Mafarkin Macizai Da Kare

    TAMBAYA (13)

    Assalamu Alaykum malam an tashi lpy dan Allah malam inaso a daure a amsa min tabayoyina wllhy nasha tura tambaya amma ba taba amsa min ba ngd

    Tambaya ta farko malam nakai shekara hudu da aure inada yarinya 1 amma malam bansan dadin aure ba hatta sha’awa ma ban santaba sannan wani lokacin inajin zafi idan muna saduwa da mijina wani lokacin kuma idan nayi mafarkin ana sadauwa dani nakanji dadin haka shine nakeso nasan mi yake kawo hakan nagode

    Tambaya ta biyu malam ina yawan yin mafarkin macizai amma basa yimin komai kawai zan gansu dayawa ne Sosai sannan inayin mafarkin anbata min guri da kashi nayi ta wankewa amma baya wankuwa sai mafarkin kare yana bina nida yarinta amma kafin na farka ina illatar da Karen dan dakyar yake motsawa dan Allah malam ka amsamin cikin ilimin da ubangiji yayi maka Nagode

    AMSA

    Kamar yanda muka san cewar kowacce cuta tanada magani kuma babu wani abu da zai gagari Allah SWT. A shawarce kije Islamic chemist kiyi musu bayani in sha Allahu za a samu maganin da ya dace da matsalarki. Sannan kuma fassarar mafarkin saduwa kamar yanda Imam Muhammad Ibn Seerin (Dalibin Imam Malik, Allah ya jikansu baki daya) ya ce: Mafarkin mace tana saduwa da namiji na nufin fadawa tarkon zunubi, idan mara lafiya yayi mafarkin yana saduwa da mahaifiyarsa to mutuwarsa kenan saboda anan mahaifiyar tana nufin kasar da aka halicceshi, haka kuma mafarkin saduwa na nufin bashi ko kuma samun sauqin rayuwa, mafarkin saduwa da karuwa na nufin son duniya ko kuma samun ribar kasuwanci, mafarkin saduwa da macen Aljannah (Hurul Ayn) na nufin zurfin addini da tsarkin ruhi

    Mafarkin kare na nufin mutum mai yawan aikata zunubbai, ganin kare na nufin mace mai girman kai wadda take tareda mutane masu duqufa akan sabon Allah. Fada da kare na nufin son duniya. A takaice dai mafarkin kare yawanci abune mara kyau indai ba mafarkin dan karamin farin dan kwikwiyoba wanda yakeda alaqa da haihuwar yaron da za a so kuma zai taso a matsayin nagari

    Mafarkin kashi yana nufin kudi, yin kashi akan gado na nufin sakin aure, yin tafiya akan kashi na nufin wahala da kunci, kashi a mafarki na nufin kudi, boyayyen sirri, tafiya, fada, waraka daga cuta, mummunan tunani, waswasi, shaawa da yarda. Jin warin kashi a mafarki na nufin bashi, aiki fiyeda kima, bari ga mai ciki. Ganin kashin mutum a mafarki na nufin kusantar bala'i, bude kasuwance.

    Mafarkin macizai na nufin gaba tsakanin maqota, sirikai ko kuma yaya. Idan maciji ya hadiye mutum a mafarki na nufin mutum zai samu wani shahararren muqami. Bakin maciji na nufin qaqqarfan maqiyi, farin maciji na nufin rarraunan maqiyi. Kashe maciji na nufin yin aure. A takaice dai yin mafarkin maciji ko gansheka na nufin kishi, hassada, yaudara, damfarar mutane, saba alqawari da kuma tsananin qiyayya

    SHARHI

    Idan akwai hoto wanda ake ratayawa a bango a gidan da kike (na mutum ko na dabba) to a cireshi ko kuma a juyashi saboda Annabi SAW ya ce: "Mala'ikun rahama basa shiga gida wanda akwai kare ko kuma sura (hoto)"

    (Sahihul Bukhari 3543)

    Sannan kuma ki dage da adhkar na safiya da maraice saboda sharrin maqiya da mahassada

    Sannan kuma a dage da addu'ar Allah ya kauda sharrin da mafarkin ya kunsa domin kuwa an karbo daga Abu Hurairah RTA, Annabi SAW ya ce: "Babu abin da yake canza qaddara sai addu'a"

    Tirmidhi 3573

    Subhanakallahumma wabi hamdika, ash-hadu anla ilaha illa anta, astaghfiruka wa'atubi ilay

    Amsawa:

    ✍️Usman Danliti Mato Usmannoor_As-salafy)

    ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

    **************************

    Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

    Question and Answers in Islam

    No comments:

    Post a Comment

    ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

    HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.