Ticker

6/recent/ticker-posts

Hukuncin Wanda Yayi Sallah Ba Tareda Tsarki Ba

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Assalamu alaikum. Malam ga tambayata kamar haka, mutun ne ya tashi da janaba da safe yana tashi sai yayi sallah asuba kuma yaci gaba da sallah har tsawon wannan ranar sai washe gari sai yatuna jiya baiyi wankan janaba ba shin yazaiyi wajen rama sallolin jiya? Allah yasa mudace

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

Wa'alaikumus Salam warahmatullahi Wabarkatuh

Wanda yayi sallah batareda Tsarki ba, ya wajaba agareshi yayi Tsarki sannan ya sake sallarsa abisa ittifaqin malamai koda a bisa mantuwa yayi.

Imamun Nawawi ya ce: Musulmai sun haɗu a kan haramcin yin sallah da hadasi, kuma sun haɗu a kan cewa bãta inganta ta kowane irin yanayi, sawa'un yana sane ko baya sane ko acikin mantuwa ne. Idan yayi sallar da janaba ne bai Saniba ko kuma a matuwa to babu zunubi akansa. Amma idan yayi sallar yana sane cewa yanada janaba kuma yasan haramun ne yin sallah da janaba, to ya aikata zunubi mai girma.

WALLAHU A'ALAM

Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance Damu...

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G

𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam

Post a Comment

0 Comments