Ticker

6/recent/ticker-posts

Na Manta Banyi Sallar Isha'i Ba Sai Washegari Na Tuna

TAMBAYA (17)

Aslm mlm ykk dafatan kana cikin koshin lfy namanta jiya banyi sallar isha'i ba kuma nayi sallar asuba da azahar sai na tuna yazanyi

AMSA:

Waalaikumussalam. Warahmatullahi. Wabarakatuhum.

To dan uwa, zaka rama sallarne daga lokacin da ka tuna saboda kanada uzurin mantuwa kuma Allah SWT baya kallafawa bawanSa abin da bazai iya ba kamar yanda hujjar hakan tazo a cikin Qur'ani mai girma, Suratul Baqara ayata 286 (Amanar rasulu):

لَا يُكَلِّفُ اللَّهُ نَفْسًا إِلَّا وُسْعَهَا

البقرة (286) Al-Baqara

Allah ba Ya kallafa wa rai fãce ikon yinsa

Hujja ta biyu:

An karbo daga Abu Hurairah RA, Annabi SAW ya ce: "Duk wanda ya manta baiyi sallar farillah ba to ya ramata da zarar ya tuna, babu wata kaffara sama da hakan"

(Muslim 831)

Wallahu ta'ala a'alam

Amsawa:

Usman Danliti Mato (Usmannoor_As-salafy)

Question and Answers in Islam

Post a Comment

0 Comments