Ticker

6/recent/ticker-posts

Hukuncin Saurayin Da Ya Ɗaura Budurwasa A Hanyar Fasikanci

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Wani ne suka yi soyayya da wata yarinya, hasali baidai Yi Zina da ita ba Amma sun rinka soyayya wadda ta saɓa ma shari'a, Karshe sun rabu, Shi ya Zama bawan Allah nagari, salihi, Amma ita daganan ta cigaba sosai yanzu haka yarinyar tazama karuwar gida, Shin ya zaiyi, shi ne ya Zama sanadiyyar fadawar ta ga hakan.

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

Bābu wani mutum da zai yi wa wani nuni zuwa ga wani aiki face sai ya samu kamasho na sakamakon wannan aiki duk lokacin da aka aikata.

Wanda ya lalata mace ya ɗora ta a hanyar fasiqanci, har ya kasance ta saba da abin, to zai cigaba da samun kamasho a duk lokacin da ta yi fasiqanci da wani, koda kuwa bayan ya mutu, domin shi ne ya yi sanadiya ko ya fara jefa ta a cikin wannan hali.

Zina tana da wahalar bari ga wanda ta ratsa ruhinsa. Shiyasa Aʟʟαн() Ya ce:

وَلَا تَقۡرَبُوا۟ ٱلزِّنَىٰۤۖ إِنَّهُۥ كَانَ فَـٰحِشَةࣰ وَسَاۤءَ سَبِیلࣰا ٢٣۝

Kuma kar ku kusanci zina. Haƙiƙa! Ita alfasha ce, kuma mummunar hanya ce. (Surah Al-Israai: 32)

Allah Mai ilimine a kan komai, Ya san cewa idan mun kusanci zina za mu iya afka mata, kuma barinta ya fi fara ta wahala.

Duk da cewa shi be aikata zina da ita ba, amma ai shi ne ya ɗora ta a hanya, shi ya kusanto da ita zuwa ga zunubin, don haka ba zai tsira daga zunubin da take samu ba.

Tunda shi yanzu ya tuba ya gyara ayyukansa, wajibine ya same ta ya yi mata wa'azi. Kamar yadda be ji kunyar saɓa wa Allah tare da yarinyar ba, kada ya ji kunyar zuwa ya yi mata nasiha. Ya yi iya bakin 'kokarinsa wajen fahimtar da ita hatsarin abin da take aikatawa tare da azabar da Ubangiji Ya tanadar wa mazinata.

Idan ta ji tsoron Allah ta daina, to madalla. Idan kuma ba ta daina ba, Allah Ya ga zuciyarsa, sai ya cigaba da istigfari da yawaita ayyukan alkhairai, tare da yin ayyuka masu gudana da za su amfanar da shi har bayan mutuwarsa. Tabbas Allah Mai yawan gafara ne.

WALLAHU A'ALAM

Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance Damu...

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://chat.whatsapp.com/GUq2GCCzlcdL6nknqLYYox

𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam

Post a Comment

0 Comments