𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀❓
Assalam Alaikum.. Allah gafarta Mallam, nine nake
lalata da wata yarinya inama tunanin nine farkon fara zina da ita, nine silar ɓata mata tarbiya gaba ɗaya. Amma ni yanzu na tuba nabar zina kuma
har nayi aure na haihu harda yara. Ita kuma wannan yarinyan har yanzu ina
ganinta kan titi tana yawo ta zama karuwa. Idan mun haɗu ko kallonta bana son yi balle ma asan
cewa na taɓa
kulla wata hulda da ita saboda kariyan mutuncina da kimana. Shin mallan yanzu a
hakan meye matsayina gashi ni na tuba amma kuma ita tana kan aikinta na alfasha
wanda nine sanadiyyar shigarta shi, shin ni bayan neman Allah gafara ya isa ko
sai na nemi gafaranta, 'yan uwanta da kuma kila mijinta idan zata yi aure?
𝐀MSA❗️
الحمد لله وحده.
Dafarko dai muna tayaka murna da Allah yasa kagane
wannan danyen aiki daka aikata babban kurene tun mutuwa bata riskeka kaba,
Allah yasa tubanka ya dore yakuma karbi tuban, yasa wannan yarinya ta tuba
tadena.
Hakika kaci amanar wannan yarinya kaci amanar
musulunci da al'ummar musulmai ka cutar da rayuwarta ka cutar da iyayenta kaci
Amanar Allah da manzansa, baya kuma da cin zarafinta amatsayinta na mace wacce
musulunci ya girmamata. Zina dai zunubine mai girman gaske wanda ke kwashewa
mutum albarkar rayuwa.
Sannan kasani tundaka ranar daka yaudareta kaci
mutuncinta harkai zina da ita wallahi duk wata zina datayi bayan wacce kafara
yaudararta to kana da kaso nazunubi acikinta, kasani Allah ba'azzalumi bane ba
zai barka hakaba.
kai yanzu zakaso ace, Uwarkace wannan yarinyar?
zakaso ace kanwarkace wani yazamto sanadiyyar zamanta haka? zakaso ace
yayarkace takasance haka ko zakaso ace 'yarkace haka? gashi yanzu kaida kanka
bakama so kanuna alamarma kasanta, to kasani zina bashice wallahi duk wanda yai
da uwar wani za ai datasa uwar, inkai da 'yar wani za ai dataka, idan kai saida
kabada kuɗi ko
wani abu najan hankali idan Allah yaga dama kai taka 'yar ita zata nema ayi da
ita kuma acikin gidanka za ai zinar da ita akyaleka da bakin ciki kamar yanda
kasa iyayen wata bakin ciki, kullum baka da sukuni.
Anan zamu kara fahimtar fasaha da hikima cikin
hadisan Annabi sallallahu Alaihi wasallam wanda ya ce duk wanda ya assasa wani
abu na alkhairi duk wanda yai aiki ko koyi da wannan alkhairi to asalin wanda
ya assasa alkharin zaita samun ladan duk
wanda yai aiki da alkhairin koda shawarace kuwa yabayar wajan wani akin
alkhairi har duniya takare haka wanda ya assasa aikin sharri.
Yanzu kaga
wannan baiwar Allah kaine farkon wanda ya assasa mata zina duk wanda yai zina
da ita kanada zunubinka na musamman amatsayinka nawanda ya assasa mata zina.
Amma dangane da neman yafiyar iyayenta ko mijinta
duk wannan bai taso ba, saboda Allah bayasan bayyana mummunan Abu haka shari'a
batasan abun da zai haifar da fitina atsakanin al'umma wanda bayyana ma
iyayenta da neman gafararsu zai iya buɗe wata sabuwar kofar fitina da rikici atsakani,
dan haka ka kara zage damtse wajan nema mata gafara wajan Allah da iyayenta,
miji kuwa bata samu ba, balle kanemi gafararsa.
Kadage wajan bin duk wasu hanyoyi nakaga kajawo
hankalinta danta daina wannan mugun aiki, zance baka kulata dankare mutuncin
kanka baima taso ba anan, dole kabi hanyoyin dakabi wajan yaudararta harka
shawo kanta kai zina da ita, sune za ka sake bi wajan jan hankalinta dataji
tsoran Allah ta tuba kamar yanda katuba, kanuna mata kaima kayi nadamar abun da
ka aikata da ita, kuma kanajin ciwon abun atare dakai, kada ka karaya wajan bin
hanyoyin dazaka tabbatar kaci nasara wajan tadena karuwanci ta tuba.
Idan Allah yasa kai nasara ta tuba, to tunda kaine
kasata wannan hanyar kuma katuba, itama ta tuba, to ihsanin dazakai mata shi ne
ka aureta kazauna da ita itama tasamu zurriya, ko kuma katashi haikan kashiga
nema mata mijin aure nakirki ya aureta danta samu zurriya dayyiba, dan kasamu
ko Allah yakalli tubanka yayafema wancan cin mutunci dakai mata ko Allah zaisa
yakalli niyyarka yakarbi tubanku kai da ita baki daya.
wannan shi ne kadai abun da zakayi idan harda
gaske kayi nadamar wanan mugun aikin naka kuma ka gwammace jin kunyar duniya a kan ta lahira agaban
mutanenen duniya baki ɗaya,
ta duniya kuwa watakilama iya unguwarkune kawai kuma bata kaiwa wata kana
cikinta wannan jin kunyar shi ne Zaman lafiyarka.
Sannan ku kuma mata irin waɗannan bayanai nayanda ake maida rayuwarku
kamar ta dabbobi awulakantaku wulakanci makaskanci ya isheku izinah a kan yanda
kuke bada kanku bori yahau yayi sukuwa daka baya yafi kowa kinku daganinku
aruyuwarsa.
'yar uwa yanzu kiduba dai yanda mai tambayarnan
yake bayani waifa yama tuba kenan, amma haɗuwa da ita kan hanya bayasan yi, shi
namiji inzai zina da mata dubu ba muwarsa bane bawanda ya isa yagane kuma
zaisamu wacce zata zauna dashi, ayayinda ke kuma zai lalata miki rayuwa cikin
wasu 'yan mintuna biyar zuwa goma dazaki wulakantar dakanki danki faranta masa
rai ki kuma fusata mahaliccinki mahaliccinsa ga kuma kaskanci da tozarci dazaki
janyowa rayuwarki har ta 'yayanki kinci amanarsu, iya abun da wanann mai
tambayar yafadi acikin tambayarsa ya isa wa'azi da kukan zuci a kan yanda kuke
saida rayuwarku da mutunciku da darajarku da Allah yaimuku ga wasu maikiyanku
makiyan rayuwarku, a kan naira dubu ɗaya ko uku dazai baki kiyi ankon bikin kawarki ko
yasaki amotar daya sato kuɗin
babansa ko uwarsa ya iyo hayarta, ko yadakko batare da ubansa ya sani ba, ko
saboda kuɗin
kifin gwangwani da maltina da shinkafa dakayan makulashe dazai dunga saya miki
kina zuwa dasu collage kina nuna kewatace alhali mahaukaciyace wacce dabba
tafita tunani maikyau.
Saboda darajar 'ya mace ne fa musulunci yai umarni
daki dunga rufe duk jikinki inzaki fita saboda tsadarsa ne aka umarceku da
hakan, bawai dan atsananta muku bane, duk wani abu mai tsada ɓõyeshi ake ba'a bayyanashi afili shin
bazaku hankaltaba yaku uwayen al'ummar manzan Allah sallallahu Alaihi wasallam!
koda kuɗi ɓõyesu ake bakasan kowa yasan nawane
alalitarka saidai kadunga dakkowa kaɗan-kaɗan
kana hidimarka meyasa saboda suna da daraja, to kuma darajarkuce tasa musulunci
ya umarceku da ku kame kanku tahanyar sutura mai kyau, da kin ruduwa da
kyalekyalen duniya.
Mace zinari ce bata tsufa, shiyasa sanda wani yagi
sake alokacin ne kuma wani sai ganki ya ce yana sonki, kuma babu mummuna cikin
mata saidai inbata gyara kanta bane danme zakibar wani mugu azzalumi makiyinki
ya lalalata miki rayuwa da hanakalinki da kimarki da mutuncinki, haka kawai dan
wata karamar bukata ta duniya, ya kamata muyi tunani na nutsuwa kugane masu
alaka daku danku zauna dasu kuyi rayuwa mai kyau gwargwadon abun da Allah
yabasu, ba masu aro mashin roba-roba, ko masu aro mota suna zuwa suna hure muku
kunnuwa kuna mantawa da irin darajar da Allah yai muku ba, ko masu shiga rigar
addini suna yaudararku dasunan cewa sudin na Allah ne, a'a kawai wani abune
ajikinki suke bukatar su ɗanɗana suji yaya kuke su gujeku.
Da rayuwa cikin kaskancin da fushin mutane da
fushin Allah dana masu imani gwara rayuwa cikin mutunci da talauci. Allah yasa
mufahimta kuma mu gane.
WALLAHU A'ALAM
Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku
kasance Damu...
𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇
https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi
𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177
ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ
**************************
Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.
No comments:
Post a Comment
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.