TAMBAYA (16)❓
Dan Allah inada tambaya akan ayar datake magana
aakan dalilin dayasa ake neman ilimi aha ko hadisi ngd
AMSA:
Neman ilimi fardu ayn ne ba fardu kifaya ba bi
ma'ana ya zama dolene wani daya daukewa wani, shiyasa ba'a gadon ilimi saidai
mamaci ya tafi da abinshi. A takaicedai yakamata musa a ranmu cewar:
(طلب العلم فريضة علي كل مسلم ومسلمة)
Hujjar dalilin neman ilimi tana cikin ayar da
Allah SWT ya turo Mala'ika Jibrilu AS wadda aka cirota daga Lauhul Mahfuz zuwa
Baitul Izza (Ka'aba dake sama ta daya) wadda itace aka fara saukarwa zuwaga
Annabi SAW wato Suratul Alaq aya ta farko:
( اقْرَأْ بِاسْمِ رَبِّكَ الَّذِي خَلَقَ
)
العلق (1) Al-Alaq
Ka yi karatu da sunan Ubangijinka, wanda Ya yi
halitta.
Hujja ta biyu kuma, itace wata aya: a lokacin da
ake yiwa Annabi SAW wahayin Qur'ani ya kasance idan Mala'ika Jibrilu AS ya
karantardashi sai ya dinga karantawa da sauri don gudun kada ya manta sai Allah
SWT ya saukarda wannan ayar:
( فَتَعَالَى اللَّهُ الْمَلِكُ الْحَقُّ ۗ وَلَا تَعْجَلْ بِالْقُرْآنِ مِن قَبْلِ أَن يُقْضَىٰ إِلَيْكَ وَحْيُهُ ۖ وَقُل رَّبِّ زِدْنِي عِلْمًا )
طـه (114) Taa-Haa
Sa'an nan Allah Mamallaki, Tabbatacce Yã ɗaukaka. Kuma kada ka yi gaggãwa da Alƙur'ãni a gabãnin a ƙãre
wahayinsa zuwa gare ka. Kuma ka ce: "Yã Ubangiji! Ka ƙãra
mini ilmi."
Iya wannan ayar kadai ta isa kafa hujja da neman
ilimi ga kowanne musulmi. Akwai kuma hujja ta uku, wato: ayata 25 har zuwa ta
28 (a cikin dai Sura ta 20 din) inda Annabi Musa AS yake roqon Allah ya buda
masa kirjinsa (da ilimi)
( قَالَ رَبِّ اشْرَحْ لِي صَدْرِي )
طـه (25) Taa-Haa
Ya ce: "Ya Ubangiji! Ka buɗa mini, ƙirjĩna.
Haka kuma akwai sahihin hadisi wanda Annabi SAW ya
ce: "Neman ilimi wajibi ne ga kowanne musulmi"
Tirmidhi Chapter 10 Hadisi mai lambata 2614
Sannan hadisin yazo a cikin Sunan na Ibn Majah da
kuma Musnad na Imam Ahmad
Shi ilimi baya buya haka ma jahilci baya buya.
Misali: Ibn Sina (Rahimahullah) ya kasance shahararren masanin lafiya wanda
akewa laqabi da Yariman likitoci (Prince of Physicians) kuma har yanzu jami'o'in
duniya suna kafa hujja da littafinsa mai suna Littafin Likitanci (The Book of
Medicines) wanda Lorry Dowsing ya ce "Duk wanda yaje asibiti ya amshi
magani ya warke to ya zama tilas yayi addu'a ga Avecina (Yana nufin Ibn Sina)
kuma a cikin Qanun na Ibn Sina shi dai Lowry Dowsing din ya fitarda mujalladi
(Volume) na littafinsa ya kawo sunan Ibn Sina a matsayin abin kafa hujja. Da
neman ilimi ba abune mai muhimmanci ba da kafirin likitancan bazai kafa hujja
da littafin musulmin likita ba
Irinsu ibn al-Haitham balaraben da ya kirkiro
camera ta daukan hoto mawallafin littafin Kitabul Manazir (Book of Optics),
irinsu al-Khawarizimi dan kasar Persia wanda ya kirkiro concept din linear da
quadratic equation da kuma Algebra, ga
al-Kindi wanda ya kirkiro sufuri (zero:0), ga irinsu al-Idrisi balaraben da ya
fara fitarda taswira (map) din duniya, shine ya wallafa littafi Tabula Rogerina
(Book of Roger) littafin da Sarkin Norman Roger II ya sahale fitarsa mai
daukeda taswirai 70 da suka kunshi geography climates dakuma dabi'un al'umma
daban daban, irinsu Abu Abdullah Muhammad Ibn Batuta dan kasar Morocco wanda ya
share wajen shekaru 30 yana zagaye kasashen duniya dayawa tareda tattaro ilimin
da ya samu ya wallafa littafi mai suna "Rihla" ma'ana tafiye-tafiye
(travels)
Abbas Ibn Firnas, likita, mawaqi, engineer
kasar dan Andalusia, shine engineer na
farko wanda ya fara gwaji akan yiwuwar mutum zai iya shawagi a sama kamar
tsuntsu, wanda yayi wasu yan hikimomi (ya daure jikinsa da wasu sassan ressan
bishiya kamardai fuka-fukai) ya hau saman gini ya fado sai gashi yana shawagi a
sama kamar tsuntsu wanda silar hakan aka bude kofar binciken da har aka kirkiro
jirgin sama. Shine ya kirkiro agogon ruwa dakuma alhariri a jikin garaya ta
dinga fitarda sauti (guitar). Ibn Firnas yayi tadabburine da ayoyin Qur'ani
kamar irinsu aya ta 19 dake cikin Suratul Mulk inda Allah SWT ya ce:
( أَوَلَمْ يَرَوْا إِلَى الطَّيْرِ فَوْقَهُمْ صَافَّاتٍ وَيَقْبِضْنَ ۚ مَا يُمْسِكُهُنَّ إِلَّا الرَّحْمَٰنُ ۚ إِنَّهُ بِكُلِّ شَيْءٍ بَصِيرٌ )
الملك (19) Al-Mulk
Bã zã su yi dũbi ba zuwa ga tsuntsãye a kansu,
mãsu sanwã, kuma suna fiffikãwa, bãbu mai riƙe da su sai (Allah),
Mairahama? Lalle shi Mai gani ne ga dukan kõme.
Hatta mata ma ba'a barsu a baya ba, irinsu Zaynab
bint al-Kamal, yar Baghdad dake kasar Iraq, tayi rayuwa a karni na sha uku
(13th century) itace mace ta farko da ta zamo likita mai lasisi kuma itace ta
gina asibiti mai suna Dar al-Shifa (house of healing) bi ma'ana "Gidan
waraka" wanda har yanzu ana amfana dashi. Likitar (Zainab) ta wallafa
littattafai na lafiya kuma ta shiga tarihin wadanda suka bada gudunmawa a
duniyar ilimin lafiya, an girmamata a zamaninta silar bude kofar neman ilimi ga
mata. Kalubale ga matan wannan zamanin wanda a maimakon a nemi ilimi ayi aiki
da shi saidai a share awanni anata kallon fina-finai da sauraren kade-kade
wadanda bazasu amfanar da su anan duniyarba ballantana acan lahira
Dukkan wadannan bayin Allah wadanda kusan shekara
duba da ta wuce sun duqufane wajen neman ilimi da kuma yadashi. Indai muma zamu
duqufa muyi da ikhlasi mu cire riya to tabbas wataran sai sunanmu ya shiga
tarihin masana
Ya Allah ka bamu ilimi mai amfani wanda zai zamo
sadaqatul jariya
Wallahu ta'ala a'alam
Amsawa:
Usman D. Mato (Usmannoor_As-salafy)
Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku
kasance Damu...
𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇
https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi
𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.