Ticker

6/recent/ticker-posts

Ta Fara Jinin Haila, Bata San Hukunce-Hukuncenta Ba

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Aslm, malam da fatan katashi lfy. Allah ya kara lfy da nisa kwana mai amfani. Mallam yarinya ta shekara sha uku ta fara jinin haila tun January bata sanar dani ba sai jiya da take complain na ciwon ciki, nake tambaya ta ko ta taɓa gani jini  sai ta fara gayamin da nake mata fada na rashin sanar dani sai tace ta gaya abbanta, Amma mlm ba abin da ta nuna mata game da tsarki, wannan lamari ya daga min hankali don Allah mlm ya zan yi game da ibada da tayi-tayi ba tsarki ga Azumi huɗu duk a rashin sani. wlh ban sani ba sai jiya.

𝐀𝐌𝐒A❗️

Zaku Zaunar da ita ne Sai Kuna Sanar da ita Abubuwan da Suka Wajaba Akanta. Domin a Yanzu ta Balaga. Da kuma Ka'idojin Jinin Haila da Abubuwan da Suke Nuna Alamun Ɗaukewar sa da kuma yadda ma Ake yin Tsarkin. Da yadda ya Kamata mace ta Zauna a daidai Lokacin da take Cikin Jinin. Ma'ana Ba Zata Ke Yin Sallah da Azumi ba, Matukar Tana Cikin Wannan Rashin Tsarkin.

Sannan a Nuna Mata Cewar Sallar da Bata yi ba, Ba zata Rama ba. Amma Zata Rama Azumin da Bata Yi ba. Kamar Yadda Haka Yake a Shari'a.

A irin Wannan Al'amarin Ana son Uwa ta Kulla Wani Kawance da Wata Babbar Alaka Tsakanin ita da ɗiyar ta. Ta yadda Zasu Kawar da Kunyar da take Tsakanin Su, ta ɓangaren Sanar da Ita Hukunce-hukuncen Shari'a, Wadanda Suka Wajaba Akanta. Domin Wani Nauyi ne da Allah ya Ɗora Musu Na ilimantar da 'Yayan su da ya Kamata Su Sauke. Kar Su Bar Su a Cikin Duhun Jahilci. Wanda kuma Hakan Ba zai Yiwu ba, Har Sai an Sami Wata Babbar Alaka Tsakanin Uwa da Ɗiyar ta.

Domin Haka Matan Sahabbai Suke Iya Cire Kunyarsu, Su Tambayi Manzon Allah Akan Abin da yake na Kunya Ne, gudun Fadawa Kuskure. Kuma Manzon Allah ya Basu Amsar da Suka Bukata. Har ma Nana Aisha Allah ya Kara Mata Yarda tana Cewa "MADALLA DA MATAN MADINA, KUNYA BA TA HANA SU SUYI TAMBAYA AKAN ADDINI". Da yawa Ma Malaman Islamiyya Suka Ji Kunyar Fitar da Irin Wannan Ilimin a Gaban Mata. Sabida Kunya Ko Kuma Suna Tunanin Kar Ayi Musu Wani Fassara na Daban.

Sabida Haka Kenan, Za ta Rama Azumin da tayi a Cikin Rashin Tsarki Kuma a Bisa Rashin Sani.

Rashin Sanin ne ya sa  Allah ba zai Kama ta da Lefin Hakan ba. Amma dai za ta Rama. Sallah Kuwa babu Ramuwa.

Allah ta'ala yasa mudace.

WALLAHU A'ALAM

Zauren Fatawowi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance Damu...

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://chat.whatsapp.com/GUq2GCCzlcdL6nknqLYYox

𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam 

Post a Comment

0 Comments