Ticker

6/recent/ticker-posts

Hukuncin Yin Tofi A Cikin Sallah

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Assalamu alaikum Allah ya kara ma malam lafiya, malam ina da juna biyu, to miyau na cika min bakina, to idan ina sallah sai ya cika min baki sai dai inyi karatu a zuciyata, to malam ya matsayin sallah ta take? Nagode.

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

Wa'alaikumus Salamu. Wanda ke da lallurar taruwar miyau ko kaki, ba zai zama dalilin yin karatun sallah a zuciya ba, tun da kin san kina da wannan lallurar, to abin da ya kamata ki riqa yi shi ne, duk lokacin da za ki yi sallah sai ki sami tsumma ko hankici ki riqa zuba miyau ɗin a ciki don ki sami damar yin karatun sallah kamar yadda Annabi ya ce a yi sallah kamar yadda aka ga yana yi.

Malam Abdurrahman mai littafin Akhdhariy shi cewa ma ya yi duk wanda zai tofar da wani abu in yana sallah zai tofar ne a cikin rigarsa.

Matnul Ahdhariy 64.

Akwai halascin tofar da wani abu da ya dami mutum a cikin sallah, sai dai haramun ne mutum ya yi tofi ta fuskar alqibla, ko ta ɓarin dama, saboda mai yin sallah yana ganawa da ubangijinsa ne, amma ya halasta ya yi tofi ta ɓangaren hagunsa ko a qarqashin qafafunsa, kamar yadda Anas ɗan Malik ya ruwaito daga Manzon Allah

Duba Bukhariy 413, da Muslim 551.

Allah ne mafi sani.

Jamilu Ibrahim Sarki, Zaria.

Zauren Fatawowi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance Damu...

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://chat.whatsapp.com/J1hm5Tw12uYBqfaiPwf28l

𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam

Post a Comment

0 Comments