𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀❓
Assalaamu Alaikum Wa Rahmatul Laah. Menene
hukuncin kamewa da sarawa ga manyan malamai da shugabannin addini da waɗansu ’yan agaji suke yi don nuna girmamawa
gare su?
𝐀𝐌𝐒𝐀❗️
Wa Alaikumus Salaam Wa Rahmatul Laahi Wa
Barakaatuh.
Matsalar ƙamewa da sarawa ga shugabanni wadda aka fi
sani da gaisuwar sojoji a asali ba matsala ce ta aqeedah ko ibadah kai-tsaye
ba, amma dai wani abu ne da za a iya cewa yana da alaƙa da tsarin rayuwa ta
hulɗa a
tsakanin jama’a. Ta wannan fuskar ce waɗansu malamai kan iya kafewa a kan cewa, shi ba
laifi ba ne. Musamman dayake ba su ga wani nassi ƙarara a kan hana aikata
shi ba!
Amma kuma idan aka kalli cewa, asalin waɗannan abubuwan: Tun daga dinkin kayan na
agaji, da yadda ake sanya su, da tsarin horar da masu amfani da su, da faretin
da suke yi da sauransu, duk daga kafirai ne aka koyo su, ba daga tsarin
musulmin yau ba ne ma, balle magabatan wannan al’ummar ta farko. Koyi da
kafirai kuwa a cikin duk wani abin da ya keɓance su na addini ko rayuwa abin ƙyama
ne, saboda nassoshi da suka zo a kan hakan, kamar inda Allaah yake cewa:
ثُمَّ جَعَلۡنَـٰكَ عَلَىٰ شَرِیعَةࣲ مِّنَ ٱلۡأَمۡرِ فَٱتَّبِعۡهَا وَلَا تَتَّبِعۡ أَهۡوَاۤءَ ٱلَّذِینَ لَا یَعۡلَمُونَ
Sai kuma muka ɗora ka a kan wata shari’a daga umurni, don
haka sai ka bi ta, kuma kar ka bi sha’awar ran waɗanda ba su sani ba. (Surah Al-Jaathiyah:
18)
Wurin fassara wannan Ayar, Shaikhul Islaam Ibn
Taimiyah (Rahimahul Laah) a cikin Iqtidaa’u Siraatal Mustaqeem Mukhaalafatu As-Habal
Jaheem, ya ce:
وَقَدْ دَخَلَ فِي ( الِّذِينَ لَا يَعْلَمُونَ ) كُلُّ مَنْ خَالَفَ شَرِيعَتَهُ . وَ ( أَهْوَاؤُهُمْ ) : هُوَ مَا يَهْوُونَهُ وَمَا عَلَيْهِ الْمُشْرِكُونَ مِنْ هَدْيِهِمُ الظَّاهِرِ ، الَّذِي هُوَ مِنْ مُوجِبَاتِ دِينِهِمُ الْبَاطِلِ وَتَوَابِعِ ذَلِكَ فَهُمْ يَهْوُونَهُ . وَمُوَافَقَتُهُمْ فِيهِ اتِّبَاعٌ لِمَا يَهْوُونَهُ
Duk wanda ya saɓa wa Shari’ar Annabi (Sallal Laahu Alaihi
Wa Alihi Wa Sallam) ya shiga cikin (waɗanda ba su sani ba). Sannan kuma (Sha’awar ransu)
ita ce: Abubuwan da suke sha’awar sa, da kuma irin abin da mushirikai suke a
kansa na ɗabi’u
da al’adunsu na fili, wanda kuma yake cikin abin da addininsu na ƙarya
ya ɗora
musu shi, da sauran abubuwan da suke bin bayan waɗannan ɗin duk abubuwa ne da suke sha’awarsa.
Dacewa da su a cikin hakan kuma biyayya ne ga abin da suke sha’awar sa.
Kuma a cikin hadisin Abdullaah Bn Umar (Radiyal
Laahu Anhumaa) Manzon Allaah (Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallam) ya ce:
« وَمَنْ تَشَبَّهَ بِقَوْمٍ فَهُوَ مِنْهُمْ »
Kuma duk wanda ya kamantu da waɗansu mutane, to kuwa yana cikin su. (Sahih
Al-Jaami’: 2831)
A cikin littafin Jilbaabul Mar’atil Muslimah
Al-Imaam Al-Albaaniy (Rahimahul Laah) ya kawo nassoshin da suka hana kamantuwa
da kafirai a cikin babuka da dama na addinin musulunci, kamar a babin Sallah,
da Jana’iza, da Hajji, da Azumi, da Yanka, da Abinci, da Tufafi da Kwalliya, da
Ladubba da Al’adu, da sauransu. Daga nan ne kuma sai ya ce (shafi: 206):
فَثَبَتَ مِمَّا تَقَدَّمَ أَنَّ مُخَالَفَةَ الْكُفَّارِ ، وَتَرْكَ التَّشَبُّهِ بِهِمْ مِنْ مَقَاصِدِ الشَّرِيعَةِ الْإِسْلَامِيَّةِ الْعُلْيَا ، فَالْوَاجِبُ عَلَى كُلِّ مُسْلِمٍ رِجَالًا وَنِسَاءً أَنْ يُرَاعُوا ذَلِكَ فِي شُؤُونِهِمْ كُلِّهَا ، وَبِصُورَةٍ خَاصَّةٍ فِي أَزْيَائِهِمْ وَأَلْبِسَتِهِمْ ، لِمَا عَلِمْتَ مِنَ النُّصُوصِ الْخَاصَّةِ فِيهَا
Ya tabbata daga abin da ya gabata kenan cewa: Saɓa wa kafirai da barin kamantuwa da su yana
daga cikin manyan manufofin Shari’ar Musulunci masu girma. Don haka wajibi a
kan dukkan musulmi mazansu da mata shi ne: Su kula da hakan a cikin dukkan
sha’anoninsu, musamman ma a cikin shigansu da tufafinsu, saboda abin da ka riga
ka sani na nassoshi keɓantattu
da suka zo a kan hakan.
Sannan kuma wani abin da ya sa shari’a ta hana
kamantuwa da kafirai a cikin ayyuka da ɗabi’unsu na a fili a zahiri shi ne: Kamantuwa da
su a zahiri kan kai ga kamantuwa da su a ɓoye a cikin zuciya. Shiyasa wanda ya sanya tufafi
irin na malamai ko sarakuna ko kuma na sojoji sai ya riƙa jin zuciyarsa tana ba
shi tunanin takawa da yin magana irin nasu, kamar dai yadda Shaikhul Islaam
(Rahimahul Laah) ya yi bayani a wani wurin a cikin Al-Iqtidaa’u:
Kuma abin da yake nuna gaskiyar wannan alaƙar a
tsakanin ɓoye da
bayyane shi ne hadisin Saheeh Muslim (1007) daga An-Nu’uman Bn Basheer (Radiyal
Laahu Anhu) cewa: Manzon Allaah (Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallam) ya
kasance yana daidaita sahuhuwanmu, har kamar yana daidaita sillen kibau ne. Har
sai da ya ga mun fahimta kuma mun ɗauki
hannu. Sai watarana ya fito ya tsaya har ya yi shirin yin kabbara sai ya ga
wani mutum ƙirjinsa ya fito daga cikin sahu, sai ya ce:
« عِبَادَ اللَّهِ لَتُسَوُّنَّ صُفُوفَكُمْ أَوْ لَيُخَالِفَنَّ اللَّهُ بَيْنَ وُجُوهِكُمْ ».
Bayin Allaah! Ko dai ku daidaita sahuhuwanku ko
kuma lallai Allaah ya sassaɓa a
tsakanin fuskokinku.
A cikin wata riwaya kuma a cikin Al-Musnad: 18927
ya ce:
« أَقِيمُوا صُفُوفَكُمْ - ثَلاَثاً - وَاللَّهِ لَتُقِيمُنَّ صُفُوفَكُمْ أَوْ لَيُخَالِفَنَّ اللَّهُ بَيْنَ قُلُوبِكُمْ »
Ku tsai da sahuhuwanku - sau uku. Wallahi! Ko dai
ku tsai da sahuhuwanku ko kuma Allaah ya sassaɓa a tsakanin zukatanku.
Da wannan yana nuna cewa saɓani a fili a zahiri ko da a wurin daidaita
sahun sallah ne yana kai wa ga saɓani a
cikin zukata. Wannan ya nuna kenan ayyukan gaɓoɓi a fili suna da tasiri a kan ayyukan da suke a ɓoye.
Allaah ya shiryar da mu.
Ta wata fuskar kuma a iya cewa: Gaisuwa da girmama
manya ko shugabanni wani abu ne da kowaɗanne mutane suke da yadda suke yin ta a al’adarsu.
Kwaɓe
takalma da rusunawa da sadda kai ƙasa a wurin Hausawa da Fulani ita ce hanyar
girmama na-gaba. Kamar yadda yin zaman tahiya da duƙawa kusa da ƙasa
yake zama hanyar da fadawa suke girmama sarakuna a fadojin ƙasashen
hausa. Su kuwa Yarbawa girmama manyansu a al’ada ita ce su kwanta miƙe
ruf-da-ciki.
Shi kuma musulunci sai ya zo da yin sallama da
musafaha kawai, kuma ya hana sauran gaisuwayin da ba su ba. Al-Imaam Abu-Daawud
(2142) ya riwaito daga Qais Bn Sa’ad (Radiyal Laahu Anhu) wanda ya tafi ƙasar
Farisa kuma ya ga yadda suke yin sujada wurin girmama shugabanninsu da
manyansu. Da ya komo sai ya gaya wa Annabi (Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa
Sallam) hakan sannan ya ce:
فَأَنْتَ يَا رَسُولَ اللَّهِ أَحَقُّ أَنْ نَسْجُدَ لَكَ
Manzon Allaah! Haƙiƙa kai kafi cancantar a
yi maka sujada don girmamawa.
A ƙarshe dai ya ce masa:
« فَلاَ تَفْعَلُوا لَوْ كُنْتُ آمِرًا أَحَدًا أَنْ يَسْجُدَ لأَحَدٍ لأَمَرْتُ النِّسَاءَ أَنْ يَسْجُدْنَ لأَزْوَاجِهِنَّ لِمَا جَعَلَ اللَّهُ لَهُمْ عَلَيْهِنَّ مِنَ الْحَقِّ »
Kar ku yi hakan. Idan da zan umurci wani ɗaya ya yi sujada ga wani ɗaya, to da na umurci mata ne su yi sujada
ga mazajen aurensu, saboda abin da Allaah ya ɗora a kansu na haƙƙin. (Al-Albaaniy a
cikin Sahih Abi-Daawud: 1857 ya inganta wannan maganar ta ƙarshe, musamman dayake
tana da shawaahid kamar riwaiyar Abu-Hurairah da At-Tirmiziy ya hassana ta kuma
Ibn Hibbaan da Al-Haakim da Az-Zahabiy suka sahhaha ta daga Hadisin Mu’azu).
Ka ga a nan Annabi (Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi
Wa Sallam) bai goyi bayan yin koyi da al’adar waɗanda ba musulmi ba a wurin gaisuwa da
girmama manya.
Kuma a fili ƙarara Annabi (Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi
Wa Sallam) ya hana mu koyi da waɗanda
ba musulmi ba a wurin gaisuwa, kamar inda ya ce:
« لَيْسَ مِنَّا مَنْ تَشَبَّهَ بِغَيْرِنَا لاَ تَشَبَّهُوا بِالْيَهُودِ وَلاَ بِالنَّصَارَى فَإِنَّ تَسْلِيمَ الْيَهُودِ الإِشَارَةُ بِالأَصَابِعِ وَتَسْلِيمَ النَّصَارَى الإِشَارَةُ بِالأَكُفِّ »
Ba ya tare da mu duk wanda ya kamantu da waɗanda ba mu ba. Kar ku kamantu da Yahudawa
da Nasara. Domin gaisuwar Yahudawa ta yin nuni da yatsu ne, kuma gaisuwar
Nasara nuni ne da tafukan hannu. (At-Tirmiziy ya riwaito shi kuma Al-Albaaniy
ya hassana shi a cikin: As-Saheehah: 2194).
Kuma An-Nasaa’iy a cikin Amalul Yawm Wal Lailah:
340 ya riwaito daga hadisin Jaabir cewa Manzon Allaah (Sallal Laahu Alaihi Wa
Alihi Wa Sallam) ya ce:
« لَا تُسَلِّمُوا تَسْلِيمَ الْيَهُودِ وَالنَّصَارَى ، فَإِنَّ تَسْلِيمَهُمْ بِالْأَكُفِّ وَالرُّؤُوسِ وَالْإِشَارَةِ »
Kar ku yi sallama irin sallamar Yahudawa da
Nasara. Domin sallamar su da tafukan hannuwa ne, da kai, kuma da nuni.
(Al-Albaaniy a cikin As-Saheehah ya kawo shi a ƙarƙashin hadisi mai lamba:
1783)
Sannan kuma a cikin Al-Adabul Mufrad (1004)
Al-Bukhaariy ya kawo da isnadi sahihi maganar ɗaya daga cikin manyan Taabi’ai watau
Ataa’u Bn Abi-Rabaah (Rahimahul Laah) cewa:
كَانُوا يَكْرَهُونَ التَّسْلِيمَ بِالْيَدِ ، أَوْ قَالَ : كَانَ يَكْرَهُ التسليم باليد
Sun kasance suna ƙyamar yin gaisuwa da
hannu kawai, ko kuma ya ce: Ya kasance yana ƙyamar yin sallama da
hannu.
Wannan shakkar ba matsala ba ce: Riwayar farko
tana nufin malaman Ataa’u, watau Sahabbai kenan, duk suna ƙyamar hakan. Riwaya ta
biyu kuma tana nuna shi kansa Ataa’un ne yake ƙyamar hakan. Don haka, kowacce ce ma dai hujja ce,
in Shã Allãh.
Sannan kuma ƙungiyoyi da malaman musulunci a duniyar
yau sun bayar da fatawar rashin halaccin irin wannan gaisuwar. Kamar
Al-Lajnatud Daa’imah:
1/235-236, da Fataawaa As-shaikh Ibn Jibreen, da As-Shaikh Saalih Al-Fauzaan,
da As-Shaikh Uthaimeen a cikin wani shirin rediyo: Liqaa’ul Baabil Maftuuh, sai kuma As-Shaikh
At-Tuwaijiriy a cikin littafinsa: Ad-Durarus Saniyyah Fil Kutubin Najadiyyah,
inda ya ce:
وَمِنَ التَّشَبُّهِ بِأَعْدَاءِ اللهِ تَعَالَى : الْإِشَارَةُ بِالْأَصَابِعِ عِنْدَ السَّلَامِ ، وَكَذَلِكَ الْإِشَارَةُ بِالْأَكُفِّ مَرْفُوعَةً إِلَى جَانِبِ الْوَجْهِ ، فَوْقَ الْحَاجِبِ الْأَيْمَنِ ، كَمَا يَفْعضلُ ذَلِكَ الشُّرَطُ وَغَيْرَهُمْ ، وَكَذَلِكَ ضَرْبُ الشُّرَطِ بِأَرْجُلِهِمْ عِنْدَ السَّلَامِ . وَيُسَمُّونَ هَذَا الضِّرْبَ الْمُنْكَرَ وَالإِشَارَةَ بِالْأَكُفِّ : التَّحِيَّةُ الْعَسْكَرِيَّةَ ، وَهِيَ تَحِيَّةٌ مَأْخُوذَةٌ عَنِ الْإِفْرِنْجِ وَأَشْبَاهِهِمْ مِنْ أَعْدَاءِ اللهِ تَعَالَى ، وَهِيَ بِالْهَزْءِ وَالسُّخْرِيَةِ أَشْبَهُ مِنْهَا بِالتَّحِيَّةِ
Kuma yana daga cikin kamantuwa da maƙiyan
a'Allaah Ta’aala:
Yin nuni da yatsu a wurin gaisuwa. Haka kuma yin nuni da tafukan hannu a ɗaga su zuwa gefen fuska sama kaɗan da girar idon dama, kamar dai yadda
jami’an tsaro da waɗanda
ba su ba ma suke yi. Haka kuma buga ƙafafun da suke yi a wurin gaisuwar. Wannan
bugawar da ta ke mummunar abu, da yin nuni da tafukan shi suke kira wai
gaisuwar sojoji. Ita kuwa gaisuwa ce da aka kwafo ta daga Turawan Ingilishi da
masu kama da su daga cikin maƙiya Allaah Ta’aala. Kuma ta fi kama da izgili da wulaƙanci fiye
da zama gaisuwan girmamawa.
Idan dai har musulunci yana da ta-cewa a irin
wannan wurin kamar yadda muka gane, to fa bai halatta wani musulmi ya kawar da
kansa daga wannan abin ba. Kuma bai halatta shugabannin ƙungiyoyin musulunci,
musamman masu da’awa
zuwa ga a bi Sunnah su ma su ƙyale ana aikata hakan gare su ko ga waninsu ba
tare da sun yi tsawa ko sun yi bayanin fuskar gaskiya a kan hakan ba.
Kuma bai halatta musulmi su mayar da wannan abin
wani abin musu da jayayya a tsakaninsu ba, bayan abin da ya bayyana na nassoshi
sahihai da fatawoyin manyan malamai a kan hakan. Musamman ma a cikin wannan
halin da yanayin da al’umma take ciki, inda maƙiya suka sako ta a gaba
suna ƙoƙarin murƙushe ta da ganin bayanta.
A kan haka ne hadisi sahihi daga sahabi
Abu-Umaamah ya zo cewa: Annabi (Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallam) ya ce:
« مَا ضَلَّ قَوْمٌ بَعْدَ هُدًى كَانُوا عَلَيْهِ إِلاَّ أُوتُوا الْجَدَلَ »
Waɗansu
mutane ba su taɓa ɓacewa a bayan wata shiriya da suka kasance
a kanta ba, har sai ka ga an saka musu jayayya da musu a tsakaninsu.
Daga nan kuma sai ya karanta wannan ayar:
مَا ضَرَبُوهُ لَكَ إِلَّا جَدَلَۢاۚ بَلۡ هُمۡ قَوۡمٌ خَصِمُونَ
Ba su buga maka shi ba sai domin jayayya kawai, su
dai mutane ne masu husuma kawai. (Surah Az-Zukhruuf: 58)
Asalain hadisin yana cikin Musnad na Ahmad, kuma
Al-Albaaniy ya í shi a cikin Sahih Al-Jaami’i: 5633.
Allaah ya ƙara mana shiriya da ƙafewa a kan Sunnah sak.
WALLAHU A'ALAM
Sheikh Muhammad Abdullaah Assalafiy
Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku
kasance Damu...
𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇
https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi
𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177
No comments:
Post a Comment
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.