Ba kasafai akan hangi sarakuna a kasar Hausa sun je janaza ko ta'aziyya ba, hasali ma wanda akawa mutuwa ne kan je, kafa da kafa, zuwa fada domin yiwa sarkin garin su ta'aziyya.
Sai dai Mai Martaba Sarkin Karaye, Dr. Ibrahim Abubakar, yayi wani abu irin sa na farko a tarihin dani na taba ji ko gani; daukar makara a kafadar sa domin yin rakiya ga wadda ta rasu. Hakika Sarki ya kyauta koda kuwa menene alakar sa da wadda ta rasu din.
Wannan kyakkyawan misali da Mai Martaba Sarki yayi jarumta ce, wannan kyakkyawar mu'amula ce, wannan kulawa ce, wannan saukin kai ne, wannan kauna ce ga wadanda ake mulka kuma wannan abin koyi ne.
Da fatan Allah ya sakawa Mai Martaba Sarki da alkhairi ya kara masa kusaci da talakawan sa, itama mai rasuwa Allah ya jikan ta, mu kuma ya kyauta namu karshen, amen.
Kawu Sule Rano
15-09-2021
YADAWA Comr Baba Hamza
0 Comments
Post your comment or ask a question.