Ina Binta Bashi Sai Kudinta Ya Biyo Ta Hannuna A Rashin Saninta

    TAMBAYA (06)

    Slm malam Dan Allah tambaya ta itace mutumne kana binshi kudi sai ya hana ka kuma yana da shi sai kudinshi ya biyo ta hanninka sai ka rike kace a maimakon naka mlm yakenan

    AMSA

    Waalaikumussalam. Warahmatullahi. Wabarakatuhum.

    To da farko dai yakamata musan cewar cin bashi matsalane babba indai ba ya zama dole ba

    Idan mutum ya amshi bashi da kyakkyawar niyyar biya to ko da ya mutu Allah cikin ikonSa yakan iya bayyanawa yan uwan wanda ake bin bashin a mafarki cewar ga halin da wane yake ciki silar bashin da ya ci

    Ya tabbata a cikin Hadith al-dayn wato "Hadisin bashi", an karbo daga Abu Hurairah (RTA) ya ce: Annabi SAW ya ce: "Mutumin da ya biya bashin da ake binsa kamar wanda ya wuni yana azumi ne kuma ya kwana yana sallah"

    (Bukhari 1873, Muslim 1394, haka kuma yazo a cikin Musnad na Imam Ahmad Bin Hanbal lambata 3952 a cikin litattattafan fiqhu kuma yazo a cikin Risalar Imam al-Shafi'i hadisi mai lambata 470 da kuma littafin al-Mughni hadisi mai lambata 2052 na Ibn Qudamah)

    Idan kuma mutum ya ci bashinne ba tareda niyyar biya ba to wannan kam tun a kabari zai fara gamuwa da alhakin wanda yake binsa bashin musamman ma idan wancan din bai yafe ba

    An karbo daga Abu Hurairah (RTA). Annabi SAW ya ce "Bai halarta a sallachi gawa ba har sai an sauke mata bashin da ake binta"

    Hadisin yana cikin Sahih Muslim 1636 da kuma Sahih Bukhari 502 a cikin littafinsa na fiqhu (Adabul Mufrad) babin haramcin sallah ga wanda ake bi bashi

    Akwai littafin Muhammad Ibn Seerin (Rahimahullah) dalibin Imam Malik (Rahimahullah), littafin mai suna "Qamus din Mafarkai" wanda yayi bayanai akan fassarar mafarkai daban daban. A ciki yayi bayanin aikin Mala'ika Siddiqun (AS) wanda Allah ya wakilta a bangaren ilimin mafarkai

    Imam Ibn Seerin (wanda yayi zamani a qarni na 9) ya ce: "Idan mutum yayi mafarkin ana binsa bashi to hakan na nufin yana son ya sauke wannan bashin", ya ce "bashi a mafarki na nufin tarin zunubbai haka kuma alamune dake nuna mutum zai tuba zuwa ga Allah SWT" ya ci gaba da cewa "idan mutum yayi mafarki ana binsa bashi ya biya kuma da ya farka sai ya manta wanene yake binsa to hakan na nufin yayi wani zunubi yasani ko bai sani ba kuma illar zunubin tana tattare da shi har sai ya tuba"

    Tunda dai har kudin mallakin wanda kike bi dinne to ba laifi bane kiyi amfani dasu tunda haqqin kine

    To amman dukda haka yakamata ace kin sanarda mai kudin cewar kudinta ya biyo ta hannunki kuma kinyi amfani dasu saboda kada ta ga lokaci daya kin daina tambayarta, sai zargi ya shigo, idan kuma zato ya shigo to shaidan zai iya kimsa mata cewar kudin da kika riqe yafi adadin wanda take binki tun asali wanda hakan kan iya haifarda rigima a tsakaninku (Daman kuma Annabi SAW ya hanemu da yin zato saboda yin zato shine mafi qaryar zance)

    Hadisin yana cikin Sahih Bukhari mai lambata 6306 da kuma Sahih Muslim 3573, haka kuma yazo a cikin Sunan Abi Dawud da Sunan at-Tirmidhi)

    Shawarar da zan baki anan shine ko dai ki yafe mata kudin (musamman ma idan basuda yawa) kema sai Allah SWT ya yafe miki silar hakan ko kuma ki binciko wani ko wata wanda take jin nauyinsa ya shigo maganar domin a sasanta a biyaki haqqinki

    Idan hakan bai yiwu ba sai ki garzaya wajen hukuma domin su amsar miki haqqinki musamman ma idan kudin suna da yawa

    Wallahu ta'ala a'alam

    Subhanakallahumma wabi hamdika ash-hadu anla'ilaha illa anta astaghfiruka wa'atubi ilayk

    Amsawa:

    ✍️Usman Danliti Mato (Usmannoor_As-salafy)

    https://chat.whatsapp.com/IqsWWSpUkwk6b8hWJ6vXOO

    Question and Answers in Islam

    No comments:

    Post a Comment

    ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

    HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.