Ticker

6/recent/ticker-posts

Na Tuba Daga Aikata Zina, Shin Allah Zai Yafe Min?

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Assalamu'alaikum. Malam tambayana anan shine: Nine nakeda budurwa muna tare har yakai ga mukayi zalunci (ma'ana muka sadu da juna har ta samu juna biyu daga karshe taje ta cire) gashi ni kuma ban taɓa yin zina ba. Daga nan hankalina ya tashi! tun daga wannan lokaci nakasa samun kwanciyar hankali sabida muninsa. Hatta lokacin da abin ya auku nayi nafila da istigfari ina me zubar da hawaye da nadaman abin da ya faru. Tunda nake ban taɓa yin abin da nayi nadama kamar wannan ba. Aman malam tun daga nan ban sake ba, na tuba inata neman gafaran ubangiji. Malam hakan ALLAH ze yafe min duk da abin da ya faru na cire cikin?

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

Wa alaikumus salam wa rahmatullahi wa barakatuhu.

Duk da cewa waɗannan laifukan da kuka aikata suna daga cikin mafiya girman laifukan da Allah ya haramta, Kuma ya gargadi bayinsa akansu, to amma wannan ba yana nufin cewa Allah ba zai gafarta muku bane.

Mutukar kunyi tuba irin tubar da Allah yake so, to tabbas Allah zai gafarta muku waɗannan laifukan. Allah Madaukakin Sarki ya gaya ma Annabinsa (sallal Lahu alaihi wa aalihi wa sallam) cewa:

قُلْ يَا عِبَادِيَ الَّذِينَ أَسْرَفُوا عَلَىٰ أَنْفُسِهِمْ لَا تَقْنَطُوا مِنْ رَحْمَةِ اللَّهِ ۚ إِنَّ اللَّهَ يَغْفِرُ الذُّنُوبَ جَمِيعًا ۚ إِنَّهُ هُوَ الْغَفُورُ الرَّحِيمُ ٣٥۝

Ka ce: (Allah Ya ce): "Yã bãyĩNa waɗanda suka yi ɓarna a kan rãyukansu! Kada ku yanke ƙauna daga rahamar Allah. Lalle Allah na gãfarta zunubai gabã ɗaya. Lalle Shĩ, Shĩ ne Mai gãfara, Mai jin ƙai." (Suratuz Zumar ayah ta 53).

Imamu Ahmad ya ruwaito wani hadisi acikin Musnadu nasa (Juzu'i na 4 shafi na 385) daga Sayyiduna Amru bn 'Abisah (rta) ya ce : "Wani mutum yazo wajen Manzon Allah tsoho ne Tukuf, yana dogarawa da sandansa. ya ce : "Ya Rasulallahi hakika ni ina da wasu Laifukan yaudara da kuma Fajirci waɗanda na aikata. Shin za a gafarta min kuwa?".

Sai Manzon Allah ya tambayeshi "Shin baka shaida cewa babu wani abin bautawa da gaskiya sai Allah ba?".

Sai mutumin ya ce "Eh, Kuma na shaida cewa Kai Manzon Allah ne".

Sai Manzon Allah ya ce masa "An riga an gafarta maka laifukanka na yaudara da kuma fajirci".

Al Imam Ibnu Katheer ya ce duk waɗannan ayoyin da hadisan Manufarsu ita ce a fahimci cewa Allah yana gafarta dukkan Zunubai amma bisa sharadin tuba. Kuma kada wani bawa ya yanke tsammani daga samun rahamar Allah. Domin rahamar Allah mayalwaciya ce.

Bisa waɗannan Hujjoji nake Qara jan kunnenka da cewa ka yawaita tuba tare da cikakkiyar nadama. Kuma ka nisanci dukkan wasu ayyukan saɓon Allah. Kuma ka yawaita istighfari da ayyukan alkhairi ko yaushe. Da sannu waɗannan ɗin zasu zama dalilin kankare wadancan kusakuren naka._

Kuma ina baka shawarar cewa kayi kokari kayi aure domin kiyaye mutuncinka da addininka. Kamar yadda Annabi yayi umurni kuma ya kwaɗaitar da al'ummarsa.

Allah ta'ala ya tsare maba imanimmu

WALLAHU A'ALAM

Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance Damu...

𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

Question and Answers in Islam

Post a Comment

0 Comments