Ticker

6/recent/ticker-posts

A Ina Allah Ya Ke?

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Malam, wasu ne ke gardama cewa: Wai Allaah yana sama ne, amma iliminsa ne ke ko’ina. Wasu kuma sun ce: Allaah yana nan a ko’ina ne. Wanne ne gaskiya?

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

Malaman Bidi’a daga cikin Jahamawa da mabiyansu ne suke da ra’ayin cewa, ba za a ce Allaah yana a sama ba!

Amma a wurin malamai Ahlus-Sunnah waɗanda suka kafe a kan abin da Manzon Allaah (Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallam) ya rasu ya bar Sahabbansa (Radiyal Laahu Anhum) a kai, ba su saɓa da juna ba a kan cewa: Allaah Maɗaukakin Sarki a sama ya ke! Saboda dalilai ƙwarara a cikin Alqurani da Sunnah da suka tabbatar da haka, kamar cewa:

ءَأَمِنتُم مَّن فِی ٱلسَّمَاۤءِ أَن یَخۡسِفَ بِكُمُ ٱلۡأَرۡضَ فَإِذَا هِیَ تَمُورُ ، أَمۡ أَمِنتُم مَّن فِی ٱلسَّمَاۤءِ أَن یُرۡسِلَ عَلَیۡكُمۡ حَاصِبࣰاۖ فَسَتَعۡلَمُونَ كَیۡفَ نَذِیرِ

Shin ko kun amince ne wanda ya ke a sama ya kisfe ƙasa da ku a halin tana jujjuyawa. Ko kuwa kun amince ne wanda ya ke a sama ya aiko muku da azaba? Za ku san yadda gargaɗina ya ke!

 (Surah Al-Mulk: 16-17).

Annabi (Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallam) kuma ya ce:

أَلاَ تَأْمَنُونِى وَأَنَا أَمِينُ مَنْ فِى السَّمَاء ، يَأْتِينِى خَبَرُ السَّمَاءِ صَبَاحًا وَمَسَاءً

Yanzu ba za ku amince mini ba, alhali ni ne Amintaccen wanda ya ke sama?! Labarun sama na zuwa mini safiya da maraice?!

 (Sahih Al-Bukhaariy: 3344, Sahih Muslim: 1064).

Abu ne sananne kuwa cewa abin nufi da: ‘wanda ya ke sama’ ba kowa ba ne, in ban da Allaah Subhaanahu Wa Ta’aala .

Sannan kuma Al-Imaam Muslim ya riwaito a cikin Kitaab: Al-Masaajid, Baab: Tahreem Al-Kalaam Fis-Salaah, Lamba: 1227 da isnaadinsa sahihi har zuwa ga Sahabi Mu’aawiyah Bn Al-Hakam (Radiyal Laahu Anhu) wanda ya ce:

Ya kasance ina da wata kuyanga da take yi mini kiwon tumaki a wurin dutsen Uhudu da ƙauyen Al-Jawaaniyyah. To, wata rana da na tafi na duba sai na tarar kyarkeci ya cinye akuya guda daga cikin tumakin. Da yake ni ma ɗan Adam ne kamar sauran mutane: Ina fushi kamar yadda suke yi, sai na buge ta. Amma kuma da na dawo wurin Manzon Allaah (Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallam) na faɗa masa abin da ya auku, sai ya girmama wannan aikin da na yi. Don haka sai na ce: Manzon Allaah! Yanzu ba zan iya ’yanta ta ba?

Sai ya ce: Ka zo mini da ita. Da na zo da ita, sai ya tambaye ta:

أَيْنَ اللهُ؟

A ina Allaah ya ke?

Ta ce: A sama ya ke!

Ya ce:

وَمَنْ أَنَا؟

Ni wanene?

Ta ce: Kai Manzon Allaah ne!

Sai ya ce:

اعْتِقْهَا ، فَإِنَّهَا مُؤْمِنَةٌ

Ka ’yanta ta, domin kuwa ita mumina ce!

 (Muslim da Abu-Daawud da An-Nasaa’iy suka fitar da shi).

A nan ya fito a fili cewa: Annabi (Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallam) ya amince, kuma bai yi musu kan maganar yarinyar ba cewa: Allaah a sama ya ke!

Saɓanin yadda ya musunta wa wadda ta ce: Kuma a cikinmu akwai Annabi yana sanin gobe!!

Hasali ma dai da wannan ilimin na sanin cewa Allaah a sama ya ke, da kuma saninta cewa shi Manzon Allaah ne, ya tabbatar da imaninta har ya ce: Ka ’yanta ta, domin kuwa ita mumina ce!

Don haka malaman Aqeeda da Tawheed da suka biyo baya ba su yi sakaci ba, sai da suka tabbatar da wannan aƙidar a cikin wallafe-wallafensu, kamar yadda Ibn Abi-Zayd Al-Qairawaaniy (Rahimahul Laah) ya ce:

وَأَنَّهُ فَوْقَ عَرْشِهِ الْمَجِيدِ بِذَاتِهِ ، وَهُوَ فَي كُلِّ مَكَانٍ بِعِلْمِهِ

Kuma cewa: Shi (Allaah Ta’aala) yana a sama da Al’arshinsa mai girma da Zatinsa, kuma Yana nan a ko’ina da Iliminsa.

Allaah ya shiryar da mu ga tafarkin mutanen kirki a cikin maganganunmu da ayyukanmu na fili da na ɓoye, har zuwa ƙarshenmu.

WALLAHU A'ALAM

Sheikh Muhammad Abdullaahi Assalafiy

Zauren Fatawowi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance Damu...

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://chat.whatsapp.com/Cnf26Q8MPqz9yUYU1nxqRq

𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

Question and Answers in Islam

Post a Comment

0 Comments