𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀❓
Assalamu akaikum Malam Dan Allah ina tambaya. Wata
ce take gaya min abunda ta aikata abaya yanzu kuma ta shiryu take san taji
yadda zatayi akan abin da tayi abaya. Wani lokacin da ya wuce bata azumi kuma
bata sallah ko ance taje tayi sallah sai tace tayi, Kuma azumi koda ta dauka
sai ta karya babu wanda yasani. To yanzu
kuma ta dage tana yi, shine tace yaya zatayi da waccen ta baya? Malam muna san
karin bayani.
𝐀𝐌𝐒𝐀❗️
Wa alaikis salam wa rahmatullahi wa barakatuhu.
Akwai fatawoyi guda biyu akan wannan mas'alar.
Wasu maluman suna ganin wajibcin ramukon dukkan salloli da azumin da kika barsu
a baya koda sun kai na shekaru 20 ko 30 ko fiye da haka, saboda kasancewar
sallah ita ce aiki mafi girma acikin rukunan musulunci. Shi kuma azumi yana
daga cikin manyan ibadun dake bin bayan sallar.
Amma wasu Maluman suna ganin cewa ba sai kin
ramasu ba. Sun dogara da hujjar cewa ai duk wanda yabar sallah da gangan ya
riga ya kafirta. Koda kwaya ɗaya
ce, kuma koda ya yarda da farlancinta akansa, ya riga ya kafirta. Shi kuwa
kafiri babu wajibcin yin azumi ko zakkah ko sauran ayyukan musulunci akansa.
Yanzu kuma da kika tuba, to kin dawo musulunci
kenan. Shi kuwa musulunci yana rushe duk wani laifin da mutum ya aikata acikin
kafirci kamar yadda Manzon Allah ﷺ ya
fada acikin hadisi "MUSULUNCI YANA RUSHE ABIN DA KE KAFINSA".
Don haka yanzu sai kici gaba da kula da sallolinki
na farillah, ki yawaita nafilfili, kuma ki yawaita yin azumin nafilah da sadaqoqi
domin samun kusanci da Mahaliccinki.
Kada ki sake yin wasa da sallah domin ita ce
marabar musulmi da kafiri. Kuma Manzon Allah ﷺ ya ce "Abin da ke Tsakanin mutum da
kafirci shine barin yin sallah".
Da kuma cewarsa ﷺ "Sallah ita ce ginshikin addini. Wanda
ya tsayar da ita hakika ya tsayar da addini. Wanda kuwa ya rusheta to ya rushe
addini".
WALLAHU TA'AALA A'ALAM.
Zauren Fatawowi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku
kasance Damu...
𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇
https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi
𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177
ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ
**************************
Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.
No comments:
Post a Comment
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.