Ticker

6/recent/ticker-posts

Shin Ya Hallata Ga Miji Ya Shiga Ɗakin Matar Da Ba Kwananta Ba?

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Assalaamu Alaikum, Malam, tambaya ce gare ni: Mutum mai mata biyu, wai me ya halatta a tsakaninsa da matar da ba a ɗakinta ya ke ba? Za su iya riƙe hannu ko sumbanta ko runguman juna?

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

Wa Alaikumus Salaam Wa Rahmatul Laah.

Daga cikin littafin Haƙƙoƙin Maaurata da na rubuta ne na kalato wannan, tare da ƙarin bayani. Me yiwuwa ya zama amsa ga wannan tambayar, in Shã Allahu

A’ishah Ummul-Mu’mineen (Radiyal Laahu Anhaa) ta ce:

كَانَ رَسُولُ اللَّهِ - صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ - لاَ يُفَضِّلُ بَعْضَنَا عَلَى بَعْضٍ فِى الْقَسْمِ ، مِنْ مُكْثِهِ عِنْدَنَا ، وَكَانَ قَلَّ يَوْمٌ إِلاَّ وَهُوَ يَطُوفُ عَلَيْنَا جَمِيعًا ، فَيَدْنُو مِنْ كُلِّ امْرَأَةٍ مِنْ غَيْرِ مَسِيسٍ ، حَتَّى يَبْلُغَ إِلَى الَّتِى هُوَ يَوْمُهَا ، فَيَبِيتُ عِنْدَهَا

Manzon Allaah (Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallam) ya kasance ba ya fifita sashenmu a kan sashe wajen rabon-kwana, a iya zamansa a cikinmu; kuma da ƙyar wani yini guda ke wucewa face kuwa ya kewaya mu gaba-ɗaya, kuma ya kusanci kowace mace amma ba tare da saduwa ba, har sai ya kai ga mai girki a ranar, sai ya kwana a wurinta. (Abu-Daawud: 2137 ya riwaito shi).

A cikin riwayar Al-Bukhaariy (5268) da Muslim (1474) ya ce: Idan ya yi sallar La’asar sai ya kewaya matan aurensa…

Kuma a cikin riwaiyar Ahmad ya ce: Sai ya kusance ta: Ya shafe ta amma ba tare da saduwa ba.

A ƙarƙashin wannan hadisin da makamantansa malamai suka gano cewa:

1. Haƙƙin miji ne ya yi adalci a tsakanin matan aurensa a wurin rabon-kwana da ciyarwa da shayarwa da tufatarwa da sauran abubuwan da suke a fili, kar ya fifita wata a kan wata.

2. Haƙƙin mata ne ta san cewa, miji ba zai iya yin adalci a tsakanin matan aurensa ba a cikin abubuwan da suke a ɓoye, kamar soyayyar zuciya da sha’awar saduwa da sauransu.

3. Haƙƙin miji ne kar ya shiga gida ko ɗakin matar da ba kwananta ba da dare, sai in akwai larura mai ƙarfi, kamar rashin lafiyarta da makantan haka.

4. Haƙƙin miji ne kar ya shiga ya kwanta, ko kuma ya yi barcin dare sai a ɗakin matar da ya ke kwananta ne kawai.

5. Haƙƙin miji ne kar ya sadu da wata daga cikin matansa sai wacce ita ce ke da kwana, ko kuma idan akwai amincewa da yarda daga wacce ta ke da kwanan.

6. Haƙƙin mata ne kar ta yarda mijinta ya sadu da ita idan dai ba kwananta ba ne, ko in ba da izinin wadda ta ke da kwanan ba.

7. Haƙƙin miji ne ya shiga ɗakin wadda ba kwananta ba da rana, kuma ya kusance ta da dukkan komai, in dai ba saduwa ba.

8. Haƙƙin mata ne kar ta hana mijinta yin komai na soyayya tare da ita a lokacin da ba kwananta ba, matuƙar dai hakan ba zai kai ga saduwa ba.

9. Haƙƙin mata ne kar ta goya wa mijinta baya wurin wuce-iyaka har a kai ga saduwa a lokacin da ta san ba kwananta ba ne.

10. Haƙƙin mata ne ta yarda idan miji ya shiga ɗakin wacce ba kwananta ba, ko da kuwa ya yi wasa da ita, in dai bai kai ga saduwa ba.

(Dubi Ta’leeq na As-Shaikh Sameer Az-Zuhairiy ga Buluugh Al-Maraam, shafi: 324).

WALLAHU A'ALAM

Sheikh Muhammad Abdullaahi Assalafiy

Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance Damu...

𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

Question and Answers in Islam

Post a Comment

0 Comments