar cikin har yaye sannan a
kammala aikin tare da madogara/Manazarta.
Ma'anar Haihuwa:
Ita kalmar Haihuwa a
Hausance tana nufin ƙaruwa
ko Daɗuwa
don kuwa a kan ce wane ya samu ƙaruwa
idan an yi masa haihuwa ko kuma a ce wance ta sami ƙaruwa idan ta haihu. Haka ma kuma akan
ce dukiya ta haihu Kai tsaye idan ta ƙaru.
Amma dai fitacciyar ma'ana ta kalmar haihuwa ita ce fitar da ɗa
daga ciki wato dai mace ta haife abin da ke cikinta (M T Adamu 2015).
Haihuwa ita ce fitar abu mai
rai cikin abu mai rai bayan ɗaukar lokacin da Allah ya ɗibarma
wannan abin na zama cikin ciki ko ƙasa
ko kwai. Duk kan abin da ke haihuwa ba zai sami ciki ba har sai aure ya ƙullu da jinsin namiji na wannan halittar
mace mai haihuwa.
Muhimmancin haihuwa:
Babu ko shakka a kan
muhimmancin haihuwar domin kuwa duk wanda ya haihu ya alfahari da 'ya'yansa
haka mai dukiya na alfari da yaɗuwar dukiyarsa haihuwa ta ƙunshi muhiman abubuwa kamar haka:
- Tabbatar da irin/ Hana kuɓucewar
irin
- Alfahari da yawa
- Barin
magaji
- Samun mataimaki
- Hana gori da sauransu da yawa.
• Shigar ciki:
Da zaran an yi aure abu na
farko fa kowa ke saurare shi ne samun ciki, har a ƙosa da jira idan anyi jinkirin samun
ciki har dangi su fara tambaya ko lafiya wance shiri?
Da an ce matar wane ciki
gareta abin murna da farin ciki ya samu ga 'yan uwa da abokan arziki. Addinin
musulunci tun da sha'anin bayyanar ciki ya fara tasiri don kafin Hausawa su karɓi
addini, Amarya baza ta san tana da ciki ba har sai an yi mata al'adar 'Karan ƙirji'
al'adace ta sanar da 'yan uwa da abokan arziki da dangin miji da na mata cewar
aure ya yi albarka ko da ba ayi al'adar a gabansu ba duk wanda ya ganta da ɗaure
da zane a ƙirji an san albarkar
aure ta samu (Sarkin Sudan B S).
Kenan tun kayaking farko na
haihuwa addinin musulunci ya kawar da wannan al'ada ya kawo sutura ya kuma hana
wasar kanin miji irin ta al'adar maguzawa, ta hanyar dokokin da addinin
musulunci ya tanadar ma zamantakewa.
•Renon Ciki:
Bayan bayyanar ciki kuma sai
kowane ɓangare
na 'yan uwa kowa ya duƙufa
wajen sauke nauyin da ya jingina garai na renon ciki da kula da mai ciki don
tabbatar da lafiyar uwa da abin da ke cikinta. Ba a cika ba mai karamin ciki
magain sha har sai ya kai wata bakwai, da yakai wannan lokacin za a fara bata
maganin zaƙi da sauƙin guiwa kamar:
- Sayen Danyi da Ƙayoyinta da Sassaƙen Daniya da Ganyen Loda da Karan dafi.
Sai a jiƙa su cikin kasko a aje wuri mai sirri,
da ta riƙa tsarki da ruwan maganin har ta haihu
don maganin fason farji (matucci). Haka kuma bayan cikin ya kai wata bakwai sai
a jiƙa mata waɗannan
magunguna a wuri mai kyau su zata sha lokaci lokaci har ta haihu.
- Gadon Maciji da Sasssaƙen Bubuƙuwa
da Saiwar Namijin yaɗiya wato Kulumbo.
A irin wannan ma addinin
musulunci ya zo da wasu magunguna da ake ba mai ciki kamar: Na'a Na'a da Hulba
da Ruwan zam zam da sauransu.
• Naƙuda:
Naƙuda ita ce babbar alama ta ƙarshe dake nuna kusan towar haihuwa, don
kuwa wani hali ne na damuwa da zafi da raɗaɗi
marar misali da mai ciki take shiga kafin haihuwa. Akwai alamomi da dama da
akan gane cewa naƙuda
ta zo musamman in ciki ya tsufa ya kai wata tara. Naƙuda tana ɗauke da tsananin zafi da zogi da shiga halin
damuwa ga makusantar mai naƙuda,
don ansan tashiga halin ko a haihu lafiya haka aka fi so ko a rasa ta ko arasa jariri ko a rasa su
baki ɗaya
wanda ba'a fatar haka. A irin wannan halin na naƙuda
addinin musulunci ya zo da sauyi mai cike da sauƙi ga
mata, don kuwa kafin zuwan musulunci:
Kafin zuwan Musulunci bayan
jiƙe_jiƙen
da ake ba mai ciki a kwai magunguna da aka tanada domin ba mai naƙuda na jiƙe_jiƙen itatuwa da saiyu da tsirrai da
sauransu. Misali. Jiƙa ƙasar ƙofar
ɗakin
mai naƙuda ungozoma takan samo tsohuwar wuƙa ta sassaƙo ƙasar ƙofar
ɗakin
da mai ciki take ciki ta sama da ta ƙasa
ta jiƙa abaiwa mai naƙuda dan haihuwa da sauri kuma cikin tsauƙi. Idan an sha waɗannan
abubuwa kuma ba'a haihuwa sai abi waɗannan
matakan:
• Sa muciya a bakin mai naƙuda:
Idan naƙuda ta yi nauyi, mai
naƙudar ta galabaita kuma ga ɗa
yana son fitowa ƙarfin
uwar ya ƙare sai ungozoma/mai taimakon mai
haihuwa ta sa akawo mata mucciyar tuƙa
tuwo ta tura ma mai naƙuda
ita abaki da muciyar ta taɓa maƙoshi ta sai ta fara kakarin amai wannan
kakarin da mai ciki ke yi sai ya taimaka wa yaro ya fito, shi ke nan sai murna
da kula da uwar da abin da aka haifa bisa ga al'ada. Wannan kakarin ya zama
maimakon nishin da ake buƙatar
tayi kuma ƙarfinta ya ƙare saboda zafi da wahalar naƙuda.
• Yin turare tanka: Idan aka
sa muciya ba a haihu ba sai a ɗebo wuta a daka tanka a fara
rufe ɗakin
da take a zuba tankan cikin wutar sai hayaƙin
ya game ɗakin
ga yaji sai ta fara tarin kafin hayaƙin ya gama ta dalilin tarin tuni an
haife abin da ke ciki.
Wadannan duk hanyoyi ne na ƙarin azabtar da mai naƙuda da musulunci ya zo sai aka samu
abubawa da suka haɗa da:
• Yi wa abin da ke ciki Sallama: Ungozoma
takan tsaya a gaban mai naƙuda
tana yin sallama ga abin da ke ciki, tana cewa " Assalam salam, Assalam
salam gade Rakayyadi ko Rakayyada, muna lale marhabin cikin farin ciki da
walwala, muna lale da zuwa cikin Duniya gidan ƙarya.
A sauko a sauko a sauko salamun salamun, Allahumma amin. Za ta fadi haka har
sau uku.
•Idan naƙudar tayi nauyi ba a haihu ba sai a jiƙa wani abu da ake cema Hano ko Hannun
Fatcima, wani abu ne mai yatsu biyar amma a dunƙule
yake in an jiƙa wa mai naƙuda in haihuwar babu matsala kuma lokaci
yayi ana jiƙa shi sai yatsun su
buɗe
sai aba mai ciki tana sha sai haihuwa. In ko akwai sauran lokaci ba zai buɗe
ba. Abin ya ƙiya kenan.
•karɓo
Rubutu wurin malamin da ke ba da rubutu a unguwar. Cikin waɗannan
hanyoyin sai a haihu da yardar Allah. Kuma duka babu inda tasha irin wahalar da
ake sha a baya.
• Haihuwa:
A wasu lokutan haihuwa ta
kan zo farat ɗaya bagatatan babu shiri sai mace kawai
ta haihu ba wata gargada, Ungozoma bata
kusa. A wannan yanayin sai a ɗauki jaririn a ɗora
kansa bisa sabuwar tsintsiya a kusa da mai haihuwa kafin zuwan unguwar zoma.
Haka kuma ana haihuwar wasu
yara da riga har ana yi wa irin wanɗannan
yaran laƙabi da 'Mai riga'. Ana gutsura jikin
rigar ta haihuwa ayi wa yaro laya da ita, maganin baki da tsari daga Ibilishi.
• Wanka Jariri:
Wajen Hausawa rashin wanke
Jariri da farko ya fita fes fes yakan haifar da warin jiki idan mutum ya girma,
shi ake kira warin ƙashi.
Ana wanke Jariri sau uku idan namiji ne mace kuma sau huɗu,
kuma idan an yi wankan in za a zubar da ruwan wankan wadda za ta zubar sai ta
fashe da dariya wai don yaron ya yi fara'a in ya girma, haka za a yi ta yi har
a gama wankan, ana ba yaro ruwan wankan shi na ƙarshe
ya sha wai don ya tashi da abin kai nai ya iya dogaro da kai da neman na kai.
wannan duk tasiri ne da
Musulunci ya yi a kan al'adun Hausawa da na haihuwa, game da sallamar da ake
yiwa jariri yana ciki, da wadda ake yi mai in anyi mai wanka, wannan sallamar a
maimakon kiran sallar da addini ya tana ce.
Ana gama yiwa yaro wanka sai
Ungozoma ta yi wa jariri sallama ta ce " Assalam salam Rakayyadi in namiji
ne, Assalam salam Rakayyada in mace ce".
A rana ta uku sai kakan
jariri ko ubansa ya je wurin wani malami ya sanar da shi an samu ƙaruwa, kuma ga sunan da ya ke so ko ya
bar wa malamin ya zaɓa masa. In malamin ya je sai
a fito da jaririn malam ya yi masa "Kiran sallah a kunnen dama iƙama ga kunnen hagu" wato huɗuba.
Haka kuma a ranar zanen suna
musulunci ya yi tasiri ga sha'anin zanen suna tun daga fara salati ga Annabi da
karanta Fatiha da addu'o'in da ake aiwatar a ranar duk addinin musulunci ya zo da
su.
Wannan duk tasiri ne da
Musulunci ya yi a kan al'adun Hausawa da na haihuwa, game da sallamar da ake
yiwa jariri yana ciki, da wadda ake yi mai in anyi mai wanka, wannan sallamar a
maimakon kiran sallar da addini ya tana ce.
• Camfe-Camfen Haihuwa: Camfi
wata hanya ce ta ƙudurce
afkuwa ko faruwar wani abu da sakamakonsa zai iya zama mai kyau ko amfani ko
mummuna mai cutarwa kuma ya danganci yarda da amincewa.. Adamu T. M (2015).
Camfi yarda ce da al'ummar
Hausawa su ke da suma suke tafiyar da rayuwarsu tare da shi, duk zamanin da
Bahaushe ya tsince kansa zai ƙirƙiri camfi daidai da wannan zamanin. Haka
abin yake ga sha'anin haihuwa akwai camfe-namfen da suka keɓanta
ga mai ciki har tayi yaye tana, kamar:
Rowa, ɗaibar
ruwa Rijiya da dare, kallon mai naƙasa,
zuwa kasuwa, Tsallake rafi, Leƙe,
Zama ƙasa, Hujin hanci Tsiwa (rashin
kunya), Taɓa
kayanta kafin wankin nono, Fita waje kafin suna da kuma bayar da nono tsaye da
zubar nono ga jariri.
Waɗannan
da ma wasu camfe-camfe ne da addini ya kawar da ci a sha'anin haihuwar Hausawa.
• Sunaye:
Kafin Zuwan Musulunci
Hausawa na amfani da lokaci ko sanadi ko yanayi ko sifa wajen rada wa yaro
suna.
Misali: Sunayen lokaci, Ɗan dare da Tarana Magawata/ Harande da
Malka Anaru da sauransu.
Sunayen Sanadi sun haɗa da:
Korau da Hana da Audi da Kamaye da Bakuso da Tuni ko Tunau da Tumba da Dela/
igge/ kande da Tanko/ Mati da sauransu.
Sunayen Yanayi: sun danganci
yanayin da aka haifi yaro, irin su sun haɗa
da: Mai riga/ Sutura da Gambo da Ayashe da Gwamma da Kyauta da Makwashi da Auta
da sauransu.
Sunayen Sifa: Irin waɗannan
sunayen suna samuwa ne da dalilin sifar yaro. Kamar: Zabaya da Cindo da Cibi da
Jatau da Kumatu Dodo da sauransu.
Amma da addinin musulunci ya
zo cikin rayuwarsu sai suka sauya sunayensu zuwa na addinin musulunci suma kuma
sun kasu kamar haka sunayen Allah da na Annabawa da na Mala'iku da na Sahabbai
da na Waliyyai da na Alƙur'ani
da sunaya daban daban da na Sha'awa.
Sunayen Allah: Su ne sunayen
da aka samu dalilin karɓa Musulunci kuma Hausawa a
ko'ina a faɗin duniya suna sa wa yaransu su, sunayen
sun haɗa
da: Abdullahi da Abdurrahman Abdulkarim da Abdulhamid da sauransu.
Sunayen Annabawa: Daga cikin
sunayen Annabawa Hausawa sun sa wa yaransu su, wasu sun barsu yadda yake wasu
kuma sun yi kwaskwarima, misali: Adamu ,Ado, Ada da Ibrahim, iro Yunus,yanusa
Inusa Muhammad, Mamman,Na'Allah Na Ta'ala da sauransu
Sunayen Matan Annabawa: Nana
Khadijah, Hajo, Hadi, Dije. Nana Saudat, Saudi, saude. Nana Aisha, Ai, Shatu,
Indo. da sauransu.
Sunayen Mala'iku: Jibiril da
Mika'i da Ridwan da sauransu.
Sunayen Sahabbai: Abubakar
da Umar da Usman da Aliyu da Bilal da Hamza da Jafar da Barira da Suwaiba da
Sauransu.
Sunayen Waliyyai: Sayuɗi da
Hambali da Hanafi da Gazali da Shehu da Inyas da malik da sauransu.
Sunayen daga Alƙur'ani: Suna ye ne da aka ci karo da su
ciki Al'ƙur'ani irin su Lantana daga
"Lantanalul birra" Falyata daga "Falyatana fa silmutana
fisun" da Raihan/Raihanat dana "Walhabbu zul asfi war raihan" da
Sauransu.
Sunayen daga Abubuwa
daban-daban: waɗannan sunayen sunaye masu
naso na musulunci da dama waɗan da Hausawa ke la'akari da
su wajen sanya wa lya'yansu kamar sunayen ranakun mako, irin su Jimma da
Asshibi da Ladi da Tanin Balaraba da sauransu. Sunayen lokaci Kuma kamar
Masalaci da Imam da Azumi da Hajiya ko Alhaji da Sunayen sha'awa kamar Aziza (Madaukakiya) da Aliya ( Mai girma) Kausar da
Huda da Hamida da Fa'iza da Bushra da sauransu
Adam T.M (2015).
Sunayen Sha'awa: mafi yawa
Hausa lakabi suka fi yi wa yaransu da irin waɗannan
sunayen misali: Aman da Aarif da farhan da Fu'ad da Mahir da sauransu. Anan
Addinin Musulunci ya bada gagarumar gudummawa a sunayen 'ya''yan Hausawa.
• Shayarwa:
Shayarwa na nufin aikin
ciyar da Jariri da nono kai tsaye daga nono Uwa. Hanya ce ta ɗabi'a
ta samar da abinci mai muhimmanci da kariya ga jariri a farkon rayuwar. Nono na
ƙunshe da abubuwan da jikin jariri ke buƙata wajen haɓaka
girman yaro. Shayarwa na inganta haɗin
gwiwa tsakanin uwa da yaro kuma tana da fa'idoji da yawa na koyon lafiya ga uwa
da jaririnta.
Addinin Musulunci ya zo da
hukuncen hukunce game da abin da ya
shafi shayarwa da lokacin da ya dace a yaye yaro. Saɓanin
abin da aka saba kafin musulunci ya nashe dukkan al'adun Hausawa ta kowane ɓangarorin
rayuwa.
Akwai ayoyi da hadissai da
ke ɗauke
da hukuncen hukunce da suka shafi shayarwa da yaye kamarhaka:
والوالدت يرضعن اولدهن حولين كاملىن لمن اراد أن يتم
الرالرضاعة
Kuma
masu haihuwa (sakakku ) suna shayar da abin da suka haifa shekaru biyu cikakku
ga wadda ta yi nufin cika shayarwa.(Sura ta 2 aya 233).
ووصينا الإنسن بوالديه حملته ٱمه وهنا عل وهن وفصاله في
عامين أنشكرلي ولوالديك الي المصير
Kuma munyi wasiyya ga mutum game da mahaifansa biyu
(uwa da uba). Uwarsa ta ɗauke shi a cikin rauni akan wani rauni kuma yayensa a
cikin shekaru biyu (Muka Ce Masa) Ka gode MINI da kuma Mahaifanka biyu makoma
gare Ni kawai take. (Sura ta 21aya 41).
Manzon
Allah (S A W) ya ce " Nonon Uwa shi ne Mafificin Nono ga yaro, kuma a
shayar da Yaro har ya Kai shekara biyu" ( Sahih Muslim).
A wani hadisin kuma cewa ya
yi, Annabi Muhammad (S A W) ya ce " Babu Nonon da ya fi na Uwa,
Waɗannan
ayoyi ne da hadisa da suku nuna yadda mace ke wahala game da ɗaukar
ciki da kuma lakaci yaye.
Haka kuma a lokacin
shayarwar aiki biyu ta ke yi aikin shayarwa da ba da tarbiyya ga yaro ta fuskar
umuni da hani akan koyarwar addinin musulunci kamar bashi nono da Bismillah da
fara bashi na dama tun yana jariri daga nan har ya girma ta fara bashi abu ga
hannun da umutar yaro yaci ya ya sha ya sa duk da hannun dama tare ya yin
Bismillah yi wa yaro addu'ar safiya da ta yamma fara koyar da yaro addu'a idan
ya fara magana haka dai za'a aza yaro a kan halaye da ɗabi'u
da addini ya tana da. Bayan yaro ya kai lokacin yaye kuma akwai abubuwan da ake
gudanarwa na al'ada da addini ya yi tasiri akai kama ana kan yi, ita ce al'adar
ba dan yaye rubutu don kar ya yi rigima ana ba yaro rubutun daidai rigimar yaro
in yaro bai da rigima sosai ba a bashi da yawa.
A sha'anin haihuwa addinin
musulunci ya yawo sauyi sosai da duk da al'ummar Hausawa suna da tsarin tafiyar
da rayuwarsu daidai kaifin tunaninsu, kusan duk wani mataki da kula da mai ci
al'adar Hausawa ta tanade shi, sai dai addini ya kore wasu ya tabbatar da wasu
ya ƙara kyautata wasu.
Kammalawa:
Anga ma'anar haihuwa bayan
bayanin buɗewa da muhimmancin haihuwa da tasiri
Addinin Musulunci ga al'adun haihuwa tun daga shigar ciki har yaye.
Manazarta:
Adamu T. M ( 2015). Haihuwa da Suna. Salma- A'aref Publishers
Kano Nijeriya.
Ibrahim A. S Sudan. Karan Kirjin Maguzawa. Sashen koyar da Al'adun Hausawa Jami'ar Usmanu Danfodiyo Sokoto.
Inno Shenu |
Raihanatu Umar Garba 08100887109 |
Aisha Hassan Hassan |
Fatima Yahya kamar |
Aisha Abubakar D/daji |
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.