Bayani Game Da Maita Da Kanbun Baka

    𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

    Assalam Alaikun. Shin menene hukuncin maita a musulunci  naji ance babu maita se kanbun baka. Kuma akwai hanyan da ake jinyan wannan matsala a musulunce? Domin wlh wannan abu ya daure min kai. Sabida masu aikin jiyyan wadanda mayu suka kamasu matsafa ne. Ko kuma dai nace bansan da me suke jinyan ba.

    𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

    Wa'alaikumus Salam warahmatullahi Wabarkatuh

    Da farko dai maita ba halitta bace, Tsafi ce. Maita wani abune wanda yakeda alaƙa da bokanci da tsafi, domin abune musamman ake zuwa ake samoshi a wajan bokaye wanda ake yin amfani da shi ana cutarda mutane ana saka musu cuta ajikinsu ko wani nau'i na rashin lafiya, duk da cewa wasu daga cikin malamai suna ganin cewa babu maita, amma zahirin gaskiya akwaita kuma nau'ine na tsafi da bokanci.

    Matsalar Kambun ido gaske ce ba Qarya ba. Domin Manzon Allah yayi bayaninta Qarara acikin hadisai da dama. Har ma ya ce "BAYAN QADDARAR ALLAH MAƊAUKAKIN SARKI, BABU ABIN DA YAFI HALLAKAR DA AL'UMMATA FIYE DA KAMBUN IDO".

    Kuma ya ce "DA ACE AKWAI ABIN DA KE RIGA QADDARA AFKAWA KAN MUTUM, TO DA KAMBUN IDO YA RIGATA".

    Abin da aka sani wanda mutane basa rabewa tsakanin kambun baka da maita. shi kambun baka Allah yana halittar mutum dashi, wanda shi kansa baisan ma yana da wannan halaittar ba, tayadda duk abunda suka kalla idan basuyima wannan abun addu'a ba toh wani larura yana iya samun wannan abun kamar idan yakalli wani mutum toh idan yanada kambun ido se kallon kawai ya iya cutarda wannan mutumin. Inkuma kambun bakane toh idan ya yabi abu ba tareda yayi addu'a ba toh hakan sekaga ya cutarda wancan mutumin.

    Kambun ido idan ya afka ma mutum, ko guba (Poison) bai fi shi saurin kisa ko lalata sha'anin mutum ba. Shi yasa da yawa zaka ga mutane suna ta neman maganin karya sihiri, alhali basu san cewa kambun ido ne ya afka musu ba.

    Mai kambun ido zai iya yi maka akan dukiyarka ko gidanka ko 'ya'yanka ko lafiyar jikinka, ko aikinka ko kasuwancinka, ko muryarka, ko salon rubutunka, ko yanayin tafiyarka, ko kuma duk wani abu naka wanda ya burgeshi, ko kuma ya jefa hassada acikin baqar zuciyarsa.

    Kuma masu irin wannan cutar suna nan da yawa acikin al'ummah. Watakila Akwaisu agidanku ko wajen aikinka, ko acikin abokanka ko Ajin da kake karatu, etc. Sannan kuma akwaisu acikin Aljanu ma, wadanda ta hanyar kallo suke iya cutar da mutum koda basu shiga jikinsa ba.

    Yana daga cikin manyan hanyoyin Riga-kafi, mutum ya yawaita addu'o'i da zikirorin safe da yamma da na kwanciya bacci da na shiga gida da fitowa da sanya sutura da sauransu.

    Ga wasu addu'o'i kariya daga dukkan sharri:

    أَعُوْذُ بِكَلِمَاتِ اللهِ التَّامَّاتِ مِنْ شَرِّ مَا خَلَقَ ۝ أَعُوذُ بِكَلِمَاتِ اللَّهِ التَّامَّةِ مِنْ كُلِّ شَيْطَانٍ وَهَامَّةٍ وَمِنْ كُلِّ عَيْنٍ لاَمَّةٍ ۝ بِسْمِ اللَّهِ أَرْقِيكَ مِنْ كُلِّ شَيْءٍ يُؤْذِيكَ مِنْ شَرِّ كُلِّ نَفْسٍ أَوْ عَيْنِ حَاسِدٍ اللَّهُ يَشْفِيكَ بِسْمِ اللَّهِ أَرْقِيكَ ۝ بِسْمِ اللهِ لاَ يَضُرُّ مَعَ اسْمِهِ شَيْءٌ فِي اْلأَرْضِ وَلاَ فِي السَّمَاءِ وَهُوَ السَّمِيْعُ الْعَلِيْمُ ۝

    Idan kana  yawaita yin irin wadannan Addu'o'i, Allah zai tsareka, koda kuwa mai maita da kambun baka ya aibantaka.

    Allah ta'ala yasa mudace

    WALLAHU A'ALAM

    Zauren Fatawowi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance Damu...

    𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

    https://chat.whatsapp.com/FBuwMyVjc2sGOEGLm0W7ed

    𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

    https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi

    𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

    Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

    Question and Answers in Islam

    No comments:

    Post a Comment

    ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

    HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.