Published from proceedings of a Three Day 1st National Conference on Hausa Language, Literature and Culture, Organised by the Centre for the Study of Nigerian Languages, Bayero Uniɓersity, Kano, from 14th – 16th January, 2013, Page 708 – 727
English Rendition as, “Hausa Moral Behaviour as a Pillar in Building a Better Society”
Dr. Bashir Aliyu
Sallau
Department of Nigerian Languages
Umaru Musa Yar’adua Uniɓersity
Katsina – Nigeria
TSAKURE
Ci
gaban kowace al’umma yana tafiya ne tare da ire-iren tsare-tsare da
shirye-shiryen wannan al’umma dangane da yadda take tafiyar da harkokinta waɗanda suka
shafi al’adunta da aƙidunta musamman waɗanda suke da
alaƙa da tarbiyya. Dukkan al’ummar da ‘ya’yanta
ba su da kyakkyawar tarbiyya yana da matuƙar wuya ta
zauna lafiya. Idan kuwa babu zama lafiya babu yadda za a yi wannan al’umma ta
sami bunƙasar da za ta taimaka mata ta sami
dauwamammen zaman lafiya da ƙaruwar arziki
yadda kowa zai yalwata ya sami ci gaba. Domin ba da tawa gudummuwa wajen samar
da mafita ga halin da al’ummar Hausawa suke ciki a wannan zamani, ya sa a wannan
takarda za a yi bayani a kan irin kyakkyawar tarbiyyar Hausawa kafin su sami cuɗanya da wasu
baƙin al’umma, waɗanda koyi da
al’adunsu ne ya kai al’ummar Hausawa shiga cikin wannan mummunan hali da muke
ciki a yau. Domin kuwa, matuƙar aka
waiwayi kyawawan al’adun Hausawa musamman waɗanda suka
shafi tarbiyya aka yi masu ‘yan gyare-gyare, za su taimaka a sami ingantaccen
shugabanci ba a ƙasar Hausa ba kawai, a’a, har ma da Tarayyar
Nijeriya baki ɗaya. Wannan
ne zai sa Tarayyar Nijeriya da dukkan al’ummomin da suke cikinta su sami
dauwamammen zaman lafiya, a kuma sami bunƙasa, matasa
su sami abubuwan yi yadda arzikin ƙasa zai ƙara
yalwata.
1.0
Gabatarwa
Hausawa
na cewa, “zama lafiya ya fi zama ɗan sarki”, har abada ba za a sami zama
lafiya da kwanciyar hankali ba idan babu tarbiyya mai kyau. Kyakkyawar tarbiyya
ke sa a sami ingantaccen shugabanci da zaman lafiya da ƙaruwar arziki
ga kowace al’umma. Hakika, idan muka
dubi wannan bayani da ya gabata muka kuma waiwayi irin zaman da Hausawa suka yi
kafin shigowar wannan zamani, watau lokacin da suke yin cikakken riƙo
da kyakkyawar tarbiyyarsu wadda ta yi koyi da yin biyayya ga dokokin addini, da
bin gaskiya da riƙon amana, da sadar da zumunci da taimakon
juna, da yin biyayya ga tsarin shugabanci irin na Hausawa, da riƙe
sana’o’in gargajiya, da yin juriya da gwada jarunta, da nuna kunya da kara, da
kuma kyakkyawar mu’amala a tsakaninsu, sannan kuma idan muka kwatanta shi da halin
da Hausawa suke a yau, lokacin da waɗannan kyawawa al’adu suka ɓace, ma iya
yanke hukunci da cewa, watsi da kyakkyawar tarbiyyar Hausawa ne ya kai mu shiga
cikin wannan hali na rashin tabbas. Watau halin da ƙarami ba ya
yi wa na gaba da shi biyayya, don idan wata rashin jituwa ta shiga tsakaninsu, ƙarami
ba ya jin kunyar cin mutunci wanda ya girme shi ko da kuwa ya kai tsarar
mahaifinsa. Iyaye sun koma su ne ‘ya’ya, don kuwa ‘ya’yan suna juya su yadda
suke so. Zaman banza da yaudara da cuta da yin banga ga ‘yan siyasa marasa
kishin ƙasa sun zama abubuwan yi a wannan zamani.
Haka kuma, rashin gaskiya da cin amana sun zama ruwan dare, kuma ba a ɗauke su wani
abin kunya ba. Shiga cikin irin wannan hali ga dukkan al’ummar da ta san ciwon
kanta, al’amura ne waɗanda suke bukatar dubawa da idon basira don
samun mafita. Matuƙar ana son a sami
mafita dole ne a koma wa tarbiyyar Hausawa ta gargajiya da kuma ta addinin
Musulunci wanda ya yi naso cikin al’adu da ita kanta tarbiyyar ta Hausawa.
Dangane da haka, wannan takarda za ta yi bayani ne kan wasu daga cikin hanyoyin
tarbiyyar Hausawa na gargajiya waɗanda aka danganta su da na addinin
Musulunci don kawo shawarwarin da za su taimaka a sami mafita cikin wannan hali
da ƙasar Hausa da Tarayyar Nijeriya take ciki na
rashin ingantaccen shugabanci a wannan zamani.
2.0 Waiwaye a kan Tsarin Tarbiyyar
Hausawa a Jiya
Tun
lokaci mai tsawo da ya gabata kafin shigowar addinin Musulunci ƙasar
Hausa al’ummar Hausawa suke gudanar rayuwarsu cikin kwanciyar hankali da zaman
lafiya. Wannan kuwa ya faru ne saboda suna da kyakkyawan tsarin tarbiyya wanda
ya ba kowa damarsa yadda wani ba ya shiga cikin harkar da ba ta shi ba. Wannan
dalili ne ya sa ko da addinin Musulunci ya shigo ba a fuskanci wasu manyan
matsaloli ba dangane da halin zamantakewar wannan al’umma. Matuƙar
ana son kwalliya ta biya kuɗin sabulu, yadda za a sami ingantaccen
shugabanci a wannan zamani na ga ya dace a waiwayi tsarin tarbiyyar Hausawa ta
jiya.
2.1 Biyayya ga Addini
Hanyar
bauta wa wani abu wanda mutum yake tsammanin shi zai biya masa buƙatun rayuwa na yau da kullum
shi ne addini. Addinin farko na mutanen ƙasar
Hausa shi ne addinin gargajiya watau bautar gumaka. Addinin gargajiya ya faru
ne ta bin wasu hanyoyi da mutane suka ƙirƙiro wa kansu ta bautar waɗansu
abubuwa don cim ma biyan buƙatunsu.
Irin wannan hanyar bauta ta daɗe ƙwarai a dukkan sassan duniya
ba ƙasar
Hausa kaɗai ba. Mutanen da
suka fara zama a duniya ne suka ƙirƙiro ta, daga nan abin ya
zama al’ada ga sauran ƙabilun
da suke biye da su har ya zo ga Hausawa. Irin wannan addini ya sami rauni
sakamakon zuwan addinin Musulunci ƙasar
Hausa da kuma karɓar shi ga al’ummar
Hausawa. Amma duk da haka ba a bar yin wasu abubuwan da suka danganci addinin
gargajiya ba, don kuwa za a ga yakan yi naso a wasu al’amuran rayuwar Hausawa
na yau da kullum.
Ta
wannan fuska idan muka yi waiwaye muka duba yadda al’ummar Hausawa suka gudanar
da addininsu na gargajiya, za a ga ba suna sassaƙa wani gunki ne su riƙa bauta masa ba, a’a, mafi
yawancin bautarsu ta hanyar tsafi ce. Bauta ta hanyar tsafi tana nufin bauta wa
wani aljani da aka ɗauka
yana zaune a wani wuri na daban. Ire-iren waɗannan
aljannu an ɗauka suna zaune ne a
wata kwankwamar dutse, ko wata sarƙaƙƙiya, ko wurin wata tsohuwar
itaciya, misali kuka ko tsamiya ko marke da sauransu. Ire-iren waɗannan
wuraren tsafi a ƙasar
Hausa sun haɗa da wurin bautar
aljani Tsumburbura wanda aka ɗauka
ya zauna a Dutsin Dala ta Kano da Kaina-Fara-Arnan-Birchi masu bautar aljani Ɗantalle da suka ce yana
zaune a cikin Dutsin Birchi ta Ƙaramar
Hukumar Kurfi a Jihar Katsina. Arnan Kwatarkwashi kuma suna bauta wa Maiki
wanda suka ɗauka yana zaune a
cikin Dutsin Kwatarkwashi ta Jihar Zamfara. Haka kuma, a duwatsun Kufena ta
Zariya cikin Jihar Kaduna, mazaunan farko na wannan wuri sun ɗauka
a cikin waɗannan duwatsu, akwai
wasu aljannu da suke zaune a wurin waɗanda
suke biya masu buƙatunsu.
Akwai kuma arnan Suna ta ƙasar
Kwatarkwashi da kuma wasu arnan a wasu sassa na ƙasar Katsina da suke bautar
aljani Magiro wanda suka ɗauka
yana zaune a wurin tsamiya mai sarƙaƙƙiya da duhuwa wadda ba mai
iya zuwa wurin da take sai masu yin bautar wannan tsafi.
Bayan
tsafi wani nau’i na addinin gargajiya na Hausawa shi ne bori, watau bautar
iskoki ko mutanen ɓoye.
A wurin Hausawa bori tsohuwar al’ada ce, domin kuwa an daɗe
ana yin ta a matsayin addini, kuma har yanzu da addinin Musulunci ya zama jiki
ga Hausawa ba a bar yin ta ba. Hausawa sun ɗauka
ban da ma mutane, wannan duniya da muke ciki tana ɗauke
da wasu ɓoyayyun halittu masu ɗabi’u
irin na mutane. Wannan dalili ne ya sa suke kiran su mutanen ɓoye.
A saboda wasu dalilai ‘yan bori sun rarraba iskoki zuwa kashi biyu; baƙaƙen iskoki da fararen iskoki.
Baƙaƙen iskoki su maƙetata ne masu neman mutum da
sharri. Idan ana son a yi wa mutum maganin da zai mutu, ko ya haukace, ko ya
lalace, ko wani bala’i ya faɗa
masa ana neman taimakon yin haka daga baƙaƙen iskoki. Ire-iren su sun
haɗa da Uwar-gona da Baƙo da Kure da Gajimare da
Danko da Duna da Kakare. Su baƙaƙen iskoki ba a neman su sai
ta ɓaci don su ƙara ɓata
al’amari.
Fararen
iskoki kuwa na kirki ne kuma suna taimakon mutane ta hanyar bayar da dukiya da
kuma sarauta. Bugu da ƙari
kuma, suna ba mutane maganin cuce-cuce ciki har da na maganin baƙaƙen iskoki. Daga cikin fararen
iskoki akwai Sarkin Makaɗa
Dafau da Sarkin Aljan da Sarkin Rafi da Uban Dawaki da Inna (Bafulatana) da Ɗangaladima da Malam Alhaji.
Waɗannan
iskoki baƙaƙe da farare,’yan bori sun
bayyana, wasunsu na zama tare da mutane, su kuma yi abota da su. Mutanen na
hawa borinsu sai su riƙa
gaya masu magungunan wasu cuce-cuce. Haka kuma suna gaya masu labarin gaibi,
watau abubuwan da za su faru gobe ko baɗi
da sauransu. Ire iren waɗannan
mutane da suke yin hulɗa da
aljannu ne Hausawa suke kira ‘yan bori. Dukkan wanda yake son zama ɗan
bori dole sai an yi masa girka. Ana yin girka don a shirya dukkan iskokin da
suke kan mutum don ya zauna lafiya da su. Ana kuma yin girka don yin magani ga
marar lafiya wanda iskoki suke kansa kuma suka hana shi zama lafiya.
Bayan
addinin gargajiya sai addinin Musulunci wanda shi addini ne Allah Maɗaukakin
Sarki Ya aiko ta hannun Annabi Muhammadu, tsira da amincin Allah su ƙara tabbata a gare shi, don
ya shiryar da al’ummar duniya zuwa ga hanya madaidaiciya a cikin shekara 610
Miladiyya. Addinin Musulunci ne ya biyo bayan addinin Kirista wanda Allah Maɗaukakin
Sarki ya aiko ta hannun Annabi Isa, Allah ya yarda da shi. A tsakanin waɗannan
addinai akwai shekaru ɗari
shida (Ibrahim,1982:63).
Ba
kamar sauran addinan da suka gabace shi ba, addinin Musulunci an aiko da shi ga
dukkan al’ummar duniya don ya zama hanyar shiriya ga kowa. Annabi Muhammadu,
tsira da amincin Allah su ƙara
tabbata a gare shi, ya fara da kiran ‘yan’uwansa Banu Ƙuraish don su karɓi
wannan addini.Wasu suka karɓa wasu
kuwa ba su karɓa ba. Sannu a hankali
yana wa’azi tare da sahabbansa cikin ɗan
ƙanƙanin lokaci, sai da dukkan ƙasashen Larabawa suka karɓi
addinin Musulunci. Wannan ne ya sa aka kafa ƙungiyar al’ummar Musulmi
wadda take da cibiya a Madina. Annabi shi ne shugaban wannan al’umma, kuma
dukkan wani abu da za ya zartar, sai ya yi shawara da sahabbansa.Wajen tafiyar
da wannan al’umma ba a nuna ƙabilanci
ko fifiko tsakanin jama’ar da suke cikinta. Abin da ta sa gaba shi ne haɗin
kai da son juna da nuna ‘yan’uwantaka a tsakanin Musulmi. Babban tsarin mulkin
wannan al’umma shi ne shari’ar addinin Musulunci. Kafin Annabi ya ƙaura, ya bar wa al’ummar
Musulmi Alƙur’ani
Maigirma da kuma Hadisai don su yi masu jagora dangane da addininsu (Ibrahim,
1982:63).
Manyan
shika-shikan addinin Musulunci biyar ne kamar haka:-
i)
Shedawa ba abin bautawa da
gaskiya sai Allah, kuma Annabi Muhammadu, tsira da amincin Allah su ƙara tabbata a gare shi,
BawanSa ne kuma ManzonSa ne.
ii)
Tsayar da Sallah.
iii)
Bayar da Zakka.
iɓ) Yin Azumin watan Ramalana.
ɓ) Ziyartar Ɗakin Allah don yin aikin
Hajji ga wanda
Allah
Ya ba iko.
Idan
muka waiwaya muka duba al’ummar Hausawa kafin shigowar addinin Musulunci da ma
bayan shigowar sa za a fahimci cewa, mutane ne musu matuƙar biyayya ga dokokin addinin
da suke bauta wa. Misali, al’ummar Hausawa a lokacin da suke bautar addinan
gargajiya suna matuƙar
yin biyayya ga abubuwan da suke bauta wa, suna tsoron su saɓa
musu don tsoron kar su yi fushin da zai sanya su saukar masu da wani bala’i.
Haka kuma, suna kyautata musu don neman yardarsu yadda za su biya musu
bukatunsa, su kuma sanar da su abubuwan da ke tafe a shekara mai zuwa, idan na
sharri ne su taimaka musu yadda za su yi maganinsu. Dangane da wannan takarda
za a ɗauki wani ɓangare
na rayuwar Hausawa domin ganin yadda addinin gargajiya ya ɗauke
shi don bayar da misali. Za a ɗauki
lalata (zina) watau saduwa tsakanin mace da namiji waɗanda
ba igiyar aure tsakaninsu don duba matsayinta da irin hukuncin da ake yanke wa
waɗanda suka aikata ta a
al’adar Hausawa kafin shigowar addinin Musulunci.
Duk
da kasancewar a al’adar Hausawa ba a yi wa budurwa aure sai ta kai shekara goma
sha takwas ko fiye da haka, watau an tabbatar da ta balaga, an yarda idan
saurayi yana neman aure budurwa ya je tsarince wurinta, watau ya kwana gidansu
a ɗaki ɗaya
da ita bisa shimfiɗa ɗaya,
ko ita ta je gidan saurayin nata su kwana tare, amma duk da haka al’ada ba ta
yarda ya ko taɓa jikinta ba, balle
ma har ya aikata wani abu da ita ba, watau ya yi lalata (zina) da ita ba. Idan
ya kuskura ya taɓa ta ko ya yi ƙoƙarin yin lalata da ita, to
ya shiga uku ya lalace, don kuwa duk wannan yanki nasu ba zai ƙara samun budurwar da za ta
yarda da shi ba. Wannan dalili ne zai kai shi ga rasa matar da zai aura, daga ƙarshe dole ya gudu ya bar ƙasar baki ɗayanta
yadda ba a za a sake jin labarinsa ba. Ire-iren waɗannan mutane ne za a tarar sun je wasu garuruwa inda ba
wanda ya san su a garin. A wasu lokuta har su mutu ba a sanin daga inda suka zo wannan ƙasa. Wannan hukunci ga namiji ke
nan.
Ita
budurwa kuwa idan ta kuskura ta yi lalata (zina) tana fuskantar hukunci mai
tsananin wanda a wani lokaci yana iya zama dalilin mutuwar ta. Wannan hukunci
ya danganta da abin bautar gidansu. Da farko abin da ake fara yi shi ne, za a
kira ta a tambaye ta, ko ta san ɗa
namiji? Idan ta amsa da cewa ta san ɗa
namiji, shi ke nan ta jawo wa kanta da dukkan zuri’arta abin kunya, sai kuma a
rage yawan dukiyar aurenta. Idan kuwa ta amsa da cewa ba ta san ɗa
namiji ba, sai aka iyayenta su bi hanyar da suka gada ta tsafi don gane
gaskiyar abin da ta faɗa.
Ga misalin ire-iren yadda ake gane budurwa ta san ɗa
namiji ko ba ta san shi ba kafin a yi mata aure a al’adar Maguzawa da kuma irin
hukunci da suke yanke wa ‘ya’yansu mata waɗanda
ba su kai budurcinsu ba dangane da abubuwan da suke bauta wa na gargajiya.
2.1.1 Masu Bautar Aljanin
Magiro
Maguzawan
da suke bautar wannan tsafi sun ɗauka
aljanin yana zaune a dutsin Kwatarkwashi. A Kwatarkwashi arnan Suna ne suke
bautar wannan gunki, haka kuma akwai wasu arnan a wasu sassan ƙasar Katsina da suke bautar
wannan tsafi. A ƙasar
Katsina a ƙauyen
Kunkunna da Makanwaci da Tamna da Maikada da Daulai cikin ƙaramar Hukumar Safana. Haka
kuma a ƙauyukan
Barza da Gerecen-Arna da Aidun Gadaje cikin ƙaramar Hukumar Ɗanmusa akwai arnan da suke yin irin wannan bauta ta tsafin
Magiro. Domin yin wannan bauta, suna samun bishiyar tsamiya ko marken da yake
da duhuwa da sarƙaƙƙiya. Waɗannan
arna na samun yashi mai laushi da kyawo su zuba a gindin wannan tsamiya ko
marke, sai kuma su kawo baƙin
zane da baƙin
rawani da baƙar
hula da baƙar
riga da baƙin
wando dukkansu na saƙi
sai a ɗaɗɗaura
su wurin wannan tsamiya. Daga nan, sai a sami tulunan giya biyu a ajiye gindin
wannan tsamiya ko marke, sai kuma a yanka baƙin bunsuru a gindin
tsamiyar. Dukkan wanda ya ga waɗannan
alamomi zai fahimci akwai wani abu da ke faruwa a wurin, kuma ana gargaɗin
mutane da su yi nesa da wurin don ba mai zuwa wurin sai wanda yake kula da
tsafin ko wani daga cikin zuri’arsa. Ana tsorata mutane da cewar, dukkan wanda
ya je wurin, idan ba waɗannan
mutane ba, dukkan abin da ya same shi ya kuka da kansa.
Mabiya
tsafin Magiro sun ɗauka
wannan aljani na kare su daga dukkan bala’o’i, kuma yana biya masu dukkan buƙatun da suka nema daga gare
shi. Haka kuma, suna ikirarin cewa, dukkan wanda yake da shakka kan gaskiyar
tsafinsu suna iya nuna masa ta hanyar kiran aljanin. Akwai dalilan da kan sa a
kira aljanin Magiro waɗanda
suka haɗa da idan ana biki
gidan mabiyansa, yana zuwa don ya bayyana wa jama’a da mahaifan wannan yarinya
da za a yi wa aure ba ta yi lalata (zina) ba a lokacin da take budurwa. Hanyar
da ake gane haka shi ne, a ranar da za a ɗaura
wa yarinyar aure, tun da asuba sai mahaifanta su kira ta, sai a ajiye turmin
daka a tsakiyar gidansu ta hau kansa ta zauna. A wannan lokaci ne za a kira
wannan aljani na Magiro. Da ya iso gidan, sai ya yi ta zagaya gidan kamar iskar
guguwa, ya kuma yi ta yin ruri kamar bajimin sa. Idan wannan yarinya ta taɓa
yin lalata, sai ya kashe ta. Idan kuwa ba ta taɓa
yi ba, sai ya yi ta zagaye-zagayensa har ya gama ba abin da zai sami wannan
yarinya. Ko kuma, idan ya rage saura kwana ɗaya
a yi bikin, sai a sami baƙin
ɗan’akuya
da jan zakara da goran giya a kai su wurin da ake yin tsafin Magiro. Idan gari
ya waye, sai a je wurin a duba. Idan an tarar ɗan’akuyan
da zakaran sun mutu, kuma goran giya babu kome cikinsa, alama ce wadda take
bayyana cewa wannan yarinya ba ta yi lalata ba, Magiro ya yi maraba da ita ke
nan. Idan kuwa aka tarar ɗan’akuyan
da zakaran, kuma ba a taɓa
goran giya ba, alama ce wadda take bayyana wannan yarinya ba ta kai budurcinta
ba, Magiro bai yi maraba da ita ba ke nan, sai ya kashe ta. Daga nan, sai
iyayenta su yi ta murna saboda ɗiyarsu
ta kai budurcinta. Daga nan, sai a ɗauki
wannan yarinya a kai ta ɗakin
mahaifiyarta inda za a yi sauran al’adun da suka dace a yi mata don kai ta
gidan miji (Ibrahim, 1982: 172).
Su
kuma Maguzuwa masu bautar tsafin Uwar-Gona a lokacin da ‘yarsu budurwa za ta yi
aure, hanyar da suke bi don su gane cewa wannan yarinya wadda za a yi wa aure
ta yi lalata ko ba ta yi lalata ba ita ce, sai a sa waɗanda
za su auri wannan yarinya su kawo ɗan’akuya.
Daga nan sai a samo turamen daka uku, a kuma samo mutane uku, sai a jera turame
biyu kusa da kusa, sai a sanya turmi na cikon ukun a gefen waɗannan
turame biyu. Daga nan, sai mutane biyu daga cikin mutanen nan uku su hau kan
turmi ɗaya - ɗaya,
shi kuma na cikon uku sai ya hau kan ɗaya
turmin. Sai a kawo wannan ɗan’akuya
a ba waɗannan mutane biyu waɗanda
suke kan turame biyu da suke kusa – kusa. Ɗaya ya riƙe ƙafafun gaba, shi kuma ɗayan
ya riƙe ƙafafun, shi kuma wanda yake
kan ɗayan turmi na cikon uku, sai
a kawo masa wani takobi na tsafi wanda aka ajiye ba a amfani da shi sai irin
wannan rana. Lokaci da ya amshi wannan takobi, sai ya sari wannan ɗan’akuya
da shi. Idan wannan yarinya ba ta san ɗa
namiji ba, sari ɗaya zai yi wa wannan ɗan’akuya
ya raba shu biyu, shi ke nan sai iyaye da abokan arziki su yi ta murna, ‘yarsu
ta kai budurcinta. Idan kuwa wannan yarinya ta san ɗa
namiji ko sara nawa ya yi wa wannan ɗan’akuya
ba zai yi masa ko ƙwarzane
ba balle ya raba shi biyu. Daga
nan, nan take wannan yarinya za ta faɗi ta mutu.
Maguzawan da suke bautar tsafin Kurmawa waɗanda ake samu a ƙasar Katsina da Kano da Zamfara, a lokacin da za su yi wa
ɗiyarsu budurwa aure,
idan an tambaye ta ce ba ta san ɗa namiji ba, sai a samo ɗan kwikwiyo da rago
a yanka su, a feɗe naman a kuma yayyanka su a haɗe su wuri ɗaya a soya. Bayan
ya naman ya soya, sai a kira wannan yarinya a ba ta naman ta ci. Idan ba ta san
ɗa namiji ba, duk lokacin
da za ta ɗauko tsokar naman ta ci, sai ta ɗauko ta ragon, za
ta ci har ta ƙoshi ba abin da zai same ta. Idan
kuwa ta san ɗa namiji ba za ta bambance naman kare da na ragon ba, sai
ta haɗa su ta yi ta ci har sai ta ƙoshi. Daga nan sai ta faɗi ta mutu nan take.
Idan kuwa a lokacin da aka tambaye ta, ko ta san ɗa namiji? Ta amsa
da cewa ta sani, sai a ba ta wannan kwikwiyo ta riƙa yawo da shi, don bayyana wa jama’a ba ta kai buturcinta
ba, sannan kuma a rage yawan dukiyar aurenta. Wannan dalili ne, ya sa Hausawa
yin karin maganar da ke cewa, ‘sharri kwikwiyo ne mai shi yake bi’.
Su kuwa Maguzawan da suke bautar tsafin Maƙera waɗanda su ma ana samun a ƙasar Katsina da Kano da Zamfara, a lokacin da za su yi wa
‘yarsu budurwa aure, idan ya rage saura kwana ɗaya a ɗaura mata aure, sai
a kira ta a tambaye ta ko ta san ɗa namiji? Idan
ta amsa da cewa ba ta san ɗa namiji ba, sai a samo jan zakara. Daga nan, sai a ɗebo jar dawa a
sami mata uku ko huɗu, sai a kamo wannan zakara a sanya shi ƙarƙashin turmin da ake daka, a zuba wannan jar dawa cikin
wannan turmi, sai waɗannan mata su yi ta dakan wannan dawa har sai sun
mayar da ita gari. Lokacin da suke dakan wannan dawa wannan zakara na ƙarƙashin turmin da suke dakan. Idan wannan yarinya ba ta
san ɗa namiji ba, duk
tsawon lokacin da aka ɗauka ana dakan wannan dawa ba abin da zai sami
zakaran, hasali ma, washegari ranar da za a ɗaura auren wannan yarinya, zakaran ne zai fara cara da
asuba don tayar da mutanen wannan gida daga barci. Idan kuwa wannan yarinya ta
san ɗa namiji, da
safe idan aka ɗaga turmin da aka sanya zakaran za a tarar ya
rududduge ya saje da ƙasa, ana ganin haka, ita kuma wannan yarinya tana faɗuwa nan take ta
mutu (Ibrahim, 1982: 173 - 175) .
Kamar
yadda aka gani ta wannan hanya ce al’ummar Hausawa kafin su karɓi
addinin Musulunci suke hukunta waɗanda
suke aikata lalata (zina), wannan ne ya sa
a wancan zamani suka zauna lafiya ba yawan zinace-zanace aka kuma sami sauƙin tafiyar da shugabancin al’umma ba tare da fuskantar
wasu matsaloli ba. Yanzu kuma, za mu duba irin
hukuncin da addinin Musulunci ya yi umurnin a yanke wa waɗanda
suka aikata wannan mummunan aiki. Da farko za mu duba cikin Alƙur’ani Maigirma, cikin sura
ta 17 Aya ta 32, inda Allah, Maigirma da ɗaukaka
Yake cewa:
“Kuma kada ku kusanci zina.
Lalle ne ita ta kasance alfasha ce kuma ta munana ga zama hanya” (Gumi, 1979:
419).
Allah, Maigirma da Ɗaukaka, a cikin Sura ta 24
Aya ta 2 da ta 3, Ya ƙara
da cewa:
“Mazinaciya da mazinaci1,
to, ku yi bulala ga kowane ɗaya
daga gare su, bulala ɗari.
Kuma kada tausayi ya kama ku game da su a cikin addinin Allah, idan kun kasance
kuna yin imani da Allah da Ranar Lahira. Kuma wani yankin jama’a daga muminai,
su halarci azabarsu” (Gumi, 1979: 528).
“Mazinaci ba ya aure2
face da mazinaciya ko mushirika, kuma mazinaciya babu mai aurenta face mazinaci
ko mushiriki. Kuma an haramta wannan a kan muminai” (Gumi, 1979: 528).
A cikin Sura ta 25 Aya ta 60
– 70, Allah, Maigirma da Ɗaukaka,
Ya ƙara
da cewa:
“Kuma waɗanda
ba su kiran wani ubangiji tare da Allah, kuma ba su kashe rai wanda Allah Ya
haramta face da hakki, kuma ba su yin zina. Kuma wanda ya aikata wancan, zai
gamu da laifuffuka” (Gumi, 1979: 551).
“A riɓanya
masa azaba a Ranar Ƙiyama.
Kuma ya tabbata a cikinta yana wulakantacce” (Gumi, 1979: 528).
![]() |
- Hukuncin waɗanda ba
su yi aure ba ne, amma waɗanda suka yi
aure, hukuncinsu a jefe su har su mutu, bayan sharuɗɗa sun
cika, kamar yadda yake ga sunna. Kuma wannan ga hakkin ‘ya’ya ne, amma
bayi, hukuncinsu bulala hamsin kawai.
- Auren mazinaci ko mazinaciya makaruhi ne
ga wanda ba haka nan yake ba, domin tsaron mutunci da kore tuhuma.
Sai wanda ya tuba3, kuma ya yi
imani, kuma ya aikata aiki na ƙwarai,
to, waɗancan Allah Yana musanya
miyagun ayyukansu da masu kyau. Allah Ya kasance Mai gafara Mai jin ƙai” (Gumi, 1979: 528).
Mun ga irin hukunce-hukuncen
da Allah, Maigirma da Ɗaukaka
Ya yanke wa mazinata a cikin Alƙur’ani
Maigirma, yanzu kuma za mu duba Hadisan Annabi, tsira da amincin Allah su ƙara tabbata a gare shi, don
samun ƙarin
bayani.
A wani Hadisi da Bukhari ya
ruwaito, ya bayyana cewa Manzon Allah, tsira da amincin Allah su ƙara tabbata a gare shi, ya
ce:
“Mazinaci ba zai
kasance mai imani ba a lokacin da yake aikata zina……” (Emarah, 1430 AH/2009:
63).
A
wani Hadisi da aka karɓo
daga Ubaidah ɗan Samit ya ce:
Manzon Allah, tsira da amincin Allah su ƙara
tabbata a gare shi, ya ce:
“Ku riƙa
daga gareni! Ku riƙa daga gare ni! Haƙiƙa
Allah Ya sanya mafita a gare su: Saurayi da budurwa (idan suka yi zina) to,
bulala ɗari ne da
korewar shekara; kuma bazawari da bazawara bulala ɗari ne da
rajamu” (Kani, Ba Ranar Bugu:212).
Wani
Hadisin da aka karɓo
daga Ɗan
Umar, ya bayyana cewa, Manzon Allah, tsira da amincin Allah su ƙara tabbata a gare shi, ya
ce:
“Ku nisanci waɗannan
(ayyuka) munana wacce Allah Maɗaukaki Ya yi hani gare ta. Kuma wanda
ya aikata ta, to, ya suturu da suturcewar Allah Maɗaukaki; kuma
ya tuba ga Allah Maɗaukaki. Saboda, lallai wanda ya bayyanar da
haƙiƙanin
lamarinsa a gare mu za mu tsayar da hukuncin Allah Maɗaukaki a gare
shi” (Kani, Ba Ranar Bugu:215).
2.2 Biyayya ga Tsarin Shugabanci Irin na Hausawa
Shugabanci
yana nufin yi wa al’umma jagora a halin zamantakewarsu na yau da kullum. A nan
duk wanda aka ba ragamar tafiyar da mulkin al’umma, nauyi ya hau kansa na tsare
lafiyarsu da dukiyarsu da mutuncinsu. Su kuma waɗanda
ake shugabanta haƙƙinsu
ne su ba wanda yake shugabancinsu haɗin
kai, da bin ummurnin sa ta hanyar bin doka da oda, da yi masa biyayya don ya
sami sauƙin
tafiyar da mulkinsu cikin kwanciyar hankali.
- Wanda ya tuba
daga kowane irin zunubi, waɗanda aka ambata
da waɗanda ba
a ambata ba, ko da laifinsa kafirci ne, to, sai ya tuba zuwa ga Allah
kawai, tuba ta gaskiya, lalle ne Allah zai karɓi
tubarsa matuƙar ajalin mutuwa bai sauka a kansa ba.
A ƙasar Hausa shugabanci yana
farawa daga gida, a kowane gida wanda yake ƙunshe da mutanen da suka kai
biyu ko waɗanda suka wuce haka,
akwai maigida wanda nauyin dukkan mutanen wannan gida yana kansa. Shi ne yake
shugabancin harkokin rayuwar yau da kullum na mutanen da suke wannan gida. A
saboda haka dukkan mutanen wannan gida waɗanda
suka haɗa da matansa da
‘ya’yansa da ƙannensa
da jikokinsa da barorinsa duk da matansu da ‘yan cin arziki suna bin
ummurninsa. Haka kuma, shi ne yake ɗaukar
nauyin yi masu dukkan abubuwan da suka shafi sutura da abinci da tsaro da kare
mutuncinsu. Idan ire-iren waɗannan
gidaje suka yi yawa, sai su kafa unguwa. Daga cikin masu waɗannan
gidaje, sai a sami wani mai kwarjini da iya tafiyar da harkokin al’ummarsa a ba
shi muƙamin
mai’unguwa. Mutanen wannan unguwa ne suke zaɓar
sa su kai shi ga dagacinsu wanda shi ne zai amince da shi. Daga nan nauyin
tafiyar da harkokin mulkin al’ummar wannan unguwa ya hau kansa. Shi ne kuma zai
riƙa
wakiltarsu a duk wasu harkoki da kuma yin sasanci a tsakanin talakawan wannan
unguwa. Haka kuma, shi zai riƙa
tattara kuɗin harajin mutanen
wannan unguwa don kai wa dagacinsu (Usman, 1972:176).
Samuwar
unguwanni da yawa ke sa a sami dagaci wanda shi yake shugabantar masu
unguwanni. Dukkan abubuwan da ke faruwa a waɗannan
unguwanni sai an sanar da shi. Haka kuma, duk wani sasanci da ya gagari
mai’unguwa, sai ya kai wa dagaci don ya sasanta. Dagaci ne yake wakiltar
al’ummominsa waɗanda suke zaune a
unguwanni a wasu al’amuran da suka shafi waɗannan
unguwanni, kuma shi masu unguwanni suke kai wa kuɗin
harajin unguwanninsu don ya kai wa hakimi.
Garuruwan
dagatai da yawa suke samar da ƙasar
hakimi wanda shi yake shugabancin dukkan garuruwan dagatai da suke ƙarƙashinsa. Dukkan abubuwan da
ke faruwa a garuruwan dagatai sai an sanar da hakimi, kuma shi yake wakiltarsu
a wasu ma’amalolin da suka shafi wannan ƙasa
tasu. Idan dagatai sun gaza wajen yin sasanci a tsakanin talakawansu, sai su miƙa maganar ga hakimi wanda
zai yi iyakar ƙoƙarinsa ya yi sasanci. Bayan
dagatai sun kammala tattara kuɗin
harajin ƙasashensu,
sai su kawo wa hakimi daga nan sai ya kai wa sarki.Waɗannan
ƙasashe na hakimai su ne suke
taruwa su kafa ƙasar
sarki wanda shi ne wuƙa
da nama a duk harkokin da ke faruwa a wannan masarauta. Dukkan mutanen da suke
zaune a wannan ƙasa
na ƙarƙashin ikonsa, kuma hakimai
na sanar da shi dukkan abubuwan da ke faruwa a ƙasashensu. Idan hakimai sun
gaza wajen yin sasanci tsakanin talakawansu, sai su kai maganar ga sarki, wanda
ta hanyar shawartar ‘yan majalisarsa zai yanke hukunci na ƙarshe ko da daɗi
ko ba daɗi.Wanda hukuncin bai
yi wa daɗi ba, dole ya yi haƙuri (wannan dalilin ne ya sa
ake yi wa sarakunan gargajiya na ƙasar
Hausa laƙabi
da sunan wuƙar-yanka).
Idan hakimai suka kammala tattara kuɗin
haraji na ƙasashensu,
sai su kai wa sarki, wanda zai sa a saka su cikin Baitulmali don gudanar da
harkokin mulki na wannan masarauta (Usman, 1972:176).
A
kowace masarauta akwai ‘yan majalisar wannan sarki, su ne suke taimaka wa
wannan sarki da shawarwarin aiwatar da mulkin wannan ƙasa cikin nasara da adalci.
Waɗannan ‘yan majalisa sun haɗa
da waziri wanda shi ne babban mai taimaka wa sarki, kuma a mafi yawancin lokaci
shi yake wakiltarsa a lokacin da ya yi wata tafiya wajen masarautarsa. Bayansa,
akwai alƙali
da magatakarda da ma’aji ko ajiya da sarkin fada da shamaki da shantali da
galadima da sarkin gida da sauransu da dama.
Bayan
waɗannan sarautu, akwai waɗanda
ake ba masu yin sana’o’in gargajiya. Kowace sana’a tana da wanda ake ba
jagorancin masu yin wannan don ya yi jagoranci da sasanci a tsakanin masu yin
wannan sana’a da kuma tafiyar da sana’ar bisa ingantaccen tsari. Ire-iren waɗannan
sarautu sun haɗa da sarkin noma ga
manoma da sarkin maƙera
ga maƙera
da sarkin aska ga wanzamai da sarkin makaɗa
ga makaɗa da sanƙira ko sarkin roƙo ga maroƙa da sarkin fawa ga mafauta
da sauransu da dama (Adamu,1978:5).
Dukkan
waɗannan sarautu da aka yi
bayani a kansu tun daga mai unguwa zuwa ga sarki da ‘yan majalisarsa da masu riƙe da sarautun sana’o’in
gargajiya, an tsara su ne bisa tafarkin gado.Watau idan wanda yake riƙe da sarauta ya rasu ko aka
tuɓe shi, a mafi yawancin
lokaci ana zaɓar wani daga cikin
‘ya’yansa ko ɗan’uwansa don ya gaje
shi.
Babban
ginshiƙin
tafiyar da kowane irin mulki shi ne adalci, watau shugaba ya zama adali wajen
tafiyar da mulkinsa ba tare da nuna bambanci ba, ya kuma ba kowa haƙƙinsa ba tare da la’akari da
nasabarsa, ko muƙaminsa
ba. Dukkan ƙasar
da take da shugabanni masu yin adalci ga talakawansu, wannan ƙasa za ta zauna lafiya ta
kuma sami ci gaba da ƙaruwar
arziki. Idan muka waiwayi yadda aka riƙa
gudanar da mulki a ƙasar
Hausa kafin zuwan wannan zamani za a ga cewa, ana gudanar da shi ne bisa
adalci, don kuwa akwai zaman lafiya tsakanin al’ummomin wannan ƙasa. Misali, a cikin gida ko
unguwa ko cikin gari, manya suna iya yin hukunci idan suka ga na ƙasa na yin rashin daidai ko
da kuwa ba su da wata dangantaka ko nasaba ta jini. A tunaninsu yaro duka na
kowa ne, matuƙar
ka ga yana yin wani abu na rashin daidai matuƙar ba ka tsawata masa ba,
to, a al’adar zamantakewa ta Hausawa ba a yi daidai ba, kuma ba za a ɗauki
wannan mutum wanda ya san daidai ba. A wancan zamani takan kai matakin idan
babban mutum ya tarar ana yin rashin daidai yana iya yin hukunci mai tsanani4
(ko da kuwa zai kai matsayin duka) ga waɗanda
ya tarar suna yin rashin daidai ɗin
ko ya san su, ko bai san su, ko da dangantaka ko ba dangantaka tsakaninsu.
Domin
cim ma wannan buri ne ya sa addinin Musulunci ya shimfiɗa
yadda za a gudanar da mulkin adalci ga kowace al’umma yadda za a zauna lafiya,
kuma wannan al’umma ta sami dauwammen ci gaba da zama lafiya. Dangane da haka,
ga irin yadda addinin Musulunci ya tsara gudanar da mulkin adalci kamar yadda
Sarkin Musulmi Muhammadu Bello ya rubuta maƙala mai taken Usul al-Siyasa ya ba Malam Umaru Dallaji
wanda aka ba tutar jihadi a ƙasar
Katsina. Domin fito da wannan tsari na shugabanci ga kaɗan
daga cikin bayanan wannan maƙala:
\
![]() |
4. Wani dattijo ya tarar da wata mata ta yiwo
yaji mutane sun taru ana ta ba ta haƙuri don ta
koma ta ƙi komawa, da ya ce ta koma ta ƙi,
sai ya ɗebo tsabgar
bedi, ya yi ta dukan ta da ita, ya tasa ta gaba sai da ya mayar da ita gidan
mijinta. Da mahaifanta suka ji labari, sai suka tarar da wannan dattijo har
gida suka yi masa godiya bisa ga wannan taimako da ya yi masu. Ita kuma wannan
mata daga wannan rana ba ta ƙara yin yaji
ba.Wannan al’amari ya bayyana irin muhimmancin shugabanci da yadda ake girmamma
na gaba, ba kamar wannan zamani ba wanda ake son ‘ya’ya, har ta kai matakin
iyaye ba sa iya hukunta ‘ya’yansu.
Ya
fara da ambaton Umarun Dallaji a matsayin mutum mai gaskiya da riƙon amana da yin ayyuka domin
neman sakamako daga Allah. Daga nan, sai ya yi masa addu’a yana roƙon Allah Ya taimake shi bisa
ga gudanar da mulkinsa, Ya ba shi tsawon kwana bisa ga wannan mulki da yake yi,
sannan kuma ya ƙara
da roƙon
Allah Ya ƙara
nunnuka yawan masu goyon bayansa. Daga nan sai wannan maƙala ta fara da cewa:
“Ka sani ya kai ɗan’uwa,
babbar ƙaddarar
da za ta faɗa a kan bawan Allah,
ita ce, a ba shi shugabancin jama’a, domin kuwa ka sani, za a tambayi kowane
mutum abin da bakinsa ya faɗa,
ayyukan da ya yi, da abubuwan da suka biyo bayansu. Idan ya kasance shi shugaba
ne, za a ƙara
da tambayar sa yadda ya gudanar da mulkinsa tsakaninsa da talakawansa. Idan ya
kasance ba ya iya sauke nauyin kansa, to, ta yaya zai iya sauke nauyin jama’ar
da take ƙarƙashinsa? Dangane da haka ne
wasu suke cewa, dukkan wanda Allah bai ɗora
masa wani nauyi na shugabanci ba ya ƙara
yi maSa godiya, don Ya sauke masa nauyin da za a tambaye shi yadda ya gudanar
da shi. Saboda haka, Allah Ya cece shi daga fitunun duniya, don kuwa babu kome
cikinta sai tashin hankali da azabtarwa a gobe lahira”.
Saboda matsalolin da suke
tattare da shugabanci ne, ya kawo wani hadisin Annabi, inda yake cewa:
Manzon Allah, tsira
da amincin Allah su ƙara
tabbata a gare shi, ya tambayi sahabbansa, “ko kuna son in gaya maku wani abu
dangane da shuganaci”? Sai suka amsa masa da cewa: “Ya Manzon Allah muna so”.
Daga nan sai ya ce: “Farkon shi akwai kushewa, tsakiyarsa, akwai nadama. Ƙarshensa kuma, akwai azaba a
ranar lahira”.
A
wannan maƙala
Sarkin Musulmi Muhammadu Bello, ya ci gaba da bayanin cewa:
“Wanda Allah,
Maigirma da Ɗaukaka,
Ya ba shi shugabanci, to, ya yi iya ƙoƙarinsa don ganin ya sauke
dukkan nauyin da yake a kansa, ta hanyar ba dukkan al’ummomin da suke ƙarƙashinsa haƙƙoƙinsu”.
Ya ƙara da bayyana cewa, duk da
yake shugabanci abu ne mai nauyi da wuyar ɗauka,
amma duk da haka nan, kyauta ce babba. Dukkan shugaban da ya yi wa Allah
godiya, ya kuma sami nasarar sauke nauyin shugabanci, to, zai sami babban rabo
wanda ba a iya misalta shi. Haka kuma, dukkan shugaban da bai yi wa Allah
godiya ba, ya kasa sauke nauyin shuganci, zai fuskanci matsananciyar uƙuba wadda ba ta misaltuwa.
A
dai wannan maƙala
Sarkin Musulmi Muhammadu Bello, ya kawo hadisai masu yawan gaske waɗanda
suka bayyana matsayi da hukuncin da ke kan shuganni masu adalci da marasa
adalci kamar haka:
Manzon Allah, tsira
da amincin Allah su ƙara
tabbata a gare shi, ya ce: “A ranar Lahira, babu wata inuwa ko wurin hutawa,
sai inuwar Allah. A wannan rana mutane bakwai ne kawai za su sami wannan inuwa;
shugaba adali wanda ya gudanar da mulkinsa kamar yadda shari’a ta shinmfiɗa,
sai saurayi wanda ya girma yana bautar Allah, sai ɗan
kasuwa wanda a lokacin da yake gudanar da kasuwancinsa hankalinsa yana masallaci,
mutane biyu waɗanda suke ƙaunar junansu saboda bautar
Allah da suke yi, sai kuma mutumin da a duk lokacin da ya kaɗaita
yana bautar Allah, idan ya tuna Allah, sai ya yi ta zubar da hawaye, sai kuma
mutumin da wata mata kyakkyawa wadda yake so, ta kaɗaice
da shi, ta kuma bukace shi da ya yi lalata (zina) da ita, amma sai ya ƙi amincewa, ya bayyana mata,
‘ina tsoron fushin Allah Maigirma da ɗaukaka’,
sai kuma mutumin da ya ba da sadaka don Allah, ba don riya ba, har ta kai
lokacin da zai bayar da sadakar hannunsa na hagu bai san abin da hannunsa na
dama ya yi ba”.
Manzon Allah, tsira
da amincin Allah su ƙara
tabbata a gare shi, ya ce: “Wanda Allah Ya fi so, kuma wanda yake kusa da
Allah, shi ne shugaba adali, wanda Allah ba Ya so, kuma wanda yake nesa da
rahamar Allah, shi ne azzalumin shugaba”.
Manzon Allah, tsira
da amincin Allah su ƙara
tabbata a gare shi, ya ce: “Na rantse da wannan wanda rayuwata take a hannunsa,
cewa, ayyukan alherin shugaba adali ana tattara su a Aljanna daidai da ayyukan
alherin da dukkan talakawansa suka aikata. Haka kuma, idan aka ba da lada ɗaya
ga ibadar da talakawansa suka yi, shi ana ba shi lada 70, 000 sakamakon dukkan
ibadar aiki ɗaya da ya yi
kwatankwacin wadda talakawansa suka yi.
An karɓo
daga Abdullahi ɗan Abbas, Allah Ya
yarda da su, ya ce: “Wata rana Manzon Allah, tsira da amincin Allah su ƙara tabbata a gare shi, ya
zo ya tsaya a bakin ƙofar
Ka’aba, daga cikin Ka’aba kuma ‘yan ƙabilar
Ƙuraish masu yawa, sai ya ce
masu, ‘Ya ku shugabanin Ƙuraysh,
ku yi abubuwa uku ga waɗanda
kuke shugabanta; idan sun bukaci adalci, ku yi musu; idan sun bukaci sasanci,
ku sasanta su kamar yadda shari’a ta shimfiɗa
a yi; idan kuma kuka yi musu alƙawari,
to ku cika alƙawarinku
kada ku saɓa. Ya Allah, Kai da
Mala’ikunka ku la’anci wanda ya kauce wa wannan tsari. Allah Maigirma da ɗaukaka
ba ya amsar ayyukan farilla da na nafila na dukkan mutumin da ya kauce wa
wannan tsari”.
Idan
muka nazarci waɗannan bayanai da aka
tsakuro daga wannan maƙala,
za a fahimci cewa, shugabanci a addinin Musulunci al’amari ne mai matuƙar muhimmanci, wanda idan
aka tafiyar da shi kamar yadda shari’a ta shimfiɗa
al’umma za ta zauna lafiya a kuma sami ƙaruwar
arziki da fahimtar juna. Babbar hanyar da za a sami wannan biyan bukata ita ce,
shugabanni su zama masu adalci ga waɗanda
suke shugabanta.
2.3 Bin Gaskiya da Riƙon Amana
Gaskiya
na nufin yin dukkan wani abu wanda zai bayyana zahirin yadda wannan abu yake,
watau ba ragi ba ƙari. Riƙon amana kuma
na nufin adana wani abu na dukiya ko sirri wanda a lokacin da bukatar shi ta
taso a bayar da shi kamar yadda aka bayar. Idan kuma wani sirri ne ba za a
sanar da kowa ba, daga kai sai wanda ya sanar da kai. Kafin zuwan wannan zamani
an san Hausawa da bin gaskiya da riƙon amana ga
dukkan al’amuransu na rayuwa. Wannan dalili ne ya sa a wancan zamani kafin
shigowar addinin Musulunci al’ummar Maguzawa ba sa faɗin ƙarya
komin tsanani5 ko daɗi. Haka kuma, al’ummar Hausawa mutane
ne masu riƙon amana. Abin nufi a nan shi ne, a wancan
zamani duk irin halin matsi da tsananin da aka shiga idan ka kawo wani abu
wanda ya shafi dukiya ko kuɗi ka ba Bahaushe ajiya ko ka ba shi saƙo
ya kai wa wani, duk irin halin da yake ciki ba za ya yi amfani da wannan dukiya
ba har sai lokacin da ka bukata ya ɗauko maka. Haka kuma, idan saƙo
ne ka ba shi ya kai wa wani zai kai masa kamar yadda ka ba shi ba tare da ya
rage wani abu ba6. Idan kuma ka sanar da shi wani sirri ba za ya
gaya wa kowa ba daga kai sai shi. Wannan al’amari ya taimaka matuƙa
gaya wajen zaman Hausawa lafiya a wancan zamani. Saboda irin yadda Hausawa suka
yarda da bin gaskiya har karin magana suke da su masu yawa waɗanda suke
nuna muhimmanci gaskiya kamar haka:
v
Komi za ka faɗi faɗi gaskiya
kome taka ja maka ta biya.
v
Marar gaskiya ko cikin ruwa yake ya yi
jiɓi.
v
Gaskiya dokin ƙarfe.
![]() |
5. A al’adar
Maguzawa faɗin ƙarya
mummunan aiki ne wanda yake sa abin da suke bauta wa ya yanke wa maƙaryaci
mummunan hukunci. Wannan dalili ne ya sa idan Bamaguje ba ya lafiya, a lokacin
da rashin lafiyar ya tsananta, idan aka tambaye shi, ya ya jiki? Sai ya amsa da
cewa, babu sauƙi. Dalilin su a nan shi ne, kar su yi ƙarya
su faɗi abin da ba
haka yake ba. Shigowar addinin Musulunci ƙasar Hausa ne
ya yi horo da cewa, a duk yanayin da mutum yake ciki na rashin lafiya kar ya ce
ba sauƙi, don sauƙi daga Allah
yake.
6. Saboda gaskiya da riƙon amana na
Hausawa a wancan zamani ya sa a cikin shekara ta 1975 lokacin ina makarantar
Sakandare ta Daura, mahaifina ya je Mai’aduwa, lokacin da zai koma gida, da ya
zo bakin ƙofar makaranta, sai ya ga wasu ɗalibai ya
kira su, ya tambaye su, ko kun san wani yaro mai suna Bishir Ali Safana ?
Suka amsa masa da cewa, mun san shi abokinmu ne. Daga nan sai ya kawo kuɗi ya ba su ya
ce su kai min. Ina zaune cikin ɗakinmu, sai na ji waɗannan ɗalibai sun
shigo suna kiran sunana. Lokacin da na zo wurinsu, sai suka kawo waɗannan kuɗi suka ba ni
suka ce, babanka ne ya gamu da mu a bakin ƙofa ya ce mu
kawo maka. Wannan al’amari ya faru ne saboda irin tarbiyyar bin gaskiya da riƙon
amana wadda iyaye da magabata na wancan zamani suka ba ‘ya’yansu da
mabiyansu.
v
Ciki da gaskiya wuƙa
ba ta huda shi.
v
Gaskiya nagartar namiji.
v
A daɗe ana yi sai gaskiya.
v
Gaskiya akurkin ɗunɗu mai wuyar
saka hannu.
Haka
al’amarin yake a addinin Musulunci, domin kuwa akwai ayoyin Alƙur’ani
Maigirma da Hadisan Annabi Muhammadu, tsira da amincin Allah su ƙara
tabbata a gare shi, waɗanda suka bayyana muhimmanci gaskiya ga
dukkan Musulmi. Yin biyayya gare su zai sa mutum ya zauna lafiya a wannan
duniya, sannan kuma ya sami sakamako da Aljanna ranar lahira, rashin yin
biyayya gare su kuma zai sa mutum ya rasa zama lafiya a wannan duniya, sannan
kuma ya sami sakamako da wuta a ranar gobe lahira. Misali, a cikin Alƙur’ani
Maigirma,Sura ta 3, Aya ta 60, Allah Maigirma da Ɗaukaka na cewa:
“Gaskiya daga Ubangijinka take, saboda haka
kada ka kasance daga masu shakka” (Gumi, 1979:84).
Haka
kuma, a cikin Sura ta 4 Aya ta 135 Allah Maigirma da ɗaukaka na
cewa:
“Ya ku waɗanda suka yi
imani!Ku kasance masu tsayuwa da adalci, masu shaida saboda Allah, kuma ko da a
kanku ne ko kuwa mahaifa da mafi kusantar zumunta, ko (wanda ake yi wa shaida
ko a kansa) ya kasance mawadaci ko matalauci, to, Allah ne Mafi cancanta da
al’amarinsu, saboda haka kada ku bibiyi son zuciya, har ku karkata. Kuma idan
kuka karkatar da magana, ko kuwa kuka kau da kai, to, lallai ne, Allah Ya
kasance Masani ga abin kuke aikatawa” (Gumi, 1979:146)
Allah Maigirma da Ɗaukaka
a cikin Sura ta 33 Aya 35 yana cewa:
“Lallai, Musulmi maza
da Musulmi mata da muminai maza da muminai mata, da masu tawali’u maza da masu
tawali’u mata, da masu gaskiya maza da masu gaskiya mata, da masu haƙuri
maza da masu haƙuri mata, da masu tsoron Allah maza da masu
tsoron Allah mata, da masu sadaka maza da masu sadaka mata, da masu azumi maza
da masu azumi mata, da masu tsare farjojinsu maza da masu tsare farjojinsu
mata, da masu ambaton Allah da yawa maza da masu ambatonSa da yawa mata, Allah
Ya yi musu tattalin wata gafara da wani sakamako mai girma” (Gumi, 1979:639).
Idan muka nazarci waɗannan Ayoyi
na Alƙur’ani Maigirma za mu fahimci Allah Maigirma
da ɗaukaka na
bayyana muhimmanci gaskiya da kuma irin sakamakon da dukkan wanda ya tsare ta
zai samu a nan duniya da gobe lahira.
Saboda muhimmancin
gaskiya ga kowace al’umma ya sa addinin Musulunci ya ƙara fito da
ita sosai don ta ƙara zama jagora ga al’umma, dangane da haka,
an sami ingantattun bayanai daga Hadisan Annabi Muhammadu, tsira da aminci
Allah su ƙara tabbata a gare shi, waɗanda suka ƙara
bayyana matsayinta da muhimmancinta ga dukkan al’ummar da take son zama lafiya
da ci gaba. Ga misalin wasu Hadisai da aka samu waɗanda suka
bayyana muhimmancin gaskiya.
An karɓo daga
Abdullah, Allah Ya yarda da shi, ya ce: “Na ji Manzon Allah, tsira da aminci
Allah su ƙara tabbata a gare shi, na cewa, gaskiya na
kai mutum ga shiriya, ita kuma shiriya tana kai mutum Aljanna. Dukkan mutumen
da ya zama aikinsa faɗar gaskiya har ta zama al’ada a gare shi, to
ya zama cikakken mai gaskiya. Faɗar ƙarya na sa a
yi zalunci, haka shi kuma zalunci na kai mutum wuta. Idan mutum ya zama
al’adarsa faɗar ƙarya,
to Allah Maigirma da Ɗaukaka, na sanya shi
cikin maƙaryata”, (Ma’arouf, 1423 AH/2003: 128, da
kuma Khan, 1417 AH/1996: 961-962).
A wani Hadisi da aka
karɓo daga Ɗan
Abbas, Allah Ya yarda shi, ya ce:
“Na ji Manzon Allah,
tsira da aminci Allah su ƙara tabbata a
gare shi, na cewa: Dukkan mutumen da yake da waɗannan siffofi
guda huɗu ya sami ɗaukaka, waɗannan siffofi
su ne: Ya zama mai gaskiya da riƙon amana, da
alkunya, da hali na kirki ko hali na gari, da kuma ɗaukar girma”,
(Ma’arouf, 1423 AH/2003: 129).
Wani Hadisin
da aka karɓo daga
Muhammad ɗan Ali
Al-Kinani ya ce:
“Manzon Allah, tsira
da aminci Allah su ƙara tabbata a gare
shi, ya ce: An gina addinin Musulunci bisa shika-shikai uku kamar haka: Shiriya
da gaskiya, da kuma adalci. Shiriya farilla ce a furucinmu, gaskiya farilla ce
a hujjojinmu, adalci farilla ne a cikin zukatanmu” (Ma’arouf, 1423 AH/2003:
129).
2.4 Sadar da Zumunci da Taimakon Juna
Sadar
da zumunci al’amari ne wanda al’ummar Hausawa suke ba matuƙar
muhimmanci, don kuwa lokaci bayan lokaci ‘yan’uwa da abokan arziki kan riƙa
ziyartar juna don gaisawa da ganin halin da suke ciki. Kafin su tafi ziyartar
‘yan’uwa da abokan arziki sukan riƙa wani abu su
kai masu, ana yin haka gwargwadon ƙarfin arzikin
mutum. Wasu kuma, saboda rashin abin da za su kai ba za ya hana su yin zumuncin
ba, suna zuwa wurin ‘yan’uwansu domin su ga halin da suke ciki ba dole sai sun
kai masu wani abu ba.
Domin
tafiyar da rayuwarsu ta yau da kullum cikin sauƙi, al’ummar
Hausawa suna bin tafarkin rayuwa ta cuɗan-in-cuɗe-ka, watau
taimakon-kai-da-kai. Ta wannan fuska, idan abin arziki ya sami ɗan’uwa, ko
abokin arziki, ko wanda ake zaune tare da shi a wannan ƙauye ko
unguwa ko gari, misali aure ko haihuwa, sai duk a taru don taya shi murna. A
lokacin bikin, za a yi ta kawo masa gudummuwa wadda wasu kan kawo hatsi ko
abinci ko kuɗi ko sutura
da sauransu don dai a taimaka wa wannan ɗan’uwa, ko abokin
arziki gudanar da wannan hidima ba tare da ya wahala ba. Irin wannan halayya ce
a wannan zamani ta haifar da ƙungiyoyin
taimaron-kai-da-kai da kuma ƙungiyoyin ajo
domin taimaka wa juna.
Haka
kuma idan abin baƙin-ciki ya sami wani mutum, misali rashin
lafiya, ko mutuwa, ko wata masifa, ‘yan’uwa da abokan arziki da waɗanda ake
zaune tare da su, na kusa da na nesa suna ziyartar sa domin yi masa jaje da
taya shi jimamin wannan hali da ya shiga na rashin lafiya ko masifa ko rashin ɗan’uwa.
Bayan
wannan al’ummar Hausawa na tafiyar da ayyukan gayya don taimakon-kai-da-kai.Ana
yin ayyukan gayya wajen yin sababbin ɗakuna da gyara
tsofaffi da yin darnin gida da na garka a gonaki da ɗorin ɗan bisan ɗaki da na
rumbu. Haka kuma ana yin ayyukan gayya a gonaki don yin sassabe da huɗa da shuka da
noma da girbi da ɗaurin amfanin
gona da kuma kawo shi gida. A cikin ƙauyuka da
garuruwa ana yin ayyukan gayya don gyaran masallatai da maƙabartu da
magudanun ruwa da mashayar ruwa ta mutane da ta dabbobi da kuma gyaran hanyoyin
da ake bi don kai amfanin gona gida da kasuwanni (Sallau, 2010: 5-6).
Shigowar
addinin Musulunci ƙasar Hausa ya ƙara
jaddada waɗannan ayyuka
na alheri, watau sadar da zumunci da taimakon kai-da-kai, don kuwa a cikin Alƙur’ani
Maigirma, Sura ta 2, Aya ta 27, Allah Maigirma da Ɗaukaka, na
cewa:
“Waɗanda suke
warware alkawalin Allah daga baya ƙulla shi,
kuma su yanke abin da Allah Ya yi umurni da shi a sadar, kuma suna ɓarna a cikin ƙasa,
waɗannan su ne
masu hasara” (Gumi, 1979: 9).
A
wata faɗar cikin Alƙur’ani
Maigirma, Sura ta 13, Aya ta 21, Allah Maigirma da Ɗaukaka, na
cewa:
“Ya ku mutane! Ku bi
Ubangijinku da taƙawa, Wanda Ya halitta ku daga rai guda,
ma’auransa, kuma Ya watsa daga gare su maza masu yawa da mata. Kuma ku bi Allah
da taƙawa, Wanda kuke roƙon juna da
(sunan) Shi, da kuma zumunta. Lalle ne Allah Ya kasance, a kanku, Mai tsaro ne.
Haka
kuma, cikin Alƙur’ani Maigirma, Sura ta 13, Aya ta 21, Allah
Maigirma da Ɗaukaka, na cewa:
“Kuma su ne waɗanda suke
sadar da abin da Allah Ya yi umurni da shi domin a sadar da shi7,
kuma suna tsoron Ubangijinsu, kuma suna tsoron mummunan bincike” (Gumi, 1979:
366).
Domin ƙara
bayyana matsayin zumunci da falalarsa ga dukkan wanda ya sadar da shi, da kuma
irin hasarar da take baibaye da dukkan wanda ya yanke shi, an sami hadisan
Annabi Muhammadu, tsira da amincin Allah su ƙara tabbata a
gare shi, waɗanda suka
fito da waɗannan bayanai
kamar haka :
An karɓo daga Jubair
bin Mut’im, Allah Ya yarda da shi, ya ce: Na ji Manzon Allah, tsira da amincin
Allah su ƙara tabbata a gare shi, Ya ce: “Dukkan wanda
ya yanke igiyar zumunci, to ba ya shiga Aljanna” (Khan, 1417 AH/1996: 952 da
kuma Emarah,1430 AH/2009: 60).
![]() |
7. Waɗannan Ayoyin Alƙur’ani
Maigirma da aka kawo, Aya ta farko da ta uku a nan waɗanda suka
bayyana ‘a sadar da shi’, watau a sadar da zumunci domin samun sakamako mai
kyau. Wanda kuma ya yanke shi ya yi babbar hasara. Ita kuma Aya ta biyu a nan
ta bayyana zumuntar ne fili ba tare da an sakaya ta ba. Ta bayyana cewa, dukkan
wanda ya tsare zumunta ya kyautata, lalle Allah, Maigirma da Ɗaukaka
zai tsare shi.
A wani hadisin da aka
karɓo daga Abu
Huraira, Allah Ya yarda da shi, ya ce:
“Na ji Manzon Allah,
tsira da amincin Allah su ƙara tabbata a
gare shi, ya ce: Kalmar Ar-Rahm
(watau mahaifa) ta samo asalinta ne daga kalmar Ar-Rahman (watau ɗaya daga cikin sunayen Allah, Maigirma
da ɗaukaka).
Dalilin haka ne Allah Maigirma da ɗaukaka, Ya ce: “Zan kyautata wa dukkan
wanda ya kyautata wa mahaifa”, (watau ya sadar da zumunci tsakaninsa da
‘yan’uwansa da abokan arzikinsa). Haka kuma, “Zan tozarta dukkan wanda ya
tozartar da mahaifa” (watau wanda ya yanke zumunci tsakaninsa da ‘yan’uwansa da
abokan arzikinsa), (Khan, 1417 AH/1996: 953).
2.5
Riƙo da Sana’a
Kafin zuwan
wannan zamani al’ummar Hausawa mutane ne waɗanda suka riƙe
sana’o’insu na gargajiya waɗanda suka haɗa da noma da
kiwo da fatauci da dukanci da ƙira da jima
da saƙa da sassaƙa da wanzanci
da sauransu. Mata ma ba a bar su baya ba, don kuwa sun riƙe sana’o’insu
da matuƙar daraja irinsu kaɗi da dakau da
kitso da sauransu. Riƙo da waɗannan
sana’o’i ya taimaka al’ummar Hausawa a wancan zamani sun zauna lafiya ba tare
da fuskantar matsalolin da a yau shugabannin wannan zamani suka gaza wajen
warware su, musamman rashin ayyukan yi ga matasa. A ra’ayina akwai ayyukan yi
ga dukkan mazauna ƙasar Hausa ‘yan gida
da baƙi. Matsalar ita ce, kowa ya mayar da
hankalinsa wajen aikin gwamnati ko na kamfanoni don a waɗannan wurare
ne za a sami kuɗi ba tare da
an yi wata wahala ba. Matuƙar an koma ma tarbiyyar riƙe sana’o’in gargajiya na Hausawa za a warware wannan
matsala.
Dangane da haka ne, addinin Musulunci ya yi horo ga mabiyabansa da su yi
riƙo da sana’o’i, don
kuwa su sana’o’i hanyoyi waɗanda za su taimaka wa al’umma ta zama mai arziki da dogaro da kai, kuma
ta zama ingantacciya. An bayyana cewa dukkan Annabawan da Allah, Maigirma da ɗaukaka, Ya aiko sun gudanar da sana’o’i iri
daban-daban. Misali, an bayyana cewa, Annabi Adamu manomi ne kuma masaƙi, ita kuma matarsa Hauwa’u kaɗi take yi. Haka kuma, Annabi Idrisu maɗunki ne, kuma gwani iya rubutu. Shi kuwa Annabi Nuhu
da Annabi Zakariya’u kafintoci ne, Annabi Salihu kuwa ɗan kasuwa. Haka al’amarin ya yi ta gudana har zuwa ga
Annabi Muhammadu, tsira da amincin Allah su ƙara tabbata a gare shi, wanda shi ya kasance makiyayi
ne (Gusau, 2004:1).
3.1
Matsayin Tarbiyyar Hausawa a yau
Idan muka dubi tarbiyyar
Hausawa a yau kuma muka kwatanta ta tarbiyyar Hausa ta gargajiya, watau kafin
shigowar wannan zamani, za a ga akwai babban sauyi, wanda wannan sauyi ne ya
kai mu shiga cikin halin da muke ciki a yanzu. Idan za mu ɗauki waɗannan
hanyoyin tarbiyya na gargajiya da kuma irin yadda zuwan addinin Musulunci ya ƙara
masu ƙarfin gwiwa, za a ga cewa, a yau watsi da su
ne ya kai ƙasar Hausa da Tarayyar Nijeriya shiga halin
da muke ciki na rashin kyakkyawan shugabanci. Misali, idan muka ɗauki biyayya
ga addini za a ga cewa, a yau addini a
baka yake kawai, a aikace ya yi rauni saboda ba a bin dokokinsa wajen yanke
hukunci kamar yadda suke cikin Alƙur’ani da
Hadisan Annabi, tsira da amincin Allah su ƙara tabbata a
gare shi. Haka kuma, tsarin shugabanci a wannan zamani ya sha bamban da yadda
Hausawa suke gudanar da shi kafin zuwan wannan zamani.
Zuwan Turawa ƙasar
Hausa ya sa sun kawo sabuwar rayuwa wadda ta shafi yadda ake gudanar da mulki,
sun ce mulkin Dimokraɗiyya ne, watau jama’a su zaɓi shugabannin
za su yi masu mulki, amma saboda yadda ake son mulkin ya sa ba a barin jama’a
su zaɓi waɗanda za su yi
masu mulkin adalci. Maimakon haka ana tilasta shugabanni a kan mutane waɗanda suke
sace dukiyar al’umma, suka cusa wa al’umma matsanancin talauci wanda ya yi sanadiyyar
mayar da wasu mutane bayi, ana juya su yadda aka so, ana sanya matasa suna cin
mutunci dukkan wanda ba ya goyon bayansu ko wanda ya ce ba su yi daidai ba.
Wannan ne ya sa a yanzu gaskiya da riƙon amana suka
ƙaura daga cikin zukatan wasu mutane, abin da
ake so kawai shi ne, ta wace hanya za a sami kuɗi a azurta a
dare ɗaya ba tare
da an yi wata wahala ba. Sannan kuma, zumunci ya yi wuya, don a wannan zamani
ana bin aƙidar kowa tashi da fisshe shi. Ɗan’uwa
mai arziki ba ya taimaka wa danginsa mabuƙata, maƙwabci
ba ya kyautata wa waɗanda yake maƙwabtaka da
su. Yara ba su kunyar manya, manya ba su tausaya wa ƙanana.
Ayyukan ɓarna
(zinace-zinace da ta’addanci da sace-sace da fashi da makami) sun yi yawa cikin
ƙasa har ta kai matsayin ba a jin kunyar aikata
su a gaban jama’a.
4.1
Shawarwarin da za su Taimaka a sami Ingantaccen Shugabanci a Wannan Zamani
Matuƙar
ana son samun gyara yadda wannan ƙasa tamu za
ta sami ingantaccen shuganacin da zai sa a sami zama lafiya, arzikin ƙasa
ya dawo yadda kowa zai sami wadata da ƙaruwar arziki
ya zama dole a koma wa tsarin tarbiyyar Hausawa ta gargajiya wadda za a yi mata
wasu ‘yan gyare-gyare yadda za ta tafi daidai da zamani kuma ba ta saɓa kyawawan aƙidun
addinin Musulunci ba kamar haka:
Ø
Dole ne a koma wa bin dokokin addinin
Musulunci ta hanyar bin koyarwa Alƙur’ani da
sunnonin Annabi Muhammadu, tsira da amincin Allah su ƙara tabbata a
gare shi. Dukkan wanda ya saɓa masu a hukunta shi kamar yadda
shari’a ta shimfiɗa.
Ø
Shugabanni su riƙa gudanar da
mulkinsu cikin adalci, kuma da yake a wannan zamani ana mulki irin na siyasa ya
zama dole a bar jama’a su zaɓi waɗanda za su
shugabance su, tilasta shugaba a kan al’umma zai ƙara ɓata al’amari.
Ø
Ya zama dole a riƙa tsare
gaskiya da riƙe amana wajen gudanar da mulki da sauran ma’amalolin
rayuwa a kowane hali mutum ya sami kansa.
Ø
Ƙara sada
zumunci da taimakon juna zai taimaka a ƙara samun
fahimtar juna, yadda za a gudu tare a tsira tare.
Ø
Koma wa sana’o’in gargajiya na Hausawa don
samun abubuwan yi maganin zaman banza da yin bangar siyasa da maula.
Kammalawa
Bisa la’akari da
abubuwan da aka tattauna a wannan takarda waɗanda suka
danganci tarbiyyar Hausawa ta gargajiya da kuma ta addinin Musulunci don samo
hanyar da za ta taimaka a sami ingantaccen shugabanci a wannan zamani, a iya
cewa ya zama dole a fahimci cewa, kyakkyawar tarbiyya ita ce ginshiƙin
da zai tarbe dukkan wata fitina da za ta fuskanci kowace ƙasa.
Kyakkyawar tarbiyya ce za ta taimaka wa ɗan’Adam ya san abin
da yake bauta wa, ita ce za ta horar da mutum ya san abubuwan da abin da yake
bauta wa yake so da waɗanda ba ya so. Yin biyayya ga dokokin addini
musamman addinin Musulunci zai sa a zauna lafiya, a kuma sami biyan bukata ta
duniya da ta lahira. Haka kuma, ya zama dole a riƙa gudanar da
shugabanci bisa adalci da tsoron Allah, a kyautata wa waɗanda ake
shugabanta ta hanyar sauraren koke-kokensu da biya masu bukatunsu. Sannan kuma,
ya zama dole a bar al’umma ta riƙa zaɓar
shugabannin da za su jagoranci mulkinta. Riƙo da gaskiya
da tsare amana na daga cikin abubuwan da matuƙar aka riƙe
su za a sami ingantaccen shugabancin da zai taimaka wa al’umma ta sami
dauwammen ci gaba da zama lafiya. Dukkan al’ummar da take sadar da zumunci,
kuma ‘ya’yanta suna taimakon junansu za ta ƙara samun ci
gaban da zai taimaka mata ta zauna lafiya. Idan har muna son samun ingantaccen
shugabanci a wannan ƙasa tamu, ya zama
dole mu rungumi waɗannan hanyoyi na tarbiyya kamar yadda Hausawa
suka riƙa gudanar da su musamman bayan sun karɓi addinin
Musulunci.
Manazarta
Adamu,
M. (1978) The Hausa Factor in West
African History, Zaria/Ibadan: Ahmadu Bello Uniɓersity
Press/Oɗford Uniɓersity
Press of Nigeria.
Al-Bukhari,
M.I. (Ba Ranar Bugu) Al-Sahihul Bukhari, Beirut-Lebanon: Dar-al-Fikr.
Alhassan, H. da Wasu, (1982) Zaman Hausawa.Zariya:
Institute of Education Press, ABU.
Muhammadu Bello, U. Ɗ. (Ba Ranar Bugu) Fassarar Maƙala Mai Taken Usul
al-Siyasa, Babu Sunan Wanda ya Fassara ta Zuwa Harshen Ingilishi.
Emarah, M.R. (1430 AH, 2009) Fassarar Littafin ‘Al-Kbae’r (The Major Sins) Zuwa harshen Ingilishi, El-Mansoura – Egypt, Dar
Al-Manarah.
Gumi, A.M.
(1979/1399A.H.) Tarjamar Ma’anonin Alƙur’ani Zuwa Harshen Hausa.Beirut-Lebanon:
Dar-al-Arabia.
Gusau, A.R.
(2004) Faɗakar da Al’umma a kan Riƙo da Sana’a, Fassarar Littafin Tanbitul Ummati Alal Tikhadhil Hirfati, Wanda
Muhammadu Sambo Ɗan Ashafa ya Wallafa. Gusau: Farin Batu
Digital Press.
Ibrahim,
M.S.(1982) ”Dangantakar Al’ada da Addini:Tasirin Musulunci kan Rayuwar Hausawa
ta Gargajiya, Kundin Digiri na Biyu. Kano: Sashen Koyar da Harsunan Nijeriya,
Jami’ar Bayero.
Isah, Z.
(2006) “Gaskiya a Tunanin Hausawa”, Kundin Digiri na Farko. Zariya: Sashen
Nazarin Harsunan Nijeriya da Afirka, Tsangaya Fasaha, Jami’ar Ahmadu Bello.
Kani, S.M. (1999)
Fassarar Bulugul Maram, Juzu’i na
Biyu, Talifin Ibnu Hajar Al’Asƙalani,
Kano – Nijeriya.
Khan,
M.H.(1417 AH/1996) Fassarar Sahih
Al-Bukhari Zuwa Harshen Ingilishi,
Riyadh – Saudi Arabia, Dar – us – Salam Publications.
Kwairanga,
A.M.B (2000/1420). Fassarar Littafi Shehu Usmanu Ɗanfodiyo na Ihya’ussunna
wa Ikmadul Bid’a, Kashi na Farko, Kano-Nijeriya: Ba Sunan Maɗaba’a.
Ma’rouf,
I. (1423 AH/2003) Fassarar Littafin Tahzeebu
Dalilul Faliheen – Sharhu Riyadus Saliheen (The Meadows of the Righteous
Abrdged) Zuwa harshen Ingilishi, Juzu’i na Farko, El-Mansoura – Egypt, Dar
Al-Manarah.
Sallau,
B.A.S. (2009) “Sana’ar Wanzanci da Sauye – Sauyen Zamani Jiya da Yau”, Kundin
Digiri na Uku. Kano: Sashen Koyar da Harsunan Nijeriya, Jami’ar Bayero.
Sallau,
B.A.S (2010) Wanzanci da Muhimmancinsa ga
Rayuwar Hausawa. Kaduna:M.A.Najiu Professional Printers, No. 3 Kenya Road.
Smith, M.G. (1957)
"The Hausa System of Social Status", in Africa Ɓol. ƊƊƁII.
No.1.
Shu’aibu, M. (2003)
“Gurbin Gaskiya Cikin Adabin Hausa”, Kundin Digiri na Biyu. Sakkwato: Sashen
Koyar da Harsunan Nijeriya, Jami’ar Usmanu Ɗanfodiyo.
Usman, Y.B. (1972) ”Some Aspects of the Eɗternal
Relations of Katsina Before 1804”, Saɓanna
Ɓol.I.No.2
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.