Mun Aikata Zina Sanadiyyar Iyayensa Sun Ki Amince Muyi Aure

    𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

    Salamu alaikum. Nakasance ina soyayya da me mata sai ze karani akan matarsa Sai yagaya da mahaifiyarsa Sai tace bazata yarda ba. Mukuma muna matukar son juna hakan tasa muka aikata zina har nasamu juna biyu kuma nasha magane nazubar da Wannan cikin kuma haryau muna tare kuma mamashi tace sam bazata yarda ba. shin Mallam Allah zai karbi tubana ya yafemini laifi da nayi? shin mamashi nada laifi ko batada mlm inah bukatar. Addu'a da zandinga yi domin Naga nafidda soyayarsa acikin zuciya na. sai Naji ka ahuta lafiya.

    𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

    Wa'alaikum salam.....

    Kowacce uwa da kowanne uba, suna da damar da zasu hana ɗansu ya auri matar da ya gadamar aurenta, idan har sun fahimci akwai matsala. Sabida nan gaba matsalar kansu zata dawo a matsayinsu na mahaifansa.

    Kasancewar ki a matsayin budurwarsa ta yaya kika bashi kanki, har yayi zina da ke, yayi miki ciki?

    Maganar gaskiya akwai matsala, ba mamaki iyayensa sun fahimci cewar ke ɗin ba ta kirki bace, domin abin da babba ya hango, yaro bazai hango ba.

    Matar kirki bata yarda da duk wani ɗan iska yayi iskanci da ita. Domin yanzu an dena yin aure sai an zurfafa bincike na kwarai, Sabida auren baragurbi wanda ba na gari ba, ko wadda ba ta gari ba.

    Sannan maganar uwarsa ko tana da lefi? bata da wani lefi, domin ba itace ta sanyaku Ku aikata wannan fasikancin ba, kuma ba mamaki ma bata San lokacin da kukaje kuka aikata wannan fasikancin ba. Sabida a haka bata da wani lefi.

    Maganar tuba kuma, Wannna wani abu ne da yake hannun Allahu subhanahu wata'ala. Idan kin tuba kinyi nadama, Idan ya gadama ya yafe miki, idan kuma ya gadama yayi miki azaba daidai gwargwadon abin da kika aikata. Domin Allah baya zalunci.

    Allah ta'ala ya tsaremu.

    WALLAHU A'ALAM

    Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance Damu...

    𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

    https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi

    𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

    Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

    Question and Answers in Islam

    No comments:

    Post a Comment

    ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

    HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.