𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀❓
Assalamu Alaikum. mace ce ta zubar da ciki har sau
biyar, ta sha azumin Ramadan na shekaru biyar, ta daina yin sallah na shekaru
biyar, kuma duk da gangar! Sai daga baya ta yi nadama. Menene hukuncin ta?
𝐀𝐌𝐒𝐀❗️
Wa Alaikumus Salaam Wa Rahmatul Laah.
A nan akwai mas’alolin da suka kamata a fara
fahimtar su kafin amsa wannan tambayar
[1] Da farko dai ya dace duk mu san cewa tun tuni
akwai bambancin fahimta a tsakanin ƙungiyoyin musulunci a kan zunubi da saɓo.
(i) Mu’utazilawa da Khawarijawa suna ganin mai saɓo da mai zunubi a matsayin kafiri ne
kawai. Kodayake Mu’utazilawa suna ganin sa a duniya yana kan wani matsayi ne a
tsakanin musulunci da kafirci (Al-Manzilah Bainal Manzilatain), amma kuma sun
haɗu da Khawarijawa a kan
cewa a Lahira yana cikin Wuta.
(II) Su kuwa Murji’awa suna da ra’ayin cewa: Mai
zunubi da saɓo
cikakken mumini ne a duniya da Lahira, domin ra’ayinsu na cewa: Saɓo ko zunubi ba ya cutarwa matuƙar dai
akwai Imani (Laa Yadurru Ma’al Imani Ma’asiyah).
(iii) Kowane ɗaya daga cikin ƙungiyoyin sun riƙe
sashe ko ɓangare
ne na hujjoji ko dalilan da su Ahlus-Sunnah Wal Jamaa’ah suka haɗa kan su, kuma suka tabbatar da matsayinsu
cewa: Mai saɓo ko
zunubi musulmi ne mai Imani, amma ba mai cikakken Imani abin yabo ba. Don haka
idan ya mutu a kan wannan aikin bai tuba ba, wannan na iya kai shi ga shiga
Wuta a farko, idan Allaah bai gafarta masa ba. Amma daga ƙarshe zai fitar da shi
saboda imaninsa na asali.
[2] Magana ta-biyu: A wurin Ahlus-Sunnah saɓo ko zunubi sun karkasu gida-gida ne:
(i) Akwai mafi-girman zunubi, watau shirka da
kafirci wanda Allaah ya yi alƙawarin ba zai yafe wa wanda ya mutu yana aikata su
ba. Su ne kamar yin tsafi ko shiga ƙungiyoyin matsafa, da bautar gunki, da
gaskata boka, da zagin Allaah, da fifita waɗansu mutane a sama da Annabawa da
Manzannin Allaah, da sauransu.
(II) Akwai kuma manyan zunubai waɗanda a asali ba su kai girman kafirci ko
shirka ba, watau kamar ƙarya da sata da zina da shan kayan maye da
makamantansu. Amma idan mutum a cikin zuciyarsa ya ƙudurce cewa wannan aikin
halal ne ba haram ba ne, to ya zama babban kafirci mai fitarwa daga musulunci.
(iii) Sai kuma ƙananan zunubai waɗanda ba su kai girman manyan ba a asali.
Amma kuma yawaitawa ko maimaita aikata su kan mayar da su kamar manyan zunubai.
Su ne kamar kallon sha’awa ga matar da ba ta halatta gare shi ba, da sauraron
maganarta, da kaɗaita
da ita, da sauransu. Idan musulmi ya nisanci aikata manyan zunubai sai a
kankare masa ƙananan.
[3] Abu na-uku shi ne: Wajibi ne kowane musulmi ya
girmama Allaah Ubangijinsa kuma Ubangijin Halittu gaba-ɗaya, kuma ya girmama dukkan umurninsa da
haninsa. Kar ya riƙa kallon zunubi ko saɓo a matsayinsu na manya ko ƙanana,
ta yadda zai iya aikata wanda ya so daga ciki, domin ganin wai ƙarami
ne.
Amma ya riƙa kallon girman Ubangijinmu Ta’aala wanda ya hana wannan zunubin ne. Don
haka ya nisanci aikatawa, kuma ya riƙa gaggawan neman gafara da tuba daga
kowane saɓo ko
zunubin da ya aikata a duk lokacin da Imani da tunanin hankalinsa suka komo
jikinsa, ya gane cewa ya aikata mummunan aiki.
Sannan kuma wajibi ne kowane musulmi ya san cewa,
aikata zunubi yana janyo tawaya ko naƙasa a cikin imanin mai aikatawa, kuma tuba
da neman gafara na janyo kankare wannan zunubin har bawan Allaah ya zama karɓaɓɓe a wurin Allaah Ta’aala. Sai dai kuma cikinmu
bayin Allaah babu wanda yake da yaƙini cewa an karɓi ko da ɗaya daga cikin kyawawan ayyukansa ko an
yafe masa dukkan zunubansa saboda tubansa da istighfarinsa, amma dai muna fatan
hakan ne kawai.
Tun da dai ga Manyan Annabawa da Manzanni
(Alaihimus Salaatu Was Salaamu) waɗanda
suka fi kowa tsoro da biyayya da ƙarin kusanci ga Allaah (Saubhaanahu Wa Ta’aala) sun kasance a cikin fatan samun
Rahama da fargabar shiga cikin azabarsa har a Ranar Lahira, kamar yadda Hadisin
Ceto ya nuna, wannan shiyasa ba za mu daina ƙoƙarin aikata ayyuka
na-gari da yawaita tuba da neman gafara a kan dukkan zunubanmu ba, har zuwa ƙarshen
rayuwarmu a duniyar nan. Muna fatan Allaah ya karɓa mana kyawawan ayyukanmu, ya yafe mana
dukkan kura-kuranmu.
[4] Na-huɗu: Hukuma ko gwamnati a ko’ina ita ce ke da ikon
kafawa da zartar da hukunci a kan masu saɓa wa dokoki daga cikin masu laifi, ita ce ke sa
kowa ya bi doka. A ƙarƙashin dokokin addininmu na musulunci akwai
hukuncin kowanne daga cikin waɗannan
laifuffukan guda uku
(i) Kisan kai ko da na jaririn da aka hura masa
rai a cikin mahaifiyarsa ne babban zunubi ne, wanda hukuncinsa shi ne: Qisasi,
watau a kashe wanda ya yi wannan laifin, tun da dai da gangar ne ya yi. Amma a
nan dayake mahaifiya ce ta aikata laifin, ba za a kashe mahaifi ko mahaifiya
saboda kisan jaririnsu ba. Sai dai ko a sanya ta biya diyya ga mahaifin jaririn
da danginsa. Wannan idan ba ta halatta laifin ba kenan. Amma halattawa kafirci
ne, ko da kuwa ba ta aikata ba.
(II) Game da ƙin yin sallah kuwa,
kodayake malamai sun sha bamban a kan kafirci ko rashin kafircin mai wannan
aikin, sai dai kuma sun yarda cewa: Duk lokacin da aka samu mai wannan laifin
dole ne hukuma ta kamo shi, ta tilasta shi ya yi sallar. To, idan har ya ƙi yi,
kuma ya yarda a kashe shi a kan haka, to shi kafiri ne kawai, ba musulmi ba ne.
Amma idan tun farko ya ƙi yin sallar don yana ganin ba wajiba ba ce a
kansa, to wannan ma kafirci ne. Allaah ya tsare mu.
(iii) A kan azumin Ramadan ma malamai sun yarda
cewa, hukuma ta kamo wanda ya ƙi yin azumin ta gargaɗe shi a kan wannan laifin. Idan bai yarda
ya cigaba da yi ba, sai alƙali ya sa a tsare shi kuma a hana shi cin komai
daga ketowar alfijir har zuwa faɗuwar rana,
har zuwa ƙarshen watan. Wannan ga wanda ya ƙi yin azumin haka nan kawai saboda tsoron
jin yunwa, da sha’awar
abinci. Amma idan ya ɗauki
cewa azumin ba dole ne a kansa ba, to wannan kafirci ne, domin ya halatta haram
kenan.
[5] Na-biyar: Amma dangane da hukuncin wannan
matar da masu aikata ayyuka irin nata, a halin da wani alƙalin musulunci bai samu
iko a kan su ba, sai dai a nuna mata hanyar tuba kawai.
Kodayake ba za mu ɗebe tsammanin samun Rahamar Ubangiji gare
ta ba, sai dai kuma ba za mu amintar da ita daga laifukan da ta aikata ba. Abin
dai da yake wajibi gare ta a nan shi ne: Ta gaggauta tuba daga dukkan zunuban
nan, ta ɗauki
matakan da malamai suka ambata.
Matakan da za ta ɗauka domin neman gafarar Allaah da samun
tubansa da yafewarsa a kan kowane irin zunubi su ne kamar haka:
1. Ta daina yin aikin saɓon a daidai lokacin da hankalinta ya dawo
jikinta, ta fahimci cewa ta saɓa wa
Allaah Ubangijinta.
2. Ta yi ƙoƙari tuban na ta ya zama saboda Allaah Maɗaukakin Sarki ne kaɗai, ba domin wani dalili daga cikin
dalilai na dabam ba.
3. Ta ji a cikin zuciyarta da jikinta cewa, wannan
abin da ta aikata mummunan aiki ne, wanda kuma zai iya haifar ma ta da mummunan
sakamako a Duniya da Barzahu da Lahira, idan Allaah Ta’aala bai tausaya ma ta
ya yafe ma ta ba!
4. Ta yi nadama da baƙin ciki a kan abin da ya
auku na wannan mummunan sakacin da ta yi har wata gaɓa daga cikin gaɓoɓinta ta karkace ta faɗa cikin saɓon.
5. Ta faɗa wa Allaah Ubangijinta Masanin ciki da wajen
al’amuranta cewa: ‘Ya Allaah! Na tuba kuma na komo gare ka. Don haka ka yafe
mini saɓon nan
da na tafka.’
6. Ta ɗaura niyyar cewa ba za ta sake komawa ga yin irin
wannan sakacin ba, balle har a samu wata gaɓarta ta sake aikata laifi mai kama da
wannan a iya tsawon rayuwarta.
7. Ta yi amfani da wani kyakkyawan aikin imani da
ta taɓa
aikatawa ko wani mummunan aikin sharri da ta nisance shi saboda Allaah kaɗai, ta yi tawassuli da hakan ga Allaah a
wannan lokacin. Watau, ta roƙi Allaah Ta’aala da wannan aikin.
8. Ta yi ƙoƙarin gyara abubuwan da take iya gyarawa na
ayyukan da sakacinta ya sa suka lalace, ko waɗanda ta ɓarnata ta dalilin wannan saɓon, idan suna iya gyaruwa.
9. Ta rabu da wuri, ko duk wanda ya zuga ta ko ya
yaudare ta ko kuma ya taimaka ma ta har ta tafka wannan zunubin.
10. Ta yi ƙoƙarin kusanta ko haɗuwa da sababbin ƙawaye da sauran mutanen
kirki, waɗanda
za su iya taimaka ma ta, su zuga ta ga cigaba da aikata alhairan da za su iya
zama gyara ko masu kankarewa ga abin da ya gabata na ɓarna.
11. Idan kuma laifin ya haɗa da haƙƙin waɗansu bayin Allaah ne, to a nan sai ta
mayar musu da haƙƙoƙin na su, ko kuma ta nemo amincewarsu da
yafewarsu.
12. Ta lalata duk kayan da take amfani da su wurin
aikata laifin, kamar misali kwalaben giya ko ƙwayoyin daskarar da ƙwaƙwalwa
ga masu shaye-shaye, ko kuma hotunan tsiraici ga masu kallon fima-fimai da
sauran makamantansu.
Waɗannan
su ne matakan da za ta ɗauka a
kan kowane daya daga cikin zunuban da ta aikata, a duk lokacin da ta aikata su.
Allaah Ta’aala nake roƙo ya tsare mu, ya taimake mu gaba ɗaya, kuma ya sa mu fi ƙarfin
shaiɗanunmu
da zukatanmu.
Ta kara da wannan
(i) Ta fara da yin yaƙi da ranta har ta fi ƙarfinta,
ta hana ta aikata saɓo.
(ii) Ta yawaita yin Isti’aazah: Neman Allaah ya
tsare ta daga yaudarar shaiɗan.
(iii) Ta yi ta ƙoƙarin zama mai khushu’i da ƙanƙan-da-kai ga Ubangijinsa
a cikin sallah.
(iv) Ta yawaita karatun Alqur’ani da lura da
ma’anoninsa da yin aiki da koyarwarsa.
(v) Ta kula da Zikirorin Safiya da Maraice da na
kwanciya barci da farkawa da sauransu.
(vi) Ta yawaita addu’a da ƙanƙan-da-kai ga Allaah, don
ya kare ta daga wannan masifar.
(vii) Ta nisanta kanta daga dukkan abin da ta san
zai iya jan ta, ya mayar da ita cikin zunubin.
Amma fa ta riƙa tunawa da maganar
Annabi (Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallam) cewa:
إِنْ تَصْدُقِ اللهَ يَصْدُقْكَ
Idan ka gaskata Allaah zai gaskata ka. (Sahih
An-Nasaa’iy: 1845).
Allaah ya ƙara tsare mana imaninmu, ya kare mu daga
sharrorin zukatanmu da munanan ayyukanmu, ya shiryar da mu ga ayyukan da za su ƙara
kusanta mu gare shi, ya yafe mana kura-kuranmu, ya karɓa mana kyawawan ayyukanmu, ya haɗa mu da bayinsa na-gari a Gidan Rahama.
WALLAHU A'ALAM
Muhammad Abdullaah Assalafiy
Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku
kasance Damu...
𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇
https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi
𝐅𝐀𝐂��𝐁𝐎𝐎𝐊👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177
No comments:
Post a Comment
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.