Ticker

6/recent/ticker-posts

Nayi Addu'ar Kwanciya Bacci Sai Aka Kirani Aka Aikeni

TAMBAYA (15)

assalamu alaikum warahamatullahi wabarakatuhu uncle inawuni yagida dan allah uncle tambayata itace akan adduar kwanchiya barchi  kamar yanzu zan kwanta sainai addua nakwanta tokafin nai barchi sai akakirani aka aikeni to idan nadawo sai nasake yin adduar kokwan chiya zanyi allah yakara lafiya

AMSA:

Waalaikumussalam. Warahmatullahi. Wabarakatuhum.

An samu sabanin malamai dangane da wannan mas'alar

Duk a cikin addinai babu addinin da yakai musulunci sauqi. Shine kadai addinin da aka tsara shi kan tafarki madaidaici sannan kuma shine addinin da idan kayi niyyar aikata abun alkhairi kuma ko da baka aikataba to Allah SWT zai baka ladan wannan niyyar kamar yanda hadisin da aka karbo daga Abu Hurairah RA ya tabbatar da hakan

(Sahihul Bukhari 7463)

A yanda na fahimta aiken da akai maka ba wajene mai nisa ba. Zata iya yiwuwa cikin gidane, kofar gida ko kuma iyaye su aikeka yin siyayya a kanti.

Idan daya daga cikin hakan ta kasance saika tuno da hadisin dake cikin Sahihul Bukhari (1:1) da Sahih Muslim (1:19) wanda aka karbo daga Abu Hurairah RA, Annabi SAW ya ce: "Ayyuka suna karbuwane da niyya, kowanne mutum zai samu abin da yayi niyyane"

Da ace bakayi niyyar addu'arba da bazaka karanta ba don haka kenan da niyyar da kuma aiken da akai maka duk qaddarace daga Allah SWT kuma da akwai hikimar da tasa Allah SWT ya tsara za a aikekan, mai yiwuwa Allah SWT yana son ka kara maimaita addu'o'inne domin kuwa Allah SWT yana son bawanSa ya roqeShi

Tunda kayi niyya a karon farko kuma kayi addu'o'in to kamata yayi yayinda ka dawo shimfidarka ka sake maimaita wadannan azkar din

Dalilai anan sune:

1) A cikin littafin Zaadul Ma'ad (Guzirin Ranar Lahira) wallafar Imam Ibn al-Qayyim al-Jauziyya ya kawo babin yada sallama ga musulmi wanda a ciki ya kawo sahihin hadisin da Annabi SAW ya ce: Idan ka hadu da dan uwanka musulmi kayi masa sallama sannan idan zaku rabu ma kayi masa sallama, sallamar farko bata fi ta karshen ba (Bi ma'ana duk sanda kayi masa cikakkiyar sallama zaka samu cikakken lada 30) haka kuma idan kuna tafiya ku biyu sai bishiya ta shiga tsakaninku (daya yabi ta dama daya yabi ta hagu to idan kun sake haduwa anason ku yiwa juna sallama) Kenan anan ana nuna falalar yawaita sallama ga yan uwa musulmai to kamar hakane idan ka maimaita azkar dincan

2) Duk sanda ka karanta "Mu'awwidathayn" (Surorin neman kariya) wato Falaqi da Nasi to kowanne harafi kanada lada 10 to kaga kenan zata iya yiwuwa Allah SWT yana son ka da alkhairin samun ladan karantasu sau uku da farko sannan kuma dai sau uku silar wancan aiken da ya qaddara za a yi maka

3) Karantawa a karo na biyu zai kawar maka da wasiwasi (akan kayi azkar din ko kuwa bakayi ba) wanda shikuma wasuwasi daga shaidanne kamar yanda ya tabbata a Qur'ani (Daga sharrin mai sanya wasuwasi, mai boyewa. Suratu Nas ayata 4) kaga idan ka karanta a karo na biyu din saikafi samun nutsuwar zuciya kuma daman da ambaton Allah ne kadai zuciya take samun nutsuwa kamar yanda Allah SWT ya fada a cikin Suratu Ra'd ayata 28

4) Idan aka ce za a bawa mutum miliyan goma (N10,000,000) ya irga ta a cikin mashin din irga kudi (counter) duk miliyan daya za a biyashi naira dubu daya (1,000) kaga kenan sakamakon irga miliyan 10 zai samu ladan dubu 10. Indai har mutum zai ji dadin wannan sallama da za a yi masa a cikin yan mintuna kadan to la shakka da za a nunawa mutum lada daya tal na karatun haruffan (Qul...) to da kwadayi zai maimaita su har sai ya gaji sannan ya kwanta bacci

A karshe, ko da ya dawo aiken ya manta bai sake maimaita azkar din ba har kuma bacci ya daukeshi to in sha Allahu zai samu kariyar Allah SWT a wannan daren silar wancan niyyar da yayi ta farko

Wallahu ta'ala a'alam

Amsawa:

Usman Danliti Mato (Usmannoor_As-salafy)

https://chat.whatsapp.com/J1hm5Tw12uYBqfaiPwf28l

Question and Answers in Islam

Post a Comment

0 Comments