Ticker

6/recent/ticker-posts

Saki Uku Ba Tare Da Sanarwa Ba

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Assalaamu Alaikum Wa Rahmatul Laah. Miji ne Ya kasa jure irin cin mutuncin da matarsa take yi masa don haka ya tura ta gidansu da manufar ya sake ta saki uku kuma ya sanar da iyayensa hakan, amma bai sanar da ita ko iyayenta ba. Yanzu kuma ana shirye-shiryen yin sulhu wai ta dawo domin tana da ciki. To, menene matsayin wannan sakin da sulhun?

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

Wa Alaikumus Salaam Wa Rahmatul Laahi Wa Barakaatuh.

Abu na-farko shi ne: Saki dai ya auku, tun da ya riga ya ƙudurce shi a cikin zuciyarsa kuma har ya furta shi ga iyayensa.

Amma abin da ba a fayyace a cikin tambayar ba shi ne: Saki na-uku ne ko kuwa saki uku ne gaba-ɗaya?

Idan saki na-uku ne ake nufi, watau waɗansu saki guda biyu sun gabaci wannan sakin, to babu maganar sulhu har sai matar ta koma ta auri wani mijin da ba wannan da ya sake ta ba, kuma har sai in shi da zaɓin ransa ya sake ta a bayan cikakkiyar saduwar aure ta auku a tsakaninsa da ita. Saboda ayar Surah Al-Baqarah: 230.

فَإِنْ طَلَّقَهَا فَلَا تَحِلُّ لَهُ مِنْ بَعْدُ حَتَّىٰ تَنْكِحَ زَوْجًا غَيْرَهُ ۗ فَإِنْ طَلَّقَهَا فَلَا جُنَاحَ عَلَيْهِمَا أَنْ يَتَرَاجَعَا إِنْ ظَنَّا أَنْ يُقِيمَا حُدُودَ اللَّهِ ۗ وَتِلْكَ حُدُودُ اللَّهِ يُبَيِّنُهَا لِقَوْمٍ يَعْلَمُونَ ٠٣٢۝

Sa´annan idan ya sake ta (na uku), to, bã ta halatta a gare shi, daga bãya, sai tã yi jima´i da wani miji waninsa. Sa´annan idan (sãbon mijin, watau na biyu) ya sake ta, to, bãbu laifi a kansu ga su kõma wa (auren) jũna, idan sun (mijin farko da matar) yi zaton cewa zã su tsayar da iyãkõkin Allah, kuma waɗancan dõkõkin Allah ne Yana bayyana su ga mutãne waɗanda suke sani.(Surah Al-Baqarah: 230).

Idan kuwa saki ukun a cikin kalma guda ko a mazauni guda ne kamar idan ya ce: ‘Ya sake ta saki uku.’ Ko kuma ya maimaita faɗin: ‘Na sake ta’ har sau uku. A kan wannan akwai saɓani shahararre a tsakanin malamai.

Abin da ya fi daidai a fahimtar malamanmu kuwa shi ne: Sakin ya auku a matsayin saki guda ɗaya wanda yake iya yin kome a cikin iddarta. Domin haka abin ya ke tun a zamanin Annabi (Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallam) da Abubakar (Radiyal Laahu Anhu), da kuma farkon zamanin Umar (Radiyal Laahu Anhu) kafin ya bayar da fatawar da ta saɓa wa waccan ɗin, kuma aka samu saɓani a tsakanin malamai ta dalilinta. 

Don haka, idan dai irin wannan saki ukun ne, to yana iya amincewa da yin sulhun matuƙar dai matar ba ta gama iddarta ba. Watau idan ba ta haihu ko ta yi ɓarin cikin da take ɗauke da shi ba.

WALLAHU A'ALAM

Sheikh Muhammad Abdullaah Assalafiy

Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance Damu...

𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

Question and Answers in Islam

Post a Comment

0 Comments