Sojoji ne a Teku,
A tsuttsube nan zuwa can,
Tsaunukan jirgi na yaƙi,
Runduna nan runduna can,
A gabas Tekun Ƙasar Sin,
Sun daddasa bishiyoyi,
Na ƙayoyi masu tsini,
Dafi da gubar masifa,
Sun yi gangankon ƙasashe,
Na NATO su tara ƙarfi,
Su cure kar su karye ,
Niyarsu guda dukkansu,
Zobe su yi wa Ƙasar Sin,
Taron dangi na yaƙi,
Su yi wa jama'ar da ke Sin.
Mai ido zai gane lallai,
Ɗayan uku ne shirinsu,
A bi su cikin biyayya,
Da ƙasƙanci da bauta,
In an turje su sanya,
Sarkar hana kasuwanci,
Da al'ummar da ke Sin,
Ko su sa ƙwanji a bi su,
Cikin tilas da dole,
Ko ai yaƙin maƙamai,
Masu linzami a teku.
Rabbana kasan shirinsu,
Ka tsare mu Ilahu sarki,
Daga dukkan kaidukansu,
Kariyarmu tana gare Ka,
Dukkan mugun nufinsu,
Da zai haifar da yaƙi,
Wanda zai sa duniyarmu,
Cikin haɗari na yaƙi,
Mummuna wanda zai ja,
Duniya halaka dukkanta,
Ka rusa ya Ilahu,
Dukkan kaidinsu Allah.
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.