Ticker

6/recent/ticker-posts

Hukuncin Wanda Ya bada Kuɗi Aka a Zana Masa Jarabawa (Exam)

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Menene Hukuncin Wanda Yabada Kudi Aka Zana Masa Jarabawa Kuma Yaci Gaba Da Karatu Da Ita?

الحمد لله

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

Bai halatta mutum yabada wani kuɗi ko wani abu azana masa jarabawa ba kowacce irice, Domin wannan kuɗin da yabayar aka zana masa jarabawa rashawace kuma ha'incine da yaudara.

Hadisi yazo daka Manzan Allah Sallallahu Alaihi wasallam acikin Muwadda malik ya ce: { Allah yatsinewa Mai bayarda rashawa da maicin rashawar ( wanda aka baiwa) dawanda yake shiga tsakani wajan sanyawa a bayarda rashawa.

fatawa lajnatul da'imah

Sannan Awani Hadisin Annabi Sallallahu Alaihi wasallam cewa yayi: ( Ha'inci da yaudara suna cikin wuta).

Hukuncin wanda yake amfani da irin wannan jarabawar yasani yana amfanine da Abun da Allah ya haramta wajan neman Iliminsa.

Allah kuma mai tsarkine baya karɓar kowani Abu sanya masa Albarka sai abun da yake maitsarki.

Wajibine masu irin wannan dabi'a su tsaya suyi karatu su samu kwalin jarabawa wanda kokarinsu da himmarsu tazama sababi nasamunsa.

Sannan masu wannan dabi'a su sani idan suka gama karatun ahaka to duk wani abu dazasu samu suci kosu sha kosuyi tufafi da wannan takardar susani haramunne suka samu.

WALLAHU TA'AALA

Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance Damu...

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://chat.whatsapp.com/DIcJIQrWyLP0oBOMSnDi5P

𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam

Post a Comment

0 Comments