Ticker

6/recent/ticker-posts

Hukuncin Yawan Waswasi Cikin Sallah

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

As Salam alaikum Malam, ina da tambaya game da yawan waswasi cikin sallah musamman idan ban sami yin Sallah a cikin jam'i ba. Sai shaiɗan yake wasa da hankalina kan ko na yi mantuwa ban cika sallar ba ko kuma na ƙara. Yaya zan yi a kan wannan lamarin?

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

Wa'alaikumus Salam warahmatullahi Wabarkatuh

Allah ya yabi bayinsa muminai acikin Suratul Mũminun dacewa:

قَدْ أَفْلَحَ الْمُؤْمِنُونَ ١۝

Lalle ne, Mũminai sun sãmi babban rabõ.

الَّذِينَ هُمْ فِي صَلَاتِهِمْ خَاشِعُونَ ٢۝

Waɗanda suke a cikin sallarsu mãsu tawãli´u ne. ( Masu nutsuwa da kushu'i acikin sallar su)

Mai yawan waswasi acikin sallah yayi kokari wajan yin sallah cikin jama'a wato tare da liman, Sannan mutum ya rika yin bakin kokarinsa wajen fitar da waswasi ko kokwanton daga zuciyarsa.

Wani lokaci yawan waswasi acikin sallah yana faruwa ne ta dalilin sakaci da shagaltuwa da sha'anin duniya da kuma rashin damuwa da Sallah, ta yadda za ka ga mutum yana sallah amma idonsa a kan hanya, ko ta window yana ganin masu wucewa. Ko kuma mutum yana Sallah amma ya kunna T.V. agabansa ko radio. (ba yaso labarai su wuceshi). Ko kuma kaga mutum yana Sallah a Masallaci amma zuciyarsa tana kasuwa. Harma wasu lokutan idan anyi Kabbara sai kaga mutum ya firgita. Azatonsa ko yaqi aka soma.😀 Hukuncin irin waɗannan Waswasin, Haramun ne. idan ma basu ɓatawa Mutum Sallarsa ba, to za su iya kaishi izuwa Rasa ladan sallar.

Wasu lokuta kuma za ka ga idan mutum yazo Sallah yana yin iyakar bakin Kokarinsu wajen Kiyayewa, amma inaa! za ka ga sun kidime sun rikice sun manta ko raka'a nawa suka yi. Irin wannan babu laifi a kan shi Mai sallan. Domin kuwa yana yin iyakar kokarinsa. Wani ma har kuka za ka ga yana yi. Kuma abin ya riga ya zama masa cuta ko larura. Mutane da yawa suna fama da irin wannan larurar.

Manzon Allah ya ce: "idan ɗayanku ya tayar da sallah, toh sheɗan zaizo yana masa waswasi acikin sallar, ko ya nuna masa cewa alwalarsa ta karye don ya ɓata maka sallah. Har wani lokacin ma ka kanji iska a tsakanin duburarka kamar kayi butu. Toh Annabi ya ce idan kaji haka kada ka katse sallarka har sai kaji doyin tusar ko kaji sautin fitar tusar.

Sannan sahabbai sun taɓa samun Manzon Allah suka ce da shi "mutum ne yana sallah zai dinga ji ana raya masa cewa 'yayi butu (tusa)' yaji ana ce ma sa alwalarka ta karye a zuciyarsa.  Manzon Allah ya ce idan ɗayan ku yaji haka toh ya ce KARYA NE!

Sannan Manzon Allah ya ce "sheɗan ba zai kyale ɗayanku ba sai ya dinga zuwa yana yi masa tambayoyi a cikin zuciyarsa. "tambayoyin da za su jefa ka cikin bala'i" yazo ya ce maka wa ya halicci sama, sai ka ce ALLAH, ya ce wa ya halicci kasa kace ALLAH, wa ya halicci kaza? Kace ALLAH, toh a karshe fa zai ce ma toh shi kuma ALLAHN wa ya halicce shi??

Toh sai manzon Allah ya ce idan kaji wannan sai ka ce:

آمنتُ باِللًهِ ورُسلُه

"Na yi imani da Allah da Manzanninsa"

ko kace:

هُوَ الْأَوَّلُ وَالْآخِرُ وَالظَّاهِرُ وَالْبَاطِنُ ۖ وَهُوَ بِكُلِّ شَيْءٍ عَلِيمٌ

"Shi ne Na farko, Shi ne Na karshe, Shi ne Bayyananne, Shi ne Ɓoyayye, kuma Shi Masani ne a kan komai.

Allah ya bamu ƙa’ida kwara ɗaya dangane da sha'anin waswasi wanda shi ne "isti'aza" wanda duk lokacin da kaji sheɗan yana taɓa maka zuciya acikin sallah toh sai kayi "isti'aza kace:

أَعُوذُ بِاللَّهِ مِنَ الشَّيْطَانِ الرَّجِيمِ

kayi sau uku kamar yadda Annabi ya koyar koda kuwa a tsaye kake a sallar ko a zaune ko cikin sujadah.

Malamai suka ce "wanda kokwanto ya aureshi, to ya rika yin sujadah bayan sallama".

Wato ka lazimta ma kanka yin sujadah bayan sallama duk lokacin da ka idar da sallah. Amma ba sai ka sake sallar ba.

WALLAHU A'ALAM

Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance Damu...

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://chat.whatsapp.com/IqsWWSpUkwk6b8hWJ6vXOO

𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam

Post a Comment

0 Comments