𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀❓
Assalaamu Alaikum Wa Rahmatul Laah. Wanda ya yi
mafarkin saduwa kuma har ya ji yanayin fitar maniyyi amma da ya farka sai bai
ga maniyyi a jikinsa ba, sai tufarsa ce kawai ta jiƙe, to wai ko zai yi
wankan janaba?
𝐀𝐌𝐒𝐀❗️
Wa Alaikumus Salaam Wa Rahmatul Laahi Wa
Barakaatuh.
Abin da Malamai suka ce shi ne, Janaba tana samuwa
ga mutum ne idan ɗaya
daga cikin waɗannan
abubuwan ya auku:
1. Fitar maniyyi daga gare shi ta hanyar babbar
sha’awar jima’i ko a barci ta hanyar mafarki, ko kuma a farke ta hanyar tunani
ko kallo ko shafan jiki ko wasanni.
2. Ɓacewar kan al’auran namiji (hashafa) a cikin na-mace
kamar a lokacin saduwa ko wasan banza, ko da kuwa ba su yi maniyyi ba.
3. Fitar maniyyi ta hanyar yin wasa da al’aura ko
ta amfani da wani inji ko wata na’ura da turawa suka ƙera musamman domin haka,
kamar ‘budurwar
roba’.
Duk wanda hakan ya same shi kuwa wankan janaba ne
ya wajaba a kansa amma ba alwala ba, saboda maganar Ubangiji Tabaaraka Wa
Ta’aala cewa:
وَإِن كُنتُمۡ جُنُبࣰا فَٱطَّهَّرُوا۟ۚ
Kuma idan kun kasance masu janaba, to sai ku yi
wanka. (Surah Al-Maa’idah: 6)
Sannan kuma Annabi (Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi
Wa Sallam) ya bayar da fatawa ga wanda yake yawaita wanka saboda fitar maziyyi
cewa:
« لاَ تَفْعَلْ ، إِذَا رَأَيْتَ الْمَذْىَ فَاغْسِلْ ذَكَرَكَ وَتَوَضَّأْ وُضُوءَكَ لِلصَّلاَةِ ، فَإِذَا فَضَخْتَ الْمَاءَ فَاغْتَسِلْ »
Kar ka yi haka. Idan dai ka ga maziyyi to sai ka
wanke al’aurarka kuma ka yi alwala irin alwalarka ta sallah. Idan kuma ka fitar
da maniyyi mai tunkuɗowa da
ƙarfi, to sai ka yi wanka. (Sahih Abi-Daawud: 206).
Wannan da ya farka ya ga tufarsa a jike, shi ma
janaba ta same shi, don haka sai ya yi wanka. Wanda Yayi Mafarki Amma Ya Tashi
Bega Komai ba wato bai fitar da maniyyi ba, To Malamai Sukace Babu Komai
Akansa, Bazeyi Wanka Ba.
Allaah ya ƙara mana fahimta.
WALLAHU A'ALAM
Sheikh Muhammad Abdullaah Assalafiy
Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku
kasance Damu...
𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇
https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi
𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177
No comments:
Post a Comment
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.