Ticker

6/recent/ticker-posts

Nafilar Jumma’a A Haraba

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Assalaamu Alaikum Wa Rahmatul Laah. Tambaya ce a kan wanda ya zo ya tarar da liman yana huɗuba, ko zai iya yin nafilarsa a haraba tun da bai samu cikin masallaci ba, ko kuwa ba zai yi ba?

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

Wa Alaikumus Salaam Wa Rahmatul Laahi Wa Barakaatuh.

Malamai suna da amsoshi mabambanta a nan:

1. Tun da dai an yarda cewa wannan sallar Tahiyyatul Masjid ce, shiyasa waɗansu suka kafe a kan cewa ba makawa sai dai a yi ta a cikin masallaci kawai, amma ba a haraba ko a wani wurin ba. Domin lafuzan hadisin abin da suka nuna kenan:

Al-Imaam Al-Bukhaariy ya ƙulla babi a cikin Sahihin Littafinsa ya yi masa suna:

باب إِذَا دَخَلَ الْمَسْجِدَ فَلْيَرْكَعْ رَكْعَتَيْنِ

Baab: Idan ya shiga masallaci to sai ya yi sallah raka’o’i biyu.

Sannan ya kawo hadisin Abu-Qataadah As-Sulamiy (Radiyal Laahu Anhu) cewa: Manzon Allaah (Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallam) ya ce:

 « إِذَا دَخَلَ أَحَدُكُمُ الْمَسْجِدَ فَلْيَرْكَعْ رَكْعَتَيْنِ قَبْلَ أَنْ يَجْلِسَ »

Idan ɗayanku ya shiga masallaci, to ya yi sallah raka’o’i biyu kafin ya zauna. (Sahih Al-Bukhaariy: 444, Sahih Muslim: 1687, Sunan An-Nasaa’iy: 738, Sunan Ibn Maajah: 1065, 1066)

Sannan Al-Imaam Muslim ya sake riwaitowa daga Abu-Qataadah ɗin dai (Radiyal Laahu Anhu) cewa:

Na shiga masallaci alhali Manzon Allaah (Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallam) yana zaune a tsakanin mutane, sai ni ma na zauna. Amma sai Manzon Allaah (Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallam) ya ce: ‘Me ya hana ka yin raka’o’i guda biyu kafin ka zauna?’ Na ce: Manzon Allaah! Na gan ka a zaune ne, kuma mutane ma duk suna zaune. Sai ya ce:

« فَإِذَا دَخَلَ أَحَدُكُمُ الْمَسْجِدَ فَلاَ يَجْلِسْ حَتَّى يَرْكَعَ رَكْعَتَيْنِ »

Idan dai ɗayanku ya shiga masallaci, to kar ya zauna har sai ya yi raka’o’i guda biyu. (Sahih Muslim: 1688)

Amma kuma wannan hadisin na Abu-Qataadah ya zo da wani buɗaɗɗen lafazi, kamar yadda waɗansu daga cikin malaman Sunan suka riwaito cewa:

« إِذَا جَاءَ أَحَدُكُمُ الْمَسْجِدَ فَلْيُصَلِّ سَجْدَتَيْنِ مِنْ قَبْلِ أَنْ يَجْلِسَ »

Idan ɗayanku ya zo masallaci, to sai ya yi sallah raka’o’i biyu kafin ya zauna. (Sunan Abi-Daawud: 467, Sunan At-Tirmiziy: 317, kuma ya ce: Sahihi ne, kyakkyawa).

Daga wannan mun gane cewa:

Wanda ya zo masallacin kuma ya yi sallar nafilarsa a haraba domin masallaci ya cika, ba za a ce ya saɓa ko bai kyauta ba, in Shã Allãh.

Har shi ma Hadisin Sulaik Al-Ghatfaaniy (Radiyal Laahu Anhu) wanda ya zo a ranar Jumma’a, an riwaito shi da irin wannan lafazin daga riwayar Jaabir Bn Abdillaah (Radiyal Laahu Anhumaa) ya ce:

 جَاءَ سُلَيْكٌ الْغَطَفَانِىُّ يَوْمَ الْجُمُعَةِ وَرَسُولُ اللَّهِ - صلى الله عليه وسلم - يَخْطُبُ فَجَلَسَ فَقَالَ لَهُ « يَا سُلَيْكُ قُمْ فَارْكَعْ رَكْعَتَيْنِ وَتَجَوَّزْ فِيهِمَا - ثُمَّ قَالَ - إِذَا جَاءَ أَحَدُكُمْ يَوْمَ الْجُمُعَةِ وَالإِمَامُ يَخْطُبُ فَلْيَرْكَعْ رَكْعَتَيْنِ وَلْيَتَجَوَّزْ فِيهِمَا ».

Sulaik Al-Ghatfaaniy ya zo a ranar Jumma’a alhali Manzon Allaah (Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallam) yana cikin huɗuba sai ya zauna. Sai ya ce masa: ‘Sulaik! Tashi ka yi sallah raka’o’i biyu, kuma ka taƙaita karatu a cikinsu. Sai kuma ya ce: Idan ɗayanku ya zo a ranar Jumma’a alhalin liman yana cikin huɗuba, to ya yi sallah raka’o’i biyu, kuma ya taƙaita karatu a cikinsu. (Sahih Muslim: 2061)

A wannan lafazin cewa ya yi: ‘Idan ɗayanku ya zo…’ Bai ce: ‘In ya shigo…’ irin na riwayoyin da suka gabata ba.

Don haka, matuƙar dai mutum masallacin Jummaar ya zo, ko ya samu cikin masallacin ko bai samu ba, umurnin da Annabi (Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallam) ya ba shi dai kenan cewa: Ya yi sallah rakaoi biyu gajajjeru.

Wannan kenan.

Kuma ai abu ne sananne cewa Masallacin Harami kamar na Makkah Al-Mukarramah a yanzu gini ne hawa-hawa: Akwai gine-gine wani a kan wani ta sama, akwai kuma gini a ƙarƙashin ƙasa waɗanda akan buɗe wa masu sallah a lokacin cunkuson jama’a, kamar a lokutan aikin Hajji. To, yanzu Alhajin da ya shiga waɗannan wuraren na sama ko na ƙasa shi ba a Masallacin Harami ya shiga ba? Shi ba zai samu ladan nan dubu ɗari (100,000) da aka faɗa ba? Kuma sai a ce: Ba zai yi nafilar Jumma’ar a wurin ba?!

Sannan kuma malamai sun tabbatar da cewa: Filin da ke kewaye da masallaci, da ginin da ke a sama da masallaci, da ginin da ke a ƙarƙashin ginin masallaci, da sauran ɗakunan da katangar masallaci ta kewaye su, waɗanda kuma aka gina domin yin sallah a cikinsu a lokacin cunkoson jama’a, duk suna ɗaukar hukuncin cikin masallaci ne.

Dubi litaffan fatawoyin manyan malamai kamar su: Fataawaa As-Shaikh Ibn Baaz: 10/221 da Fataawa As-Shaikh Ibn Uthaimeen: 14/351 don ƙarin haske.

WALLAHU A'ALAM

Sheikh Muhammad Abdullaah Assalafiy

Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance Damu...

𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

Question and Answers in Islam

Post a Comment

0 Comments