TAMBAYA (28)❓
MAlam tambayata biyu ce daya privet daya public.
Bayani nakeso kaimana a kan ranar da aka haifi fiyayyan halitta ankoyan asiri
ranar litinin amman yanxu dana lissafa sainaga zaikama laraba Kuma meyadace ayi
ranar
AMSA
Musulmai dayawa suna kafa hujjar haihuwar Annabi
Muhammad SAW a ranar 12 ga watan Rabi'ul Awwal wanda yayi daidai da 570CE wasu
kuma sunce 13 ne wasu ma 15 sukace saidai babu wani sahihin hadisi da ya
tabbatarda hakan a gaba daya cikin kutubus sittah (Bukhari, Muslim, Abu Dawud,
Imam at-Tirmidhi, Imam an-Nasa'i da Ibn Majah)
To amman mafi qaulin rinjaye shi ne an haifeshi ne
a ranar litinin saboda shi da kansa ya fada a lokacinda sahabbai suka
tambayeshi dalilin dayasa yake azumtar ranar ta litinin
(Jami'i at-Tirmidhi littafi na 9 lambata 101)
Shi kuma azumin Alhamis yana yin sa ne SAW saboda
a ranar ne ake tattara ayyukan bayi a kaiwa Allah SWT
An karbo daga Abu Hurairah, Ibn Abbas, Nana Aisha
da Abdurrahman Ibn Abi Bakrah (RA), Annabi SAW ya ce "Tabbas, ayyukan bayi
ana bijirar dasu ga Allah SWT a ranar litinin da alhamis, nafison a bijiro da
ayyukana yayinda nake azumi"
(Sunan Ibn Majah littafi na 10 lambata 1656)
Waɗanda
suka inganta Hadisin sun hada da Ibn Hajar al-Asqalani, Imam ad-Dhahabi,
al-Hafiz Ibn Khathir (Allah yayi musu rahama baki daya)
A tarihance abinda ya tabbata shi ne: Annabi SAW
ya koma ga Allah ne a ranar litinin 12 ga watan Rabi' al-Awwal, 11 AH wanda
yayi daidai da 8 ga watan June, 632 CE. Ya rasu ne bayan yan watanni kalilan da
yin hajjin bankwana (Hajj al-Wada') a lokacin yana shekaru 63
Bayan rasuwarsa kuma sai aka nada Sayyadina
Abubakar RTA a matsayin khalifa wanda duk son da yakewa Annabi SAW amman ba a
taba rawaitowa cewar yayi maulidin Annabi SAW ba. Sauran khalifofin ma duk
basuyi ba. Hakama Nana Aisha RTA, saida tayi shekaru 48 bayan wafatin Ma'aiki
SAW alhalin bata auri kowa ba saboda son kasancewar daya daga cikin matan
Annabi a cikin Aljannah to amman dukda wannan soyayya ba'a taba cewa Nana Aisha
RTA tayi maulidi ga Manzon Allah SAW ba
A shawarce bai kamata Musulmai su dinga daga
jijiyar wuya a kan wannan sabanin ba
Wasu ma musu a kan wannan mas'alar kan kaisu ga
tsananin gabar da zata rusa alaqar mu'amalarsu wanda harma hakan yake shafar
addininsu wanda anan shaidan yayi nasara kam. Don haka a shawarce kuma a
sunnance an so musulmi ko musulma suyi koyi da sunnar da Ma'aiki SAW yake a
wannan ranar da aka haifeshi wato azumtar ranar. Wannan ita ce sunnah
Mu'akkhada da ya kamata mu Dabbaqa a maimakon tuno haihuwarsa duk bayan kwanaki
360 wanda Sahabbai, Tabi'ai da Tabi'uttabi'un basu taba hakan ba. Har yanzu
banga hujjar da akace sunyi Maulidi ba haka kuma ko a Akhdari, Ishmawy, Iziyya,
Risala babu wani babi na Maulidin Annabi SAW
Bai kamata a muyi kwaikwayo da nasara ba wanda
suke murnar haihuwar Annabi Isah A.S a kowacce shekara, ranar 25 na kowanne
watan December wanda shima din bai ingantaba kamar yanda binciken malaman
tarihi ya tabbatarda hakan. Wannan yana daya daga cikin dalilan da yasa Annabi
SAW ya ce kada ku dinga kaini matsayin da ban kai ba kamar yanda mutanen Dan
Maryam (Isah AS) suke allantardashi. Ku kirani Abdallah kuma Rasulullah. Kamar
Annabi SAW ya san hakan zata faru la'akarida yanda zakaga a wajen maulidin ana
kai shi matsayin Allah SWT wasuma suna cewa yana halartar wajen maulidin. Wanda
da zai bayyana a zahiri to da tun a lokacin sahabbai ya bayyana ya sasanta
rigimar cikin gida da ta wakana tsakanin Sayyadina Aliyu RA da Mu'awiya RA a
lokacin khilafa. To amman Idan Allah SWT ya fahimtarda mutum addini to ya huta
kam. Kamar yanda hadisin Ibn Majah ya tabbatarda hakan
(Ibn Majah littafina 3 lambata 3606)
Muna roqon Allah SWT ya rabamu da qirqiro bidi'ah,
domin kuwa dukkan bidi'ah batace kuma dukkan bata zai kai mutum zuwa wutane.
Wannan hadisine wanda Abu Hazim (Muhammad bin Hazim) ya rawaito daga Abu
Hurairah shi kuma yaji daga bakin Ma'aiki SAW
(Musnad Imam Ahmad hadisi mai lambata 219). Dukda
dai malamai sunce da'ifin hadisi ne saboda raunin Abu Hazim a bangaren ruwaya
amman ma'anar hadisin (matn) haka yake saboda hadisai mutawatirai sun
tabbatarda Annabi SAW yana cewa "Dukkan bidi'ah batace dukkan bata zaikai
mutum zuwa wuta" a kowacce Khutbatul Haja da zaiyi
Amman tabbas mutum ya qwaqwule gini da yan
yatsunsa shi ne yafi sauqi a kan son zuciyarsa domin kuwa muma mun taba maulidi
a dacan kafin musan matsayinsa a addini
Abinda ya dace ayi shi ne abinda Annabi SAW yakeyi
wato azumtar ranar haihuwarsa. Shin munayi ?
Wallahu ta'ala a'alam
Amsawa:
Usman Danliti Mato (Usmannoor_As-salafy)
Questions And Answers According To Qur'an And
Sunnah. Join Us...
𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇
https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi
𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177
𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇
https://chat.whatsapp.com/Du5LNx31U9hDi6RQbbrzgW
ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ
**************************
Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.