Ticker

6/recent/ticker-posts

Shin Ya Halatta Mace Tayi Abin Da Zata Mallake Mijinta Ko Saurayinta?

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Assalamu alaikum malam ya fama da jama'a Allah ya taimaka, Tambayata itace ya halatta ga mace tayi abin da zata mallake mijinta ko saurayinta?

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

Ya halatta matar Aure ko budurwa ta mallake mijinta ko saurayinta, Wanda zai aureta. Musamman ma mace mai aure, ya zama wajibi ta mallake mijinta. Amma ta hanyar da babu sihiri ba, ba tsafi, ba dawo, ba Tsubbu, ba yaudara, ba nuna masa Abin da ba shine a zuciyarki ba.

Sai dai ki Mallakeshi ta hanyar kyautatawa, bin umarninsa, amfani da kuɗin ki wajen kyautata masa, yimasa magana mai daɗi, Nuna masa tsabar gaskiya a cikin Zantukanki da Ayyukanki da shigar ki da mu'amalar ki da dai sauransu.

Allah ta'ala yasa mudace

WALLAHU A'ALAM

Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance Damu...

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://chat.whatsapp.com/FmJ5Ojsns1KFolTP8qu9GT

𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

Question and Answers in Islam

Post a Comment

0 Comments