GANDUN KALMOMI Na Shirin Gabatar Da Mujallar TANTABARA, Fitowa Ta Musamman Kan Batun – Hausa Da Hausawa A Doron Ƙasa!
Shin kuna da sha’awar rubutu ko karatu kan al’amurran da suka shafi Hausa da Hausawa, musamman abin da ya shafi tarihi ko al’adu ko harshe ko adabin Hausawa? Kuna da waɗansu rantsattsun rubuce-rubuce ko waƙoƙi da suka shafi Hausa da Hausawa? Mujallar TANTABARA na kira gare ku da ku aiko da su domin bugawa a fitowa ta musamman a cikin mujallar. Taken wannan fitowa shi ne, ‘Hausa Da Hausawa A Doron Ƙasa’ da za a wallafa a Yanar Gizo ta bazar GANDUN KALMOMI.
Mujallar na buƙatar karɓar sharhi na musamman ko waƙoƙi da suke tattauna rayuwar Hausawa jiya da yau, ko kuma bayanai da suke tattaɓa tarihin Hausawa da al’adu da adabi da harshe da siyasa da addini da zamantakewa baki ɗaya, a tsawon tarihi. Haka za mu so mu ga an aiko da sharhi kan batutuwa da suka shafi gwarazan ƙasar Hausa, ko waɗansu manyan garuruwa da biranen tarihi da duwatsu ko mazaunai na ƙasar Hausa cikin tsawon tarihi.
Ƙa’idojin Aiko Da Bayanai:
Duk abin da za a turo, a tabbata ya shafi taken wannan fitowa ta musamman, wato “Hausa Da Hausawa A Doron Ƙasa'
Babu wata ƙa’ida kan yadda za a yi rubutun ko waƙar, a dai tabbata an sa gwanintar harshe da iya rubutu domin burgewa da ƙayatarwa, ana kuma iya turo da batutuwa da suka shafi sharhi da labarai ko taƙaitaccen tarihin wani ko wata ko kuma wasu ko hira da aka yi da waɗansu daga al’ummar ƙasar Hausa.
Waƙoƙi kuwa za su iya zuwa da kowace fuska, ko waɗanda ke bin ƙa’idojin rubutun waƙa ko kuma ballagaza, madamar sun taɓo tarihin Hausa ko al’adu da al’ummar ƙasar Hausa.
Haka kuma duk wani rubutu na burgewa da tsimawa, in dai ya shafi taken wannan fita ta musamman, za su samu gurbi a ciki.
Duk rubutun da za a yi kada ya wuce kalmomi 1,500, waƙoki kuwa kada su wuce baiti 15 ɗauke da kowane tafarki na ƙwar ɗin waƙa.
Hanyar turo da saƙo:
Ana iya turo da saƙon sharhin ko waƙa zuwa ga: admin@gandunkalmomi.org
A tabbata an saƙala ‘Saƙon Bugun Mujallar TANTABARA' a cikin wasiƙar da za a haɗo.
A turo da saƙon ta manhajar WORD ba PDF ba, a kuma tabbata an sa cikakken suna da imel da ɗan taƙaitaccen tarihi na waɗanda suka turo da saƙon.
Ranaku Na Musamman:
Duk saƙonni da za a turo ana buƙatar su iso zuwa ranar 30 ga Watan Oktoba, 2023.
Za a sanar da waɗanda sharhinsu ko waƙokinsu, suka gamsar, suka kuma fi burgewa, aka kuna amince za a buga su zuwa ranar 7 ga Watan Nuwamba, 2023.
Wannan fitowa ta musamman ta Mujallar TA TABBATA za a ƙaddamar da ita a Yanar gizo a bargar GANDUN KALMOMI a wajen BIKIN BAJE KOLIN LITTATTAFAI DA FASAHOHIN HAUSAWA (HIBAF) na shekarar 2023, tsakanin ranakun 15 da 16, na watan Disamba, 2023.
Awalajar Da Za A Samu:
Mun san ba za mu iya biyan wannan gagarumin aiki da za a turo ba, amma duk da haka waɗanda aka zaɓi rubutunsu domin bugawa za su samu tukuici na musamman, kuma za a dinga ganin rubuce-rubucen nasu taskace a cikin Mujallar TANTABARA da ke fitowa a cikin GANDUN KALMOMI a kodayaushe a Yanar Gizo da ke wataye dukkan sassan duniya da ke mu’amala da Hausawa da harshe da adabi da al’adun Hausawa.
Muna kira ga zaƙaƙarun marubutan sharhi da waƙoƙi da su kasance tare da mu a wannan fitowa ta musamman in da za mu baje kolin rayuwa da tarihin Hausa da Hausawa a doron ƙasa domin musayar ra’ayi da ilmantarwa da nishaɗantarwa da taskace tarihi na har abada.
Domin ƙarin bayani sai a tuntuɓi: admin@gandunkalmomi.org
Naku a kullum,
Ibrahim Malumfashi
Babban Edita, Mujallar TANTABARA
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.