Ticker

6/recent/ticker-posts

Dangantakar Al’ada da Addini

Takarda da aka gabatar a taron }ara wa juna ilimi na [alibai masu karatun Digiri na Uku (PhD) a Sashen Harsunan Nijeriya, Jami’ar Usmanu [anfodiyo, Sakkwato, Satumba  04-09, 2023

Shehu Adamu

+2348038403450

Department of Nigerian Languages,
Usmanu [anfodiyo University, Sokoto, Nigeria.

Tsakure

Wannan bincike mai taken: Al’ada da Adabi Tamkar [anjumma ne [anjummai. An gina shi ne domin a gano dangantakar da ke akwai tsakanin al’ada da adabi. Manufar wannan bincike shi ne ya fito da dangantakar da ke tsakanin al’ada da adabi, da yadda al’ada ta taimaka wajen gina adabin Hausa. An yi amfani da dabaru domin gudanar da wannan binciken kamar nazarta rubuce-rubucen magabata, da kuma hira da masana wannan fanni. Binciken ya tabbatar da adabi bai samu ba sai da al’ada ta baje kolin hajarta sannan adabi ya samu ranar shanya garinsa.

Dabarun Bincike

A wannan bincike, an yi amfani da hanyoyi da dabaru daban-daban domin tattara bayanai da za su taimaka a samu nasara. An yi amfani da nazarin rubuce-rubucen magabata wa]anda ke da ala}a da wannan aiki. Wa]annan ayyukan sun taimaka matu}a wajen bayar da haske da sanin makamar gudanar wannan aikin. Haka kuma an tattauna da masana, wa]anda aka samu bayanai masu inganci da suka taimaka aka }ara samun nasarar gudanar wannan bincike. 

Shimfi]a

Al’ada da adabi su ne manyan tubalai na ginin rayuwar al’umma, domin babu wata al’umma a duniya da za ta wanzu ba tare da ta martaba al’adunta da adabinta ba. Al’ummar Hausawa tana ]aya daga cikin al’ummun duniya masu bugun gaba da al’dunsu da adabinsu, kasancewar su ne ke jagoranci wani fanni na rayuwa musamman wa]anda ba su ci karo da addinin musulunci ba. Bahaushe mutum ne mai ri}o da al’dunsa musamman idan ya samu kansa a wasu wurare da ba }asar Hausa ba, yana }o}arin ya nuna shi Bahaushe ne ta ~angaren suturarsa ko abincinsa ko wasu halaye na kirki wa]anda za su nuna shi Bahaushe ne. Wato, mutum ne mai yin guzurin al’adarsa a duk inda ya samu kansa

Ma’anar Al’ada

Al’ada tana nufin dukkanin rayuwar ]an Adam tun daga haihuwarsa har zuwa kabarinsa. A ko’ina mutum ya samu kansa duk wata ]abi’a da ya tashi da ita tun farkon rayuwa ya tarar a wurin da yan rayu, ko yake rayuwa ita ce al’adarsa da za a yi masa hukunci a kai. Babu wata al’umma da za ta rayu a doron }asa face tana da al’adar da take bi, kuma da ita ake iya rarrabe tad a wata da ba ita ba

Matakan rayuwar ]an Adam uku su ne ginshi}in ginin al’adunsa. Matakan su ne Aure, da Haihuwa, da Mutuwa. Wa]annan matakan rayuwa }unshe suke da sirrin al’adar da mutum ya tashi ciki, yadda take da yadda take gudanar da ita.

Masana al’ada suna kallon al’ada a fuskoki daban-daban gwargwadon yadda za a iya fayyace }unshiyarta. Ta fuskar yanayi, ana iya kasa al’adar Bahaushe gida uku; waddab ake aiwatarwa da ga~~ai, da wadda ake furtawa da baki, da wadda ake }udurtawa a zuci ta zama a}ida.

Al’ada ita ce ginshin}in rayuwarn kowace al’umma don haka matsayinta ga al’umma yake da yawa. A cikin kowace al’umma, al’ada na a }allal wa]annan muhimman matsayi kamar siyasa da tattalin arziki da zamantakewar jama’a da tsaro da sutura. Kowace al’umma tana da hanya ta musamman tun kaka da kakanni da take bi wajen gudanar da sha’anin mulkinta da yadda take gudanar da kasuwancinta da zamantakewar a tsakaninta, kamar aure da bukukuwa dag ado. Hausawa al’umma ce mai ri}o da al’adunta da tsarin rayuwarsu yake gudana a kai. An san Hausawa da ri}on al’adunsu a duk inda suka sami kansu.

Al’ummar Hausawa mutane da ke alfahari da abin da al’adunsu suka shata sau da }afa musamman a fagen tarbiyantarwa, kyakkyawar zamantakewa tsakaninsu da juna da kuma duk wasu al’umma da suke mu’amala da su. Ta hanyar al’ada ce Hausawa ke ]aukar nauyin kula da ganin ‘ya’yansu sun tashi cikin kyakkyawar tarbiya da za su samu kar~uwa ga al’umma baki ]aya.

Ma’ana Adabi

Adabi wata hanya c eta fayyace yadda Hausawa suke sarrafa aikace-aikacen fasahohinsu domin sau}in aiwatar da ayyukan yau da gobe.

Adabin baka wani nau’i ne wanda yake ]auke da zantuka gajeru ko dogaye na hikima wa]anda suke zuwa datsi-datsi, ko a shimfi]e da ‘’Ka’’ ba a rubuce ba, tare da koyar da darasi daban-daban.

Za a iya fahimtar adabi ta yin la’akari da abubuwa guda biyu. Na farko shi ne harshe, wanda yake ma}unshin tarihi kuma linzamin bayyana tunani, ko wata manufa. Na biyu kuma fasaha wadda da ita ake bayyana tunanin da ke cikin zuciya.

Al’ada a Matsayin Rayuwa ta Zahiri

Duk wani abu da al’umma ta aminta da shi a cikin sha’anin rayuwar na yau da kullum ya zama al’ada. Wannan ya shafi duk abin da al’umma ke aikatawa a zahiri wanda ya zama rayuwa ba ta gudana sai da shi. Al’ada ta kasance duk wani abu da ]an Adam ke aikatawa tun daga haihuwarsa har zuwa mutuwa, wanda ake aikatawa da ga~~ai da kuma wanda ake furtawa da baki. Idan haka ne to al’ada ta kasance duk aikin da mutum ya yi da abin da mutum ya furta a bakinsa wato ta }unshi kowace irin rayuwa kama daga aure, haihuwa bukukuwa sana’a zamantakewa fasahohin al’umma, tunaninta da duk abin da rayuwa ta aikata.

 

 

Adabi a Matsayin Hoto na Rayuwar Hausawa.

Adabi hoto ne ko madubi da ake amfani da shi wajen duba tun daga haihuwa har zuwa mutuwa na al’ummar Hausawa, wannan ya }unshi duk wani abu da ya shafi al’adun Hausawa da suka aikata a zahiri na ga~o~i da kuma wa]anda suka furta da baki. Wanda ya }unshi abubuwa da dama da suka ha]a da halayyar rayuwa da ayyukan fasaha da hikima da ]abi’u da abinci da muhalli da sutura da duk wani abu da al’ummar Hausawa ke tin}aho da shi.

Adabi tamkar fitila ce da ake amfani da ita domin haskawa, wajen gano yadda al’umma Hausawa ke gudanar da al’amurran rayuwarsu ta yau da kullum.

Wannan ya nuna cewa adabi yana bugun gaba ne da al’ada wajen samun abin da zai nuwa wa al’umma, domin idan babu al’ada adabi ba zai rayu ba har shi kawo wannan zamani da ake ciki.

Hanyoyin za a iya Gane Al’ada da Adabi [anjumma ne da [anjummai

Za a yi amfani da rassan adabin baka domin fahimta yadda adabin ya samu damar share fagen baje-kolin hajojinsa. Za a ]auki rassan ]aya bayan ]aya domin fahimtaar inda adabi ya samu  kayan da suka bashi damar fayyace hajarsa.

Wa}a

Al’adun Hausawa sukan zama kan gaba wajen samarwa da gina wa}o}in al’umma musamman wa}o}in baka. A kan sar}a manyan da }ananan sa}onni na wa}o}in baka gwargwadon abubuwan da suke zagaye da al’umma na al’adunta da sauran abubuwa na matallaba rayuwar zamantakewa. A lokacin da Hausawa suka iya shirya wa}a sai aka sami maka]an baka wa]anda suke yi wa mutane a rukunoninsu mabambanta wa}o}i kuma suka ta~o kowane fanni na rayuwar Bahaushe kamar noma da farauta da sana’a da abinci da sutura da aure da haihuwa da mutuwa da kuma zamantakewa mai kyau da marar kyau, kamar karuwanci da zauranci da sata da duk wani fanni na rayuwa, domin cusa darasi a cikin rayuwar al’ummar Hausawa.

Misali a ~angaren al’adar Bahaushe ta sanya sutura.

Alhaji Musa [an}wairo a wa}arsa ta Mu bi al’adunmu na gargajiya.

Kyawon ]an Arewa babbar riga

Ga rawani ga jamfa

……………………

Abin ga da ban takaici

Sai ka ga ]an Musulmi (Bahaushe)

Da wando yadi guda

Ga ‘yas shat ya sa a wuya nai

Ba hulla ga kai nai

Aljihunai ba tasbaha

Sai kwalin sigari

………………………

Kuma kau matanmu da ad]iyan Musulmi

Ku zanka yi lullu~i

Ban da sayen sikyat da yak kanti

Kuna ta yawo rariya-rariya

Abin ga ya ba mu kumya.

 

Wannan wa}ar Alhaji Musa [an}wairo ta fito da bayanin yadda al’adun Hausawa suke na sanya sutura, yadda ya kamata Bahaushe Musulmi ya kasance da riga da hulla, ba gan shi da sutura na Turawa ba kamar shat da sauran su. Haka kuma, ~angaren mata ya bayyana su zan ka yi lullu~i da saka kallabi, kuma su daina yawa banza. A nan ya fito da al’adun Hausawa na sutura da kunya kamun kai.

A ~angaren sana’o’in }asar Hausa akwai rukuni na musamman na masu gudanar da wa}o}i a wannan fanni kasancewarsa mai muhimmanci a rayuwar Bahaushe.

Misali. Sani Aliyu [andawo a wa}arsa ta Sarkin Ma}era Tukur.

 

Sarki uban manoma

Sarki uban maharba

Sarki uban ma’aska

Sai ka yi sannan su kai

In ba a }ere-}ere sana’ar ga uku da ko ]aya ba a yi duniya

 

A ~angaren sana’o’in gargajiya na Hausawa kuwa, wannan wa}ar ta fito da al’adun Hausawa na sana’o’in gargajiya, inda ya bayyana sana’o’i guda uku da cewa duk ma}era ke samar masu da kayan aiki, wa]anda za su gudanar da sana’arsu.

 

A ~angaren zamantakewa kuwa wadda ta shafi al’adar karuwanci [angoma ya ta~o wannan fanni

 

[angoma mai wannan wa}ar

Kyaun tafiya dawowa

Salamu alaikum tsofaffi

Ke tsohuwar karuwa

Tsohuwar gamshe}a

Ta san wurin cinzon yara

Gaba mai afuro mai ]an jigida

Mai sakaselin mai son keke

Banza ga ta ba ]uwaiwai ba mama

[an zane kamar sirdin jakkai

Idan dai yaro, yaro ne

Nemi yarinya daidai kai

Kiyayi neman tsofaffi

In yaro ya saba neman tsofaffi

Da shi da budurwa sai gaba

Ba zai yi auren farin ba.

 

Wannan wa}ar ta [angoma ta bayyana al’adar karuwanci na wasu matan Hausawa, inda ya nuna cewa, ba al’adar }ware ba ce, inda ya fito da siffar karuwa idan ta tsufa, yadda take kwaskwarima domin gyaran jikinta, da yadda suke yi wa }ananan yara dubaru, domin nemansu

 

Wa}o}in baka na Hausa sun ta~o kowane fanni na rayuwar  Bahaushe, kasancewar mawa}an suna duba ne da abin da ke faruwa a cikin al’umma, su }ulla wa}arsu a kansa. Wato sai al’ada ta yi aikinta sannan adabi ya samu damar kutsawa ciki ya kalato abin da ya sauwa}a ya baje hajarsa. 

Azancin Magana

Al’adun Hausawa da ke wanzuwa a cikin al’umma su suka haifar da tunanin amfani da su domin sarrafa harshe da nuna }warewa, domin isar da sa}o a cikin al’umma. Wa]annan al’adun su ne ruhin aukuwar wasu karuruwan magana da habaici da zambo da kirari da sauransu, da al’umma Hausawa ke tin}aho da su. Abin nufi a nan shi ne abubuwan da suka wanzu lokaci mai tsawo da ya gabata. Sanadiyar faruwar wa]annan abubuwa sai aka samu karin magana masu fayyace yadda abin ya faru a zahiri.

Misali. Wasu karin magana mai labari.

i.                    {unar ba}in wake.

ii.                  Fargar jaji.

iii.                Jifar ga~iyar |aidu

iv.                Lullu~in Taladan

{unar Ba}in Wake. Wannan karin magana ne mai labari, wanda ya adana tarihin abin da ya faru a Katsina shekaru da dama da suka wuce. A wannan lokaci ]iyan sarakuna, mutane suke hawa a cikin gari suna yawatawa a matsayin dawaki. Ba}in wake ya ]aukin alwashin duk lokacin da aka zo gare shi ba a sake hawan kowa, sai mutane suka yi mamakin haka da ya ce. Wata rana sai ]an sarki ya ce Ba}in wake zai hawa, aka ]ora ]an sarki aka yi ta yawo cikin gari, bayan an kammala, hanyarsu ta dawowa gida, sai Ba}in wake ya saki hanya, ana fa]in ina za shi ya }yale kowa ya nufaci galambar da ake }ona tama, hasa wuta ta kama sosai sai, ya fa]a, da shi da ]an sarki duk suka }one. Tun wannan lokaci ba a sake hawan mutum a matsayin doki ba a Katsina.

Karuruwan magana da suka shafi fannonin rayuwa daban-daban

Aure

i.                    [an ba }are gurguwa da aure nesa

ii.                  Ba ji ba gani aure kurma da makaho

iii.                Da niyya karuwa ta taka matar aure.

Wa]annan karuruwan magana sun fito da al’adar zamatakewar auren Hausawa, wadda ya ta~o fanni daban-daban. Wanda ya nuna cewa karuruwan maganar Hausawa na aure suna samuwa ne ta duban al’adun Hausawa na aure.

Haihuwa.

i.                    Uwa kwance ]iya kwance haihuwar guzuma.

ii.                  Abin nema ya samu matar malam ta haihi allo.

Wa]anan kuwa, sun duba al’dun haihuwa na Hausawa

Mutuwa.

i.                    Da sau}i an yi ba}o ya mutu.

ii.                  Gata ba ya hana mutuwa.

iii.                Ranka ya da]e ba ya hana a mutu

iv.                Idan baka mutu ba komai gani ka kai.

Wa]annan kuma, sun ta~o al’adun mutuwa na Hausawa, sun fito da yadda Hausawa suka ]auki mutuwa da yadda suka bayyana ta a cikin sha’anin zamantakewarsu ta yau da kullum.  

Zuben Gargajiya

A wannan ~angare ana bayar da labari ne da ya shafi tarihin al’umma, ko wani abu mai muhimmanci da ya shafi al’umma ko kuma a }aga labarin da ake son a saka darasi a ciki domin taimakon al’umma. Duk wa]annan suna samuwa ne ta amfani da abubuwan da ke faruwa na al’adun da ke zagaye da al’umma. Idan tarihi ne aka bayar, an duba abin da ya faru ne na gaskiya na zahiri a cikin al’umma, wanda yake daidai da al’adunsu, sannan adabi ya samu damar ]oko labarin ya bayyana shi kamar yadda yake. Idan kuma, }ir}irarran labari ne irin su tatsuniya da almara da sauran su. Ana }ir}ira su ne ta duba da al’adun da ke zagaye da al’umma a shirya labari wanda ke ]auke da darasi da nisha]i da fa]akarwa ga al’ummar Hausawa.

Sakamakon Bincike

Wannan bincike ya yi }o}arin fito da abubuwa kamar haka.

i.                    Wannan aikin ya ha}i}ance cewa sai da aka samu al’adun al’ummar Hausawa kafin samuwar adabinsu.

ii.                  An gano cewa adabi yana duba ne da al’dun da ke zagaye da al’umma, domin baje fasaharsa.

iii.                Binciken ya gano cewa adabi ba ya iya rayuwa sai da al’ada, domin idan babu al’ada babu adabi.

iv.                An gano akwai dangantaka mai }arfi tsakanin al’ada da adabi

Na]ewa

Al’ummar Hausawa suna tin}aho da al’dunsu da kuma adabinsu domin su ne suke tafiyar hanyoyin gudanar rayuwa, kuma bayan harshe da su ne Hausawa ke bugun gaba wajen, tabbatar da su a matsayin Hausawa, domin su ke bayyana Bahaushe a duk inda ya samu kansa. Domin dole ne ya aiwatar da wani abu da ya shafi al’adunsa ko adabinsa. 

Wannan aikin ya fito da abubuwa da dama da su taimaka a fahimce yadda al’ada take taka rawa wajen tafiyar da rayuwar al’ummar Hausawa, da kuma bayyana yadda adabi ke haska yadda rayuwar al’adar Hausawa take a idon duniya.

Manazarta

Adamu, M. U. (2011). Sabon Tarihin Asalin Hausawa: Kaduna. Espee Printing And Advertising

Ado, A. (2013). “Matsayin Sana’ar Gardanci A {asar Hausawa Jiya da Yau”. Cikin The   Deterioration of Hausa Culture, Jami’ar Umaru Musa ‘Yar’adua da Culture Bureau International Comference.

Aliyu, R. D. 2013.  Tsarin Ba}in Al’adu Ga Ta~ar~arewar Tarbiya da Zumunta a Zamantakewar Hausawa a Yau: The Deterioration of Hausa Culture: Katsina State History and Culture Bureau in Collaboration with Umaru Musa ‘Yar’adua University Katsina. Zaria: University Press.

Ahmad, A.D. 2013. Shirin Dun}ule da Ta~ar~arewar Al’adun Hausawa: The Deterioration of Hausa Culture: Katsina State History and Culture Bureau in Collaboration with Umaru Musa ‘Yar’adua University Katsina. Zaria: University Press

Ahmed, H. G. 2013. Ta~ar~arewar Al’adun Husawa a Wannan Zamani: Rawar da Kafofin Ya]a Labarai Suke Takawa Wajen Bun}asa Ko Ruguza Al’adun Husawa a Yau: The Deterioration of Hausa Culture: Katsina State History and Culture Bureau in Collaboration with Umaru Musa ‘Yar’adua University Katsina. Zaria: University Press.

Atuwo, A. A. (2009). “Ta’addanci a Idon Bahaushe: “Ya]uwarsa da Tasirinsa a  Wasu    {agaggun Rubutattun Labarun Hausa””. Kundin Digiri na Uku Sahsen Harsunan Najeriya, Sakkwato: Jami’ar Usmanu [anfodiyo.

Bunza, A.M. 2006. Gadon Fe]e Al’ada. Lagos: Tiwal Nigeria Ltd.

Ibrahim, S. M. (1983). Kowa Ya Sha Ki]a. Ibadan: Longman Nigerian Plc. Printed by Congo Press Ltd

Junaidu, I. Da ‘Yar’adua, T. M. (2007). Harshe Da Adabin Hausa A Kammale, Ibadan: Nazareth Press Ltd.

Shehu, I. 2013. Gudumuwar Wasannin Kwaikwayon Hausa Na Rediyo Wajen Bun}asa Al’adun Hausawa: Tsokaci Daga WasanninKwaikwayo Na Duniya Budurwa Wawa da Jami’ar Jatau Na Albarkawa: The Deterioration of Hausa Culture: Katsina State History and Culture Bureau in Collaboration with Umaru Musa ‘Yar’adua University Katsina. Zaria: University Press.

Sani, A.U da Gobir, Y.A (2021) Wasannin a {asar Hausa. Kaduna: Amal Printing Press.

Umar, M. B. (1987) Dangantakar Adabi da Al’adun Gargajiya: Triumph Publishing.

Yahaya, I.Y etal (1992) Darussan Hausa. Don Manyan Makarantun Sakandire. Littafi 1-3. Ibadan: University Press. 

Post a Comment

0 Comments