𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀❓
Assalamualaikum malam don Allah a taimake mu da wannan amsar, mace ce mijin ta ya sake ta saki 1 amma tana cikin jinin haila mun yi tambaya an ce mana bata saku ba shin ya matsayin sakin a Mace mai jinin haila a Shari'ance?
𝐀𝐌𝐒𝐀❗️
Wa Alaikis salaam wa
rahmatullahi wa Barkatuhu;
Eh shakka babu wannan
sakin dai bai yi ba, Saki ne wadda ake kiran sa da suna SAKIN BIDI'A, domin Faɗin Allahu Subhanahu Wa Ta'ala ya ce;
يَا أَيُّهَا النَّبِيُّ إِذَا طَلَّقْتُمُ النِّسَاءَ فَطَلِّقُوهُنَّ
لِعِدَّتِهِنَّ وَأَحْصُوا الْعِدَّةَ ۖ وَاتَّقُوا اللَّهَ رَبَّكُمْ ۖ
Ya kai Annabi! Idan za
ku saki mãtã, sai ku sake su ga iddar su, kuma ku ƙididdige iddar. Kuma ku bi Allah Ubangijin ku da
taƙawa. (At-Talaq Ayata 1).
Irin wannan sakin ya taɓa faruwa a zamanin Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wa
Sallam, a lokacin da Sayyidina Umar ya Umarci Ɗan sa Abdullahi Bn Umar A.S akan cewa ya saki
Matar sa, Sayyidina Umar bai gayawa Ɗan sa Abdullahi Bn Umar ga dalilin da ya sa ya ce ya Sake Matar sa ba,
shiyasa Malamai suka ce ba za a samu Ɗa kamar Abdullahi Bn Umar ba, haka nan ba za a samu Uba kamar Sayyidina
Umar ba.
Abdullahi Bn Umar bai
tambayi Mahaifin sa akan meyasa ka ce na sake Matana ba, haka shi ma Uban bai
gaya masa akan cewa ga dalilin da ya sa na ce ka sake Matar ka ba, kawai
Sayyidina Umar, Umarni ya ba shi ya ce ya sake Matar sa, kuma an tabbatar da
cewa Sayyidina Umar babu wani son zuciya ko wani abun a ransa wadda har ya sa
zai cewa Ɗansa ya saki
Matar sa, Abdullahi Bn Umar ya zo gaban Annabi ya gayawa Manzon Allah
Sallallahu Alaihi Wa Sallam cewa ga shi Babana ya ce ya ce na saki Matana?
Domin a lokacin Abdullahi Bn Umar ya qi amincewa akan ya saki Matar sa, don
haka ne ya zo gaban Annabi Sallallahu Alaihi Wasallam ya kawo karar Mahaifin sa
cewa ya ce ya saki Matar sa? sai Annabi Sallallahu Alaihi Wasallam ya ce ka
Sake ta, Domin Annabi Sallallahu Alaihi Wasallam ya tabbatar da cewa babu son
zuciya a tare da Sayyidina Umar da zai sa haka kawai ya cewa Ɗansa ya saki Matar sa ba
tare da wani dalilin ba, yanzu Annabi Sallallahu Alaihi Wasallam ne ya ce ya
Sake ta yanzu maganar ta wuce ta Mahaifin sa, a take Abdullahi Bn Umar ya koma
gida ya ce toh ya Sake ta. Abdullahi Bn Umar ya Koma gida ya cewa Matar sa toh
na Sake ki.
ALokacin Sayyidina Umar
yana Jin sa ya cewa Matar sa ya sake ta, sai Sayyidina Umar ya ce toh meyasa ba
ka Jira sai ta gama Jinin hailar ta ba? Ai ba a sake Mace alhalin tana cikin
jinin haila, toh sai Umar ɗin da kansa ya
je gaban Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wa Sallam ya ce ya Rasullah, Yaron nan
ya sake Matar sa alhalin tana cikin jinin haila bata gama ba, Sai Annabi
Sallallahu Alaihi Wasallam ya cewa Sayyidina Umar ka je ka ce masa ya mayar da
ita. Annabi Sallallahu Alaihi Wasallam ya ce sai ta gama wannan jinin hailar
nata tayi tsarki, ta sake yin wani Jinin haila na biyu a wani watan daban tayi
tsarki, toh daga wannan ne idan baya son ta, yana son su rabu shike nan sai ya
Sake ta idan kuma ya hakura shike nan sai a ci gaba da zaman Auren kawai tunda
ya chanja tunanin sa.
Gaskiyar magana shi ne
wallahi ana Kuskure sosai a gurin sakin mace dayawa daga cikin Mazãje sakin
mata kawai suke yi ba tare da sanin mene ne Hukuncin sakin ba, ba tare da sanin
cewa idan na saki matar nan a wannan halin mene ne matsayin sakin ba, ko ba a
kan Jinin haila ba, akwai abubuwa dayawa waɗanda Mazãjen suke yin su, ba su san cewa saki ba ne,
sa'annan akwai sakin da suke yi alhalin ba saki ba ne kuma a hakan wai Ka ji
mace ta bar gidan sa har tayi wani Auren, ana yin Kuskure sosai shiyasa ake
cewa ki Auri mai Addini da tsoron Allah kada ki biyewa soyayyar waje, kada ki
biyewa zuciyar ki, ki tsaya dakyau ki Auri mutumin da ya san Addinin Musulunci,
domin kada ku je kina zaman Aure alhalin kuwa Auren ku ya dade da Lalacewa,
kowacce Mace da za a ce tayi bayanin Yadda Mijin ya yake Furta wasu kalmomin
wallahi da sai ka ji cewa Auren su ya jima da mutuwa, haka kuma wani bawai
Kalmar saki ba ne amma an mayar da shi Kalmar saki, mace har ta bar gidan ta je
ta Auri wani alhalin da Auren ta akan wannan mijin na farko, yakamata idan ba a
san abu toh ayi tambaya Aure ba wasa ba ne wallahi.
Allah ya ce ku sake su
akan iddar su, Ma'ana a lokacin da ba su yin Jinin haila, bawai tana gama
wannan jinin hailar ne zaka sake ta ba, a'a sai ta sake yin wani Jinin ta gama
kafin ka sake ta, dalilin haka shi ne idan Namiji ya sake Mace tana cikin jinin
haila toh wannan an zalunce ta ne, zaluncin da akayi miki shi ne wannan jinin
da aka sake ki kina cikin yin sa, toh fa baya cikin Lissafi daga cikin abun da
za ki lissafa na iddar sakin ki, a maimakon kiyi Tsarki Ukku wato kiyi Jinin
haila na wata 1 ya ɗauke, ki sake
yin wani wata 1 ya ɗauke ki, sake
yin wani wata ya ɗauke, ya zama
Tsarki ukku ke nan ba? Toh yanzu sai kin yi tsarki 4 wato Jinin haila ya zo ya ɗauke har na tsawon wata 4 Kafin nan za ki gama iddar ki,
domin wadda aka Sake ki kina yin sa baya daga cikin lissafin iddar ki, kin ga ke
nan an tsawaita miki iddar ki, kin ga wannan ai zalunci ne sosai. Allah ya ce
kada ku sake suna cikin jinin haila idan kun yi haka toh Kun zalunce su.
Sabida haka Haramun ne
Miji ya Sake Matar sa alhalin tana cikin jinin haila, idan kuma ya riga yayi
sakin indai bawai saki ukku ba ne, toh dole ne a tilasta shi sai ya dawo da ita
tayi abun da muka ambata a sama kafin nan zai sake ta, idan an tilasta shi ya
dawo da ita, toh yanzu matsala ta 2 za ta taso, shin sakin da aka yi miki a
cikin Jinin Hailar ki yayi ko bai yi ba?
A Mazahbin Imam Malik,
Abu Hanifa, Imam Shafi'i, da kuma Ahmad BN Hambali Allah ya Kara Yarda gare su
dukkan su suka ce; sakin yayi. Sai aka ce toh ya akayi aka san cewa yayi ko bai
yi ba? Sai aka ce ai shi Abdullahi Bn Umar ɗin shi ne aka samu ake tambayar sa cewa wai Matar ka da
aka Sake ta tana cikin jinin haila toh wannan sakin an Sa shi a cikin Lissafin
saki ne ko kuma ba a sa shi ba? Abdullahi Bn Umar ya ce Eh an sa wannan sakin a
cikin Lissafin saki. Amma wasu malaman suka ce ai mun tambaye shi ya ce ba a sa
shi ba, sai malaman suka rabu gida 2, waɗannan suka ce mu
mun tambaye shi ya ce an sa wannan sakin a cikin Lissafin saki, waɗannan kuma suka ce a'a mu mun tambaye shi ya ce ba a sa
wannan sakin a cikin Lissafin saki ba.
Sai aka ce toh yanzu a
zo ayi Kuri'a a tantance domin a gane, sai aka ce malaman da aka ce sun rawaito
cewa an sa wannan sakin na Abdullahi Bn Umar a cikin Lissafin saki su waye ne?
Sa'annan waɗanda suka rawaito cewa
ba a saka wannan sakin a cikin Lissafin saki ba su waye ne su ma? Sai aka ware
su gefe aka lissafa adadin Malaman, waɗannan ma aka
ware su gefe aka lissafa su, sai aka ga cewa malaman da suka ce lallai
Abdullahi Bn Umar ya sa wannan sakin a cikin Lissafin saki Manyan Malamai ne
sun fi karfi sosai a gurin ilmi akan wannan Janibin, idan za a bi yawan karatun
su da tarjibin su, toh dole ne a rinjayar da Yawan karatun su, dole ne a sa shi
akan cewa an sa wannan sakin na Abdullahi Bn Umar a cikin Lissafin saki. Wadda
shi ne Albani a cikin Littafin sa na Rawahul Galib Mujalladi na 6, ya tafi akan
cewa lallai wannan sakin yayi kuma yana cikin Lissafin saki. Kuma Sheick ibnu
Baas da su Usamin sun tafi akan cewa sakin yayi, kuma Suma suna bin Mazhabar
Hambali ne, amma sun bar shi suka ce wannan sakin Haramun ne yin sa kuma idan
an yi sa, toh bai yi ba kawai kuma sakin za a lissafa shi a matsayin saki ne.
Shiyasa ake ruda Yan Uwa
Mata akan cewa sakin yayi ne ko bai yi ba, amma idan kina da ilmin ki, shima
Mijin ki yana da ilmin sa, toh babu wani abun da zai rude miki, niyya ce Mijin
ki ya riga da yayi niyyar sakin ki, kuma har ya Sake, amma kuma sai ya samu
bayani akan cewa sakin bai yi ba domin ga abun da Allah da Manzon Allah
Sallallahu Alaihi Wasallam suka ce akan sake Mace tana cikin jinin haila, toh
idan misalin dãman ya taɓa miki saki 1
kafin na Jinin Hailar, toh yanzu zakiyi lissafi akan matsayin saki ne, don haka
zai dawo da ke sai kin gama wannan tsarkin kin sake yin wani ya ɗauke sai ya Sake ki, idan kuma ya Sake fa? toh shike nan
saki Ukkun sa sun cika yanzu, yanzu babu ke babu shi har sai kin sake Auren
wani Namijin daban kuma Sahihin Aure wannan miji na biyun ya Sake ki, toh idan
yana so sai ya dawowa ya Aure ki. Idan kuma dãman ya taɓa miki saki 2 kafin na jinin hailar, toh ba za a tilasta
masa ya dawo da ke ba kawai sakin yayi amma yayi abun da ya Saɓawa fadin Allah da Manzon Allah Sallallahu Alaihi
Wasallam.
Idan kuma wannan sakin shi
ne na farko dãman bai taɓa Sake ki ba sai
akan wannan, toh shike nan yanzu dole ne a tilasta shi ya dawo da ke ki gama
wannan jinin hailar naki a gidan sa bayan kin gama wannan, sai ki Jira wani
watan idan ya zo, sai ki sake yin wani Jinin hailar karo na biyu, toh idan
wannan ya ɗauke shike nan sai ya
Sake ki, idan Kuma ya chanja tunanin sa ya ce ya fasa sakin ki shike nan yayi,
amma yanzu kina matsayin Matar da mijin ta ya sake ta saki 1 ne, idan kuma kin
gama wannan jinin sai ya ce ya Sake ki, toh yanzu kina da saki 2 a gurin sa,
saura masa Igaya 1, idan kafin ki gama iddar ki ya zo ya ce ki dawo ya mayar da
ke shike nan, idan kuma bai faɗa ba har kika
gama iddar ki toh shike nan kin fita daga Matar sa, ko ya sake dawowa akan yana
son ki toh sai da sabon kuɗin Sadaki.
Sabida haka mata wajibi
ne gare ku a tashi a nema ilmin Addini sosai kada ki je kina yin abu alhalin
Kuskure ne idan an sake Mace a irin wannan, toh ki tabbatar da cewa sakin bai
yi ba dole ne ya dawo da ke ko baya so sai kin yi abun da Shari'ar Musulunci ya
ce kafin nan ya Sake ki. Allah ya tsare ya sharya Ameen Ya Yayyu Ya Qayyum 🤲🏽.
Wallahu A'alamu.
Zauren Fatawoyi Bisa
Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance damu cikin wannan group domin Fadakarwa...
Hukuncin Matar Da Aka Sake Ta Tana Cikin Haila
𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀❓
Assalamu alaikum Mallam. Mace ce mijinta ya sake ta
tana haila. Dan Allah jini nawa zatayi ta kare iddah. Na gode.
𝐀𝐌𝐒𝐀❗️
Wa alaikumus salam wa rahmatullahi wa barakatuhu.
Akwai saɓanin Malamai game da sakin da aka yishi alhali
matar tana cikin jinin haila. Kasancewarsa saki ne irin na bidi'ah. Wasu 'yan
kaɗan daga cikin malamai
sunce sakin bai afku ba.
Amma magana mafi karfi itace wacce mafiya rinjayen
malaman musulunci suke kai. Ita ce cewarsu sakin ya afku, wato ya yiwu. Duk da
cewar saki ne na bidi'ah. Acikin malaman dake kan wannan fahimtar akwai Maluman
Fiqhu na Mazhabobin nan huɗu wato
Imam Malik, Abu Hanifah, Imam Shafi'iy da Imamu Ahmad (Allah ya rahamshesu).
Game da siffar yadda zatayi kirgen iddarta kuwa,
shima akwai saɓanin
Malamai tun daga zamanin sahabban Annabi ﷺ. Wasu sun ce ana yin kirgen ne bisa adadin
jini, wasu kuma suka ce bisa adadin
tsarkin da aka samu abayan zuwan jinin.
To amma idan kika ɗauki fatawar Maluman da suka ce ana yin
kirgen ne bisa adadin tsarkin da aka samu bayan jini, to zaki fara kirgen ne
bayan kammala wannan jinin da kike ciki.
WALLAHU A'ALAM.
Zauren Fatawowi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku
kasance Damu...
𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒��𝐏𝐏👇
https://chat.whatsapp.com/JoWs3feDfdyGE9yBsa1RSC
𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇
https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi
𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177
ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ
**************************
Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.