Ticker

6/recent/ticker-posts

Shin Ya Hallata Mace Ta Saka Muryarta Da Karatun Alkur'ani Acikin Group?

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Assalaamu Alaikum Wa Rahmatul Laah. Akwai wani group na social media da a ciki members suke tura muryarsu da karatun Alqur’ani. To ko ya halatta mace ta saka nata muryar karatun, kasantuwar yawancin maza ne a group ɗin waɗanda kuma ba muharramanta ba?

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

Wa Alaikumus Salaam Wa Rahmatul Laahi Wa Barakaatuh.

Allaah Ubangijin Halittu dai cewa ya yi:

...فَلَا تَخْضَعْنَ بِالْقَوْلِ فَيَطْمَعَ الَّذِي فِي قَلْبِهِ مَرَضٌ وَقُلْنَ قَوْلًا مَعْرُوفًا ٢٣۝

Kuma kar ku riƙa lanƙwasa murya da Magana, sai wanda akwai cutar munafunci a zuciyarsa ya yi ɗammani. Amma dai ku faɗi magana sananniya a shari’a. (Surah Al-Ahzaab: 32).

Wannan ayar ita ce madogarin waɗansu malamai a wurin hana mace ta bayyana muryarta ga maza, hatta ma a wurin sallar da take yi ga Ubnagijinta a cikin ɗakinta!

Amma a wurin waɗansu malaman, wannan ba hujja ce gamsasshiya ba. Domin a fili ya ke ko a cikin ayar cewa: Allaah ya halatta musu faɗin magana sananniya da ta dace da shari’a (Qaulun Ma’aruuf). Kuma abu ne sananne cewa: Babu wata magana sananniya a shari’a da ta kai Alqur’ani balle ta fi shi.

A shari’a dai ba a hana mace bayyanar da karatunta na Alqur’ani ba: Ko a cikin sallah ko ba a cikin sallah ba, kamar a makaranta a gaban malamanta da sauran ’yan uwanta ɗalibai. Allaahumma! Sai dai ko in an samu wani dalili sahihi kuma sarihi wanda ya hana ta haka ɗin.

Bayan wannan, to ko zai yiwu a ƙyale mace - musamman a irin wannan zamanin da yananyin - ta saki muryarta na karatun Alqurani a cikin dandalin da ke ƙunshe da mazajen da ba ta san su ba, waɗanda kuma ba muharramai ne a gare ta ba?

A gaskiya bayan nazari, abin da na gamsu da shi a yanzu dai shi ne: Ba na ganin halaccin yin hakan ga mace mai mutunci da imani, saboda dalilai kamar haka:

1. Ɗaga muryoyin maza da mata da cakuɗuwarsu a wuraren ayyukan addini kamar na sallah a masallatai da wuraren ɗaukar karatu a makarantu, ba abu ne da ya shahara a cikin magabatan wannan al’ummar ba. Balle ko a iya cewa an samu wani abin yin ƙiyasi.

2. Haka kuma a zamunan farko, kodayake an samu waɗansu tsirarun mata masana ilimi sun zauna domin bayar da karatu da ilimi ga al’ummar da suka haɗa da mazaje ta bayan shamaki, sai dai hakan ba zai zama wani ma’auni a nan ba, domin dalilai kamar haka:

(i) Tsarkin zamunan da tsantsanin jama’a da kiyaye dokokin shari’a a cikin zamunnan baya sun sha bamban da na yau. Shiyasa abin da aka yi shi aka gama lafiya lau a cikin waɗancan zamunnan, ba zai yiwu a yau a buɗe masa ƙofa ba.

(ii) Babu buƙata ko larura ta sharia da ta sa sai mace ta tura muryar karatun ta a cikin irin waɗannan dandalolin. Don haka yin shi ba wajibi ne ko mustahabbi ba. Ba kuma za a ce halal ne ba, tun da yana iya haifar da waɗansu matsalolin da ba alheri ba.

(iii) Idan dai Annabi (Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallam) ya hana wata mace ta siffata wa wani namiji siffar wata macen da ba muharramarsa ba domin tsoron buɗe ƙofar ɓarna, to ina kuma ga sake masa muryarta a tare da shi, ta yadda yake iya saurare a duk lokacin da ya ga dama?

Don haka a fahimtata, gara mace mai mutunci ta nisanci shiga irin wannan group ɗin kawai. Ko buɗe group na mata zalla a kan hakan ma yana da na shi matsalolin. Domin mutane ba su iya kiyayewa da tsarewa a kan ƙaidojin da masu buɗe group ɗin suka shimfiɗa, kamar yadda ake ji da gani a yau a cikin jama’armu. Shiyasa zai yi wuya a hana wani namiji yin kutse a cikin matan ko da kuwa ta amfani da sunan mace ma!

Mafi kyau dai baiwar Allaah saliha ta mayar da himma da ƙoƙarinta wurin tsarkake ayyukanta gaba-ɗaya ga Allaah Mabuwayi Mai Girma shi kaɗai kawai. Ta nisanci riya da sum’ah da sauran hanyoyi masu lalatawa da rushe ayyukan bayin Allaah. Ta damu da karantar da yara da ’ya’yanta da danginta da sauran makusanta a keɓe a cikin gidanta kawai.

Allah ya datar da mu ga abin da yake so kuma yake yarda da shi.

WALLAHU A'ALAM

Sheikh Muhammad Abdullaah Assalafiy

Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah.

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://chat.whatsapp.com/IQUc0RxgCwA3JFiEKl8j5E

𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

Question and Answers in Islam

Post a Comment

0 Comments