Ticker

6/recent/ticker-posts

Sana'ar Gini

Sana'ar Gini

Sana'ar Gini sana’a ce da ake sarrafa abubuwan da suka shafi ƙasa kamar irin su yumɓu, taɓo, yashi da sauransu domin su zama masu amfani. Kamar gina muhalli da kuma gina mazubi kamar irin su tukunya, tulu, da sauransu.

Wannan sana’a ta gini daɗaɗɗiyar sana’a a ce. Asali mutane kan gina bukka ne ta hanyar amfani da kara sannan kuma daga baya a yaɓe shi da ƙasa. Daga nan kuma sai aka samu cigaba, aka koma ana gina ɗaki da zallar tubalin ƙasa, kama-kama har zuwa yin bulon ƙasa sannan a gina ɗaki da shi.

Sana’ar Gini ta kasu gida uku:

1 .Akwai ginin muhalli da ya shafi gina gida baƙi ɗayansa da dukkan nau’ukan ɗakuna kamawa tun daga ɗakin kwana, ɗakin hutu, ɗakin girki, ɗakin karatu da sauransu.

2. Ginin Tukwane da sauran kayayyakin adana ruwa, abinci da sauransu.

3. Ginin Rijiya, sana’a ce da ake haƙa rami domin samo ruwan amfanin yau-da-kullum, ko kuma masai (shadda ko sarga).

Daga Zauren:
Hausawa da Harshensu

Post a Comment

0 Comments