Ticker

6/recent/ticker-posts

Shin Ana Iya Jinin Haila Sau 2 A Wata?

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Shin jinin haila yana iya zama sau 2 a wata ko sau 1 a shekara tare d hujja Assignment ne aka bamu?

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

Mace Ba ta yin Jini a Wata Sau Biyu. Tana yin Jini idan tayi Tsarki Kuma Ba'a daɗe ba Wani Jinin ya zo, domin Hadisi ya Inganta daga Manzon Allah yake cewa: Larura Ce da Allah ya Saukar Wa 'Yayan Adam a kowanne Wata.

Wata tana yi Farkon Wata, Wata Kuma Tsakiyar Wata, Wata Kuma Karshen Wata, Sai dai Abin da Bincike ya Tabbatar Shine. Wata Matar tana iya yin Jini a Farkon Wata da Karshen Wata.. Wanda Yake Kenan a Cikin Wata Biyu tana Iya yin Jini Ukku.

Wanda Hakan ya Nuna Mai irin Wannan Al'adar, zata Iya gama Idda Bayan Rabuwa da Mijinta a Wata Biyu. Maimakon Wata Ukku, Sabida Haka Babu Zargi idan Mace tayi Aure Bayan Wata Biyu da Rabuwa da Mijin ta, Domin zata Iya Gama Iddarta a Cikin Wata Biyu ɗin.

 Malamai Suka Ce: Duk wadda Jini ya zo Mata a Wata Ɗaya Sau Biyu. Matukar ba irin Masu Waccan Dabi'ar Zuwan Jinin ne a Farkon Wata da karshen sa ba. To dole Wannan Jinin ya Zama Ɗaya  na Al'ada ne, Ɗaya Kuma Na Cuta ne.

Duk da Cewar Ana Samun Matan da Suke  yin Jini a Shekara Sau Biyu kachal, Bayan Wata Shida Kenan, ko Sau ɗaya ma a Shekara.

Akwai wadda Kuma Wata yana Iya Tsallake Mata ba tare da ta ga jinin Hailar ta ba. Ba tare da Juna Biyu a Jikin Wannan Matar ba ko wani Abu.

Allah ta'ala yasa mudace.

WALLAHU TA'AALA A'ALAM

Zauren Fatawowi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance Damu...

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://chat.whatsapp.com/Fb6qgYPXfEeHb8CD1SWAkK

𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam

Post a Comment

0 Comments