Ticker

6/recent/ticker-posts

Ayyukan Dake Sanya Mutum A Inuwar Al'arshi Ranar Alkiyama!

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Assalamu Alaikum Malam ya gida ya aiki ya kwana biyu ya iyalenka to Allah yasaka muku da alheri. To malam munaso kayimana karin bayani a kan wannan al'amari anfada a alkur'ani idan kiyama ta tsaya za asauko da rana kusa da mutane to malam wani irin aiki mutum zai juri yi ko kuma abubuwan da mutum zai kiyaye saboda yaga yarabu da wannan masifar ranar gobe kiyama. wassalam Allahh jikan iyayan malam amin.

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

Wa alaikumus salam wa rahmatullahi wa barakatuhu.

Hakika Manzon Allah ya faɗa acikin wani ingantaccen hadisi cewa akwai wasu nau'o'in mutane guda bakwai waɗanda Allah zai inuwantar dasu akarkashin al'arshinsa aranar da babu wata inuwa sai tashi. Gasu nan kamar haka :

1. Adalin shugaba.

2. Da mutumin da zuciyarsa ko yaushe take rataye da masallaci.

3. Mutum biyu da suka so juna domin Allah, suka haɗu a kan haka kuma suka rabu a kan haka.

4. Mutumin da ya tuna Allah shi kaɗai akeɓe har idanuwansa suka zubda hawaye.😭

5.Matashin da ya taso cikin bautar Allah.

6. Mutumin da wata mace Ma'abociyar kyawu da matsayi ta kirashi zuwa ga aikata alfasha amma ya ce "NI INA TSORON ALLAH".

7. Mutumin da ya bayar da sadaqah da hannunsa na dama, ya ɓoyeta har ya zamto hannunsa na haggu bai san abinda ya bayar ba.

Wannan riwayar ta Bukhariy da Muslim ce, amma a kan samu bambanci wajen jaruwar sunayen acikin wasu riwayoyin. Amma na kawosu ne bisa gwargwadon kiyayewata.

Al Imam Jalalud Deen Suyuty shima ya rubuta littafi na musamman wanda acikinsa ya kawo wasu ayyukan da dama waɗanda Manzon Allah da kansa ya faɗesu acikin hadisai ingantattu, cewa duk wanda ya aikatasu zai shiga inuwar Al'arshi.

Saboda faɗin ilimin da Allah ya bashi, sai da ya kawo guda Saba'in. Daga cikinsu akwai

1. Jinkirta ko yafe karɓar bashi daga mutumin da yake cikin tsanani.

2. Taimakon ayi jihadi.

3. Taimakon wanda bashi yayi masa yawa.

4. Taimakon bawa wajen samun 'yancinsa.

5. Wanda ya ba wa mujahidi masauki.

6. Mujahidin da ya tsaya alokacin da sauran mutane suka gudu.

7. Ciyar da mayunwaci.

8. Sadar da zumunci.

9. Matar da ta tsaya ta kula da yaranta Qanana bayan rasuwar mahaifinsu.

10. Mutumin da ya sauki bakonsa ya girmamashi da abinci na musamman.

 Don Qarin bayani aduba littafi mai suna Buzugul Hilal Fil Khisal Almujibati Liz Zilal.

Wannan yana cikin abun da Allah zaiwa bayinsa falala dashi, acikin wannan rana mutane za su kasance cikin bakin-ciki da wahala, rana zata kusanto bayi gwargwadon abun da baifi mil tsakaninta dasu ba, mutane gaba-ɗaya za suyi gumi kowa gwargwadon aikinsa, saidai wani sashi daka cikin muminai da Allah zai keɓancesu yasasu acikin inuwarsa, ya tserar dasu daka rana da kuma gumi.

Allah Ya sanyamu cikin bayinsa waɗanda za su zauna da juna akarkashin inuwar al'arshi aranar da babu wata inuwa sai ita, tare da Annabawan Allah da zaɓaɓɓunsa.🤲

WALLAHU A'ALAM.

Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance Damu...

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://chat.whatsapp.com/Fc3hX6HoDt65aKhhKOiDpX

𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam

Post a Comment

0 Comments