Gabatarwa:
Wasannin yara wasanni ne da mafi yawansu na motsa jiki ne da gudane-gudane, kuma ana aiwatar da su da sigar kwaikwayo, wasannin na nuna cikar lafiyar yara, ana gudanar da su ne da dare lokaci farin wata a wani wuri na musamman da aka tanada don yin wasannin (Dandali). Duk da yake yara komai nasu wasa ne amma akwai hikimomi da fikira da basira da ke ƙunshe a cikin wasannin, da ke da manufar faɗakarwa da nishaɗantarwa da ilmantarwa da koyar da jarumta da bin doka da ƙa'ida waɗannan da ma wasu suna ƙunshe cikin wasannin yara na gargajiya, wani abin sha'awa har yanzu ana jin waƙe-waƙensu cikin bakin yara.
Manufar
wannan aiki ita ce, bayyanin sunan wasar da kayan aikin wasar da yadda ake
aiwatar da wasar da hikimomi ko abubuwan da wasar ta ke koyarwa da Illolin
wasar, sai kammalawa a ƙarshe
da madogara.
• Bayanin sunan wasar:
Gidan Rina Gidan Zarnaƙo, Rina da Zarnaƙo(zanzaro). dukansu Kwari ne masu
hira halittarsu tayi kama da ta ƙudan zuma da ƙudan
gida. Haka kuma suna harbi (cizo) mai cutarwa, cizon su yana da raɗadi sosai ba ga yaro kawai ba
har ga babba a taƙaice kwari ne masu haɗari da ake hana yaro taɓa mazauninsu da zuwa inda aka ga alamarsu, ko fitowa suka yi
suna yawo za a yi ta ƙoƙarin kare kai daga cutarsu. Wannan kaffa kaffa da ake game da waɗannan ƙwarin
ya haifar wa yara tunanin gina wasa mai sunan waɗannan ƙwarin, ta dalilin cizon da ɗaya daga cikin kwarin ya yiwa wasu daga cikin yaran ko suka ga
sun cije wani da ganin irin mawuyacin halin da ake shiga ta dalilin cizon, tare
da gina ta bisa wasu sharuɗa da ƙa'idoji. A gani na wannan shi ne dalilin raɗa wannan sunan na GIDAN RINA
GIDAN ZARNAƘO.
• Kayan aikin wasar:
Kamar sauran wasannin yara ita ma wannan wasar akwai wasu
abubuwa da ƙa'idojin da ta ƙunsa, Jagoran wasar zai faɗa, duk da yake duk wanda ke yinta ya san da ƙa'idojin
da abubuwan da ake buƙata don yin wasar:
- 'Yan wasa: yaran da
zasu gudanar da wasar sun haɗa da maza da mata (Tarayya).
- Wuri: za a samu wani
wuri na musamman a cikin filin wasa a sa wata alama/shaida da nufin nan ne
matsera ko wurin sha (wurin da idan yaro ya karya doka zai gudu da ya taɓa wurin ya tsira).
- Buloli: Yara mata kan
murɗe gyaluluwansu ko ɗankwalayyensu, yara maza su murɗe rigunansu, su koma kamar
dorina ko bulalar doki.
Waɗannan kayan da aka tanada da su za a aiwatar da wasar, da jin
sunan wasar da kuma kayan yinta za a fahimci sai yara jajirtacci da masu juriya
kuma sai yara yan sa'a ɗaya ke aiwatar da wasar don wanda duk ya shiga cikin yaran da
suka girme shi zai wahala sosai.
• Yadda ake gudanar da wasar:
Yara ne 'yan kai ɗaya da ba su kasa yaro goma abin da yayi sama da haka ko kasa da
haka ba maza da mata, zasu zagaye cikin da'ira su riƙa
hannuwan juna sai yaro ɗaya da zai fara ya sai ya shiga tsakaninsu ya fara rera waƙa kamar
haka:
G/waƙa: Gidan Rina gidan Zarnaƙo,
Amshi: Kwandon Ƙaya.
Jagora: Gidan Rina gidan Zarnaƙo,
Amshi: Kwandon Ƙaya.
Jagora: Gidan da ba a dariya ba a ɗumi!
Amshi: Kwandon Ƙaya.
Jagora: Koway yi dariya a kashe
mai!
Amshi: Kwandon Ƙaya.
Jagora: Hum umama hum umama hum!
Ke dela ke
dela keh!
Haka jagoran zai ci gaba da aiwatar da abubuwan ban dariya da
nufin ba da dari ga sauran yara yana bin yaran ɗaya bayan ɗaya don ya samu wanda zai yi galaba a kan sa ya yi dariya. Da ya
samu wanda ya yi dariya sai kawai duka daga Kowane yaro, da yake yaran suna sane
da dokar wasar wato ba a dariya ba a ɗumi (anji tun ga baitin waƙar) da yaro ko yarinya ta yi
dariya zata sheƙa da gudu domin kaiwa wurin da aka tanada don tsira daga dukan
da sauran abokanin wasar za su yi mata ko yi ma shi, da ya ko ta taɓa wurin da aka tanada shi ke
nan ya/ta tsira ba a bugunsa/ta. Sai a adawo wurin wasa a sake ƙulla
wasar amma yaron da yaje warin tsira/sha, shi zai zama jagora shi kuma jagoran
ya tsaya wurin da wancan yaron ya fito, haka za a yi ta yin wasar har lokacin
tafiya gida wato tashi.
• Hikimomin da Wasar ta Ƙunsa ko Abubuwan da Wasar Take Koyarwa:
i - Koyar da Jarunta da Juriya.
ii - Motsa jiki da kiyon lafiya.
iii - Bin doka da ƙa'ida.
iv - Nishaɗantarwa.
v - Haɗin kai da Ƙarfafa Zumunta.
vi - Ilmantarwa da gwaninta.
i - Koyar da Jarunta da Juriya: Jarunta na nufin jajircewa da dagewa tare da nuna hazaƙa game da yanayi ko wani abu da mutum ke aiwatarwa (Gobir da
Sani 2021). Tun wurin ƙulla
wasar duk yaro mai tsoro ko raggo marar isassar lafiya ba zai shiga wasar ba.
Wannan wasar an dubi irin haɗarin da ke da ga kwarin sai aka tsara wasar ta zama cikin irin
haɗarinsu ta fuskar duka/bugu ko
gudu don kai wa matsera/wurin sha. Anan daukar dukan yaro sama da biyar lokaci ɗaya sai jajirtaccen yaro mai
juriya haka shi ma gudu sai jaruntattun yara, shi ya sa duk yaron da ya kware a
irin wannan wasa ba ya jin wahalar guda sam, haka kuma a fagen dariya ga abin
dariya an yi, amma dole yaro ya jure ko ya sha duka.
ii - Motsa jiki da kiyon lafiya: "Motsa jiki na nufin jijjiga jiki da nufin a ware jini,
ware jini na da matuƙar amfani ga lafiyar ɗan Adam" ( Gobir da Sani 2021). Kusan dukkan wasannin yara suna ɗauke da motsa jiki da kiyon lafiya domin kuwa ana yin wasannin
ne bayan an ci abincin dare, maimakon a kwanta wanda hakan na taɓa lafiya sai a tafi wurin wasa.
Wasar kuma tana ƙunshe da gudane-gudane da tsalle-tsalle da buge-buge abubuwa dai
na motsa jiki da suka shafi hakan. Motsa jiki kuma yana inganta lafiyar manya
ma ballai yara.
iii - Bin doka da ƙa'ida: "Doka na nufin umurni ko ƙa'ida da aka gindaya musamman daga hukuma ko shugaba, duk
al'ummar da ba ta bin doka da ƙa'ida hakiƙa zata samu sakwarkwacewa da koma baya ga lamurranta" (Gobir da Sani 2021).
Wannan wasar tana ɗaya daga cikin wasannin yara da suka ƙunshi
doka da ƙa'ida
kamar wasar gidan kurciya shaya, daga cikin wasannin da ke da
doka da ƙa'ida
sun haɗa da:
- Gidan Rina gidan Zarnaƙo
- Gidan kurciya shaya
- Jini da Jini
- Noti-Noti
- Salar kwaɗi/ Nayi haka ba nayi Haka ba
- Belungu, kusan tsarin
ta ɗaya da sallar kwadi
Waɗannan da wasu duk sun ƙunshe da doka da ƙa'ida.
Kuma daga nan yara ke fara fahimtar amfanin bin doka da kuma illar rashin bin
doka.
iv - Nishaɗantarwa: Nishaɗi na nufin wani yanayi ko hali
ko farincikida annashuwa da ɗan Adam ko wata halitta kan iya shiga, mai nishaɗi yana kasancewa cikin walwala
da rashin damuwa. Nishaɗi na da amfani matuƙa ga rayuwar ɗan Adam,domin yakan taimaka
wurin guje wa wasu cututtuka musamman waɗanda suka shafi zuciya da kuma shafar Aljannu. (Gobir da Sani 2021)
Wannan wasa kamar sauran wasannin yara tana sa yara nishaɗi sosai ta fuskar abubuwan da
jagoran wasa ke yi don ya sa yara su yi dariya, tun fara wasar har a kammalata
yara cikin nishaɗi su ke.
v - Zumunci: Zumunci na nufin kyakkyawar alaƙa ko dangantaka ta jini ko ta
abota da akan samu tsakanin mutane, za a iya hasashen cewa kalmar ta samo asali
ne daga zumu da ke ɗaukar ma'anar ɗan'uwa ko sa'a ko aboki. (Gobir da
Sani 2021).
Haɗuwar da yara keyi wuri ɗaya don aiwatar da wasar, yana haifar da sabo da shaƙuwa da ƙaunar
juna da tausayin juna da mutunta muradun juna, ta haka ne idan wani abu ya samu
ɗayansu sauran yara za su taru
su taya shi murna ko jaje. Haka abin yake idan faɗa ya haɗa wani da abokin wasarsu sai inda karfinsu ya kare, irin wannan
haɗin kai da Ƙarfafa
Zumunta yana ɗorewa har
girma, matsawar ana tare koma ba a tare ba za a manta lokacin ƙurciya
ba, har a riƙar faɗar tare muka yi wasa. Wasa ta ƙulla zumunta kenana.
vi - Ilmantarwa da
gwaninta: Ilmantarwa na nufin sanar da wani ko
koya masa ko nuna masa wani abin da bai sani ba. (Gobir da Sani 2021).
Wannan wasar tana koyar da jarumta da juriya da gudu da kuma gwanewa a kai.
Haka kuma tana ilmantar da yara a kan fa'idar kiyaye doka kamar yadda aka nuna
musa kiyayar wurin zaman Rina da na Zarnaƙo wannan ya zama ilimin sanin
amfanin bin doka don zaman lafiya.
• Matsaloli ko Illar Wasar Gidan Rina Gidan Zarnaƙo:
Duk da tarin fa'idodi da wasannin yara suka ƙunsa ba
a rasa matsaloli ko illolin da tsinta a cikin su koda kaɗan ne. Wannan wasar kasancewar
an gina ta a kan sharaɗin duka, to ana samun maketatan da ke da ƙudurin
sharri ga abokaninn wasa, ta hanyar:
- Ƙeta
- zamba cikin aminci
Duk in da zama ya haɗa mutane ba a rasa wani abu na rashin haɗuwar jina ko makamancin haka.
Dalilin hana ana samun wasu yara su rinƙa bugun ƙeta, ga
wanda yayi dariya, ta dalilin rashin haɗuwar jini ko wani abu da ya taɓa haɗa su a baya, wasu kuma zamba suke haɗawa da ita da za su sa dutse
cikin laulayar ko murɗewa yadda idan suka bugi yara zai ji ciyo, musamman in wani daga
cikin yaran ya zama jajirtaccen, sai a haɗa kai ba tare da ya sani ba dan kar a ce ya fi su jarunta.
Idan an kama yaro da irin laifin nan za'a ja kunnenshi tare da
yi mai gargadi kar ya sake, in ko ya taɓa yin irin wannan halin sai su yanke shawarar ba su ƙara
wasa da shi.
Saƙon Wasar: wannan wasar tana isar da
sakon cewa lallai waɗannan kwarin suna da haɗari ga yara, sanadiyar harbin(cizo) da su ke yi. A nuna haɗarinsu a cikinta ta yadda yara
za su fahinta.
Kammalawa:
Bayan ɗan bayanin abin ya shafi wasannin yara tare da faɗar samuwar sunan wasar da kayan
aikin wasar da yadda ake gudanar da wasar da hikimomin da wasar ta ƙunsa da
illar wasar.
Manazarta:
Y. A Gobir da A. Sani (2021). Waƙoƙin Hausa Na Gargajiya. Printed in Nigeria by Amal printing
press.
Umar. M. B (2009). Wasannin Tashe. Northern Nigerian
publishing Company Limited, Gaskiya Building. (Ba a samu ba a ciki).
Gusau. S. M. ( 2001). Wasannin Yara. Century Research and
publishing Company Kano Nigeria. (Ba a samu ba a ciki).
Hira da Aisha Ibrahim ƙawata ta wayar salula dan
Tunatarwa. A ranar Laraba 16/08/2023.
Hira da Sufyanu Abubakar ta baki da baki (ɗan yayana). A ranar Juma'a 18/08/2023
Raihanatu Umar Garba
08100887109
No comments:
Post a Comment
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.